< Maimaitawar Shari’a 2 >

1 Sai muka juya muka kama hanya, muka nufi hamada, ta hanyar Jan Teku yadda Ubangiji ya umarce ni. Da daɗewa muka yi ta yawo kewaye da ƙasar tudun Seyir.
ונפן ונסע המדברה דרך ים סוף כאשר דבר יהוה אלי ונסב את הר שעיר ימים רבים
2 Sai Ubangiji ya ce mini,
ויאמר יהוה אלי לאמר
3 “Kun yi ta yawo kewaye da ƙasar tudun nan da daɗewa; yanzu ku juya, ku nufi arewa.
רב לכם סב את ההר הזה פנו לכם צפנה
4 Ka ba wa mutane waɗannan umarnai, ka ce, ‘Kuna gab da wucewa cikin yankin’yan’uwanku, zuriyar Isuwa, wanda yake zama a Seyir. Za su ji tsoronku, amma ku yi hankali
ואת העם צו לאמר אתם עברים בגבול אחיכם בני עשו הישבים בשעיר וייראו מכם ונשמרתם מאד
5 kada ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku wata ƙasa daga cikinsu ba, ba ma wadda za tă iya isa ku sa ƙafarku a kai. Na ba wa Isuwa ƙasar tudu ta Seyir, ta zama tasa.
אל תתגרו בם--כי לא אתן לכם מארצם עד מדרך כף רגל כי ירשה לעשו נתתי את הר שעיר
6 Duk abincin za ku ci, da ruwan da za ku sha, za ku biya su.’”
אכל תשברו מאתם בכסף ואכלתם וגם מים תכרו מאתם בכסף--ושתיתם
7 Ubangiji Allahnku ya albarkace ku cikin dukan aikin hannuwanku. Ya kiyaye ku cikin tafiyarku a duk fāɗin hamada. Waɗannan shekaru arba’in Ubangiji Allahnku ya kasance tare da ku, ba kuwa kun rasa wani abu ba.
כי יהוה אלהיך ברכך בכל מעשה ידך--ידע לכתך את המדבר הגדל הזה זה ארבעים שנה יהוה אלהיך עמך--לא חסרת דבר
8 Saboda haka muka ci gaba, muka wuce’yan’uwanmu, zuriyar Isuwa, wanda yake zama a Seyir. Muka bar hanyar Araba, wadda ta haura daga Elat da Eziyon Geber, muka nufi wajen hamadar Mowab.
ונעבר מאת אחינו בני עשו הישבים בשעיר מדרך הערבה מאילת ומעצין גבר ונפן ונעבר דרך מדבר מואב
9 Sai Ubangiji ya ce mini, “Kada ku dami Mowabawa, ko ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku wani sashe na ƙasarsu ba. Na ba da Ar ga zuriyar Lot, ta zama mallakarsu.”
ויאמר יהוה אלי אל תצר את מואב ואל תתגר בם מלחמה כי לא אתן לך מארצו ירשה--כי לבני לוט נתתי את ער ירשה
10 (Emawa, mutane ne masu ƙarfi da kuma yawa, suna kuma da tsayi kamar Anakawa, dā sun zauna a can.
האמים לפנים ישבו בה--עם גדול ורב ורם כענקים
11 Kamar Anakawa, su ma an ɗauka su Refahiyawa ne, amma Mowab suna kiransu Emawa.
רפאים יחשבו אף הם כענקים והמאבים יקראו להם אמים
12 Haka ma Horiyawa, a dā sun zauna a Seyir, amma zuriya Isuwa suka kore su. Suka hallaka Horiyawa da suke kafinsu, suka kuma zauna a wurinsu, kamar dai yadda Isra’ila ta yi a ƙasar da Ubangiji ya ba su a matsayin mallaka.)
ובשעיר ישבו החרים לפנים ובני עשו יירשום וישמידום מפניהם וישבו תחתם כאשר עשה ישראל לארץ ירשתו אשר נתן יהוה להם
13 Ubangiji kuwa ya ce, “Yanzu ku tashi ku ƙetare Kwarin Zered.” Sai muka ƙetare kwarin.
עתה קמו ועברו לכם--את נחל זרד ונעבר את נחל זרד
14 Dukan shekarun da muka yi a tafiyarmu daga Kadesh Barneya zuwa lokacin da muka ƙetare Kwarin Zered, sun kai shekaru talatin da takwas. A lokacin, wannan tsara gaba ɗaya ta mutanen da suka isa yaƙi sun mutu daga sansani, yadda Ubangiji ya rantse musu.
והימים אשר הלכנו מקדש ברנע עד אשר עברנו את נחל זרד שלשים ושמנה שנה--עד תם כל הדור אנשי המלחמה מקרב המחנה כאשר נשבע יהוה להם
15 Hannun Ubangiji ya yi gāba da su sai da ya hallaka su ƙaƙaf daga sansani.
וגם יד יהוה היתה בם להמם מקרב המחנה עד תמם
16 To, sa’ad da na ƙarshe cikin waɗannan mayaƙa a cikin mutanen ya rasu,
ויהי כאשר תמו כל אנשי המלחמה למות--מקרב העם
17 sai Ubangiji ya ce mini,
וידבר יהוה אלי לאמר
18 “Yau za ku wuce ta yankin Mowab a Ar.
אתה עבר היום את גבול מואב את ער
19 Sa’ad da kuka iso kusa da Ammonawa, kada ku dame su, ko ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku mallakar wata ƙasar da take ta Ammonawa ba. Na riga na ba da ita mallaka ga zuriyar Lot.”
וקרבת מול בני עמון--אל תצרם ואל תתגר בם כי לא אתן מארץ בני עמון לך ירשה--כי לבני לוט נתתיה ירשה
20 (Wannan ita ma a ɗauka ta a matsayin ƙasar Refahiyawa waɗanda dā sun zauna a can ne; amma Ammonawa suna ce da su Zamzummawa.
ארץ רפאים תחשב אף הוא רפאים ישבו בה לפנים והעמנים יקראו להם זמזמים
21 Mutane ne masu ƙarfi da kuma yawa, suna kuma da tsayi kamar Anakawa. Ubangiji ya hallaka su daga gaban Ammonawa, waɗanda suka kore su, suka kuma zauna a wurinsu.
עם גדול ורב ורם כענקים וישמידם יהוה מפניהם ויירשם וישבו תחתם
22 Ubangiji ya yi daidai yadda ya yi wa zuriyar Isuwa waɗanda suka zauna a ƙasar Seyir, sa’ad da ya hallaka Horiyawa a gabansu. Su kuma suka kore su, suka zauna a wurinsu. Har wa yau, zuriyar Isuwa ne suke zama a can.
כאשר עשה לבני עשו הישבים בשעיר--אשר השמיד את החרי מפניהם ויירשם וישבו תחתם עד היום הזה
23 Kusan abu ɗaya ya faru, sa’ad da Kaftorawa daga ƙasar Kaftor suka hallaka Awwiyawa, waɗanda dā suke zaune a yankin ƙauyukan da suke kewaye da Gaza. Suka zauna a wurinsu.)
והעוים הישבים בחצרים עד עזה--כפתרים היצאים מכפתר השמידם וישבו תחתם
24 “Ku fito yanzu ku ƙetare Kwarin Arnon. Duba, na ba da Sihon mutumin Amoriyawa a hannunku, na kuma ba da sarkin Heshbon da ƙasarsa. Ku fara mallake ta, ku kuma yi yaƙi da shi.
קומו סעו ועברו את נחל ארנן--ראה נתתי בידך את סיחן מלך חשבון האמרי ואת ארצו החל רש והתגר בו מלחמה
25 A wannan rana zan fara sa tsoro da fargabanku a kan dukan al’ummai, a ƙarƙashin sama. Za su ji labarinku, za su yi rawan jiki, su kuma damu saboda ku.”
היום הזה אחל תת פחדך ויראתך על פני העמים תחת כל השמים--אשר ישמעון שמעך ורגזו וחלו מפניך
26 Daga hamadar Kedemot, na aiki’yan saƙo zuwa wurin Sihon sarkin Heshbon, a kan ina neman zaman lafiya, ina cewa,
ואשלח מלאכים ממדבר קדמות אל סיחון מלך חשבון דברי שלום לאמר
27 “Bari mu wuce cikin ƙasarka. Za mu bi ta kan hanya ne kaɗai; ba za mu ratse dama ko hagu ba.
אעברה בארצך בדרך בדרך אלך לא אסור ימין ושמאול
28 Ka sayar mana da abincin da za mu ci, da kuma ruwan da za mu sha a farashinsu na azurfa. Ka dai bar mu mu wuce ta ƙasarka kawai,
אכל בכסף תשברני ואכלתי ומים בכסף תתן לי ושתיתי רק אעברה ברגלי
29 kamar yadda zuriyar Isuwa, waɗanda suke zaune a Seyir, da Mowabawa, waɗanda suke zaune a Ar, suka yardar mana, gama muna so mu ƙetare Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji, Allahnmu yake ba mu.”
כאשר עשו לי בני עשו הישבים בשעיר והמואבים הישבים בער--עד אשר אעבר את הירדן אל הארץ אשר יהוה אלהינו נתן לנו
30 Amma Sihon sarkin Heshbon ya ƙi yă bar mu mu wuce a ciki. Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruhunsa ya taurare don yă ba da shi a hannuwanku kamar yadda ya yi yanzu.
ולא אבה סיחן מלך חשבון העברנו בו כי הקשה יהוה אלהיך את רוחו ואמץ את לבבו למען תתו בידך כיום הזה
31 Ubangiji ya ce mini, “Duba, na fara ba da Sihon da ƙasarsa gare ku. Yanzu ku fara cinta, ku kuma mallake ƙasarsa.”
ויאמר יהוה אלי ראה החלתי תת לפניך את סיחן ואת ארצו החל רש לרשת את ארצו
32 Sa’ad da Sihon da dukan sojojinsa suka fito don su sadu da mu, a yaƙi, a Yahaz,
ויצא סיחן לקראתנו הוא וכל עמו למלחמה--יהצה
33 sai Ubangiji Allahnmu ya ba da shi gare mu, muka kuwa buga shi tare da’ya’yansa maza da kuma dukan sojojinsa.
ויתנהו יהוה אלהינו לפנינו ונך אתו ואת בנו ואת כל עמו
34 A wannan lokaci mun ci dukan biranensa, muka kuma hallaka su, maza, mata da kuma yara. Ba mu bar wani da rai ba.
ונלכד את כל עריו בעת ההוא ונחרם את כל עיר מתם והנשים והטף לא השארנו שריד
35 Amma muka washe, muka kuma kwasa shanu da kuma ganima daga biranen wa kanmu.
רק הבהמה בזזנו לנו ושלל הערים אשר לכדנו
36 Ubangiji Allahnmu ya taimake mu muka ci Arower wadda take a gefen Kwarin Arnon, da garin da yake a cikin kwarin, har zuwa Gileyad. Babu garin da ya gaggare mu.
מערער אשר על שפת נחל ארנן והעיר אשר בנחל ועד הגלעד לא היתה קריה אשר שגבה ממנו את הכל נתן יהוה אלהינו לפנינו
37 Amma bisa ga umarnin Ubangiji Allahnmu, ba ku yi kusa da wata ƙasar Ammonawa, ko ƙasar da take gefen kwarin kogin Yabbok, ko kuwa wadda take kewaye da birane cikin tuddai ba.
רק אל ארץ בני עמון לא קרבת כל יד נחל יבק וערי ההר וכל אשר צוה יהוה אלהינו

< Maimaitawar Shari’a 2 >