< Maimaitawar Shari’a 27 >

1 Musa tare da dattawan Isra’ila suka umarci mutane suka ce, “Ku kiyaye dukan umarnai da na ba ku a yau.
ויצו משה וזקני ישראל את העם לאמר שמר את כל המצוה אשר אנכי מצוה אתכם היום
2 Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa cikin ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ku kakkafa waɗansu manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa.
והיה ביום אשר תעברו את הירדן אל הארץ אשר יהוה אלהיך נתן לך--והקמת לך אבנים גדלות ושדת אתם בשיד
3 Ku rubuta dukan waɗannan kalmomin doka a kansu, sa’ad da kuka haye kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasa mai zub da madara da zuma, kamar dai yadda Ubangiji Allah na kakanninku, ya yi muku alkawari.
וכתבת עליהן את כל דברי התורה הזאת--בעברך למען אשר תבא אל הארץ אשר יהוה אלהיך נתן לך ארץ זבת חלב ודבש כאשר דבר יהוה אלהי אבתיך לך
4 Sa’ad da kuma kuka haye Urdun, ku kakkafa waɗannan duwatsu a bisa Dutsen Ebal, kamar yadda na umarce a yau, ku yi musu shafe da farar ƙasa.
והיה בעברכם את הירדן תקימו את האבנים האלה אשר אנכי מצוה אתכם היום בהר עיבל ושדת אותם בשיד
5 Ku gina bagade wa Ubangiji Allahnku, bagaden dutse. Kada ku yi amfani da wani kayan aiki na ƙarfe a kansu.
ובנית שם מזבח ליהוה אלהיך מזבח אבנים לא תניף עליהם ברזל
6 Ku gina bagaden Ubangiji Allahnku da duwatsun fili, ku kuma miƙa hadaya ta ƙonawa a kansa ga Ubangiji Allahnku.
אבנים שלמות תבנה את מזבח יהוה אלהיך והעלית עליו עולת ליהוה אלהיך
7 Ku miƙa hadayun salama a can, kuna ci, kuna farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku.
וזבחת שלמים ואכלת שם ושמחת לפני יהוה אלהיך
8 Za ku kuma rubuta a fayyace dukan kalmomin wannan doka a kan waɗannan duwatsun da kuka kakkafa.”
וכתבת על האבנים את כל דברי התורה הזאת--באר היטב
9 Sai Musa da firistoci waɗanda suke Lawiyawa suka ce wa dukan Isra’ila, “Ku yi shiru, ya Isra’ila, ku saurara! Yanzu kun zama mutanen Ubangiji Allahnku.
וידבר משה והכהנים הלוים אל כל ישראל לאמר הסכת ושמע ישראל היום הזה נהיית לעם ליהוה אלהיך
10 Ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, ku bi umarnansa da ƙa’idodin da nake ba ku a yau.”
ושמעת בקול יהוה אלהיך ועשית את מצותו ואת חקיו אשר אנכי מצוך היום
11 A wannan rana Musa ya umarce mutane,
ויצו משה את העם ביום ההוא לאמר
12 Sa’ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama’a albarka, wato, kabilar Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Yusuf da Benyamin.
אלה יעמדו לברך את העם על הר גרזים בעברכם את הירדן שמעון ולוי ויהודה ויששכר ויוסף ובנימן
13 Waɗannan kabilai kuma za su tsaya a bisa Dutsen Ebal su furta la’ana, wato, kabilar Ruben, Gad, Asher, Zebulun, Dan da Naftali.
ואלה יעמדו על הקללה בהר עיבל ראובן גד ואשר וזבולן דן ונפתלי
14 Lawiyawa za su karanta wa dukan mutanen Isra’ila da babbar murya su ce,
וענו הלוים ואמרו אל כל איש ישראל--קול רם
15 “La’ananne ne mutumin da ya sassaƙa siffa, ko ya yi zubin gunki, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannu mai sana’a da aka kafa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
ארור האיש אשר יעשה פסל ומסכה תועבת יהוה מעשה ידי חרש--ושם בסתר וענו כל העם ואמרו אמן
16 “La’ananne ne mutumin da ya ƙasƙantar da mahaifinsa ko mahaifiyarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
ארור מקלה אביו ואמו ואמר כל העם אמן
17 “La’ananne ne mutumin da ya gusar da dutsen da aka kafa don nuna shaidar iyaka.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
ארור מסיג גבול רעהו ואמר כל העם אמן
18 “La’ananne ne mutumin da ya karkatar da makaho daga hanya.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
ארור משגה עור בדרך ואמר כל העם אמן
19 “La’ananne ne mutumin da ya yi rashin adalci ga baƙo, maraya ko gwauruwa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
ארור מטה משפט גר יתום--ואלמנה ואמר כל העם אמן
20 “La’ananne ne mutumin da ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya ƙasƙantar da gadon mahaifinsa ke nan.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
ארור שכב עם אשת אביו--כי גלה כנף אביו ואמר כל העם אמן
21 “La’ananne ne mutumin da ya yi jima’i da dabba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
ארור שכב עם כל בהמה ואמר כל העם אמן
22 “La’ananne ne mutumin da ya kwana da’yar’uwarsa,’yar mahaifinsa ko’yar mahaifiyarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
ארור שכב עם אחתו--בת אביו או בת אמו ואמר כל העם אמן
23 “La’ananne ne mutumin da ya kwana da mahaifiyar matarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
ארור שכב עם חתנתו ואמר כל העם אמן
24 “La’ananne ne mutumin da ya kashe maƙwabcinsa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
ארור מכה רעהו בסתר ואמר כל העם אמן
25 “La’ananne ne mutumin da ya karɓi cin hanci don yă kashe marar laifi.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
ארור לקח שחד להכות נפש דם נקי ואמר כל העם אמן
26 “La’ananne ne mutumin da bai yi na’am da kalmomin wannan doka ta wurin aikata su ba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
ארור אשר לא יקים את דברי התורה הזאת--לעשות אותם ואמר כל העם אמן

< Maimaitawar Shari’a 27 >