< Maimaitawar Shari’a 18 >
1 Firistocin da suke Lawiyawa, tabbatacce dukan kabilar Lawi, ba za su sami rabo ko gādo tare da Isra’ila ba. Za su yi rayuwa a kan hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta ne, gama wannan ne gādonsu.
2 Ba za su sami gādo a cikin’yan’uwansu ba; Ubangiji ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.
3 To, ga rabon da jama’a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa ta bijimi ne, ko ta tunkiya ce; sai su ba firistoci kafaɗar, kumatun, da kuma kayan cikin.
4 Za ku ba su nunan fari na hatsinku, da sabon ruwan inabinku, da manku, da kuma gashi na fari daga askin da kuka yi na tumakinku.
5 Gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su da zuriyarsu daga cikin dukan kabilanku don su tsaya su yi hidima a cikin sunan Ubangiji har abada.
6 Idan Balawe ya tashi daga wani garinku, wurin da yake da zama a Isra’ila, ya tafi a wurin da Ubangiji ya zaɓa, zai iya dawo a duk lokacin da ya ga dama.
7 Zai iya yin hidima a cikin sunan Ubangiji Allahnsa kamar dukan sauran’yan’uwansa Lawiyawa waɗanda suke hidima a can, a gaban Ubangiji.
8 Zai sami rabo daidai da sauran, ko da yake ya karɓi kuɗin mallaka na iyali da ya sayar.
9 Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku kwaikwayi hanyoyin banƙyama na al’ummai da suke can.
10 Kada a sami wani a cikinku da ya miƙa ɗansa, ko’yarsa a wuta, ko a sami mai duba, ko mai maita, ko mai fassara gaibi, ko mai sihiri,
11 ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu.
12 Duk wanda yake yin waɗannan abubuwa, shi abin ƙyama ne ga Ubangiji, saboda waɗannan abubuwa banƙyama ne kuwa Ubangiji Allahnku ya kori waɗancan al’ummai kafin ku.
13 Dole ku zama marasa zargi a gaban Ubangiji Allahnku.
14 Al’ummai da za ku kora sukan saurari waɗannan masu maita, ko masu duba. Amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba.
15 Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamar ni daga cikin’yan’uwanku. Dole ku saurare shi.
16 Gama abin da kuka nema daga Ubangiji Allahnku ke nan a Horeb, a ranar taro, sa’ad da kuka ce, “Kada ka bari mu ji muryar Ubangiji Allahnmu, ko mu ƙara ganin wuta mai girma, in ba haka ba, za mu mutu.”
17 Sai Ubangiji ya ce mini, “Abin da suka faɗa yana da kyau.
18 Zan tayar musu da wani annabi kamar ka daga cikin’yan’uwansu; zan sa kalmomina a cikin bakinsa, zai kuma faɗa musu kome da na umarce shi.
19 Duk wanda bai saurari kalmomina da annabin nan yake magana da sunana ba, ni kaina zan nemi hakki a kan mutumin.
20 Amma duk annabin da ya ɗauka cewa yana magana da sunana a kan wani abin da ban umarce shi ya faɗa ba, ko kuwa wani annabin da ya yi magana da sunan waɗansu alloli, dole a kashe shi.”
21 Mai yiwuwa ku ce wa kanku, “Yaya za mu san cewa wannan saƙo ba Ubangiji ne ya faɗa ba?”
22 In abin da annabin ya furta da sunan Ubangiji bai faru ba, ko bai zama gaskiya ba, saƙo ne da Ubangiji bai faɗa ba ke nan. Wannan annabi ya yi rashin hankali ne kawai. Kada ku ji tsoronsa.