< Maimaitawar Shari’a 13 >
1 In wani annabi ko mai mafarkai, ya bayyana a cikinku, ya kuma yi muku shelar wata alama mai banmamaki ko al’ajabi,
2 in kuwa alamar, ko al’ajabin da annabin ya yi faɗin ya faru, ya kuma ce, “Bari mu bi waɗansu alloli (allolin da ba ku sani ba) mu kuma yi musu sujada,”
3 kada ku saurari kalmomin wannan annabi ko mai mafarki. Ubangiji Allahnku yana gwada ku ne don yă sani ko kuna ƙaunarsa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku.
4 Ubangiji Allahnku ne za ku bi, shi ne kuma za ku girmama. Ku kiyaye umarnansa, ku kuma yi masa biyayya; ku bauta masa, ku kuma manne masa.
5 Dole a kashe wannan annabi ko mai mafarki, domin ya yi wa’azin tawaye ga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, ya fanshe ku daga ƙasar bauta; gama annabin nan ya yi ƙoƙari yă juye daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, ku bi. Dole ku fid da mugu daga cikinku.
6 In ɗan’uwanka, ko ɗanka, ko’yarka, ko matar da kake ƙauna, ko abokinka na kusa, a ɓoye ya ruɗe ka, yana cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ko kai, ko kakanninka ba su sani ba,
7 allolin mutanen kewayenku, ko na kusa, ko na nisa, daga wannan ƙarshen ƙasar zuwa wancan),
8 kada ka yarda da shi, kada ma ka saurare shi. Kada ka ji tausayinsa. Kada ka haƙura da shi, ko ka tsare shi.
9 Dole ka kashe shi. Dole hannunka yă zama na farko a kisansa, sa’an nan hannuwan sauran dukan mutane.
10 Ku jajjefe shi da duwatsu har sai ya mutu, domin ya yi ƙoƙari yă juye ku daga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma.
11 Sa’an nan dukan Isra’ila za su ji su kuma tsorata, babu kuma wani a cikinku da zai ƙara yin irin wannan mugun abu.
12 In kuka ji an yi magana a kan wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku zauna a ciki
13 cewa mugaye sun taso a cikinku, suna rikitar da mutane a birni, suna cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ba ku sani ba),
14 to, sai ku bincike labarin sosai a hankali. In kuwa gaskiya ne, an kuma tabbatar wannan abin ƙyama ya faru a cikinku,
15 dole a karkashe dukan waɗanda suke zama a wannan birni da takobi. Ku hallaka su ƙaƙaf, ku karkashe mutanen birnin da kuma dabbobinsa.
16 Ku tattara dukan ganimar birnin a tsakiyar gari, ku ƙone birnin da kuma ganimar ƙurmus a matsayin hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji Allahnku. Birnin zai kasance kufai har abada, kada a sāke gina shi.
17 Ba za a iske wani daga cikin abubuwan nan da aka haramta a hannuwanku ba, saboda Ubangiji yă juya daga fushinsa mai ƙuna, yă nuna jinƙai, yă ji tausayinku, yă kuma ƙara yawanku, kamar yadda ya alkawarta da rantsuwa ga kakanninku,
18 domin kun yi biyayya da Ubangiji Allahnku, kuna kiyaye dukan umarnan da nake ba ku a yau, kuna kuma aikata abin da yake daidai a idanunsa.