< Maimaitawar Shari’a 11 >
1 To, sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kullum ku kuma kiyaye abubuwan da yake bukata, ku kiyaye ƙa’idodinsa, dokokinsa da kuma umarnansu.
2 Ku tuna a yau, cewa’ya’yanku ba su ne suka gani suka kuma ɗanɗana horon Ubangiji Allahnku ba; ba su suka gani girmansa, hannunsa mai ƙarfi, hannunsa mai iko;
3 alamun da ya aikata da abubuwan da ya yi a cikin Masar, ga Fir’auna sarkin Masar da kuma ga dukan ƙasarsa ba;
4 ba su suka gani abin da ya yi wa mayaƙan Masar, da dawakansu da keken yaƙinsu, yadda ya sha kansu da ruwan Jan Teku yayinda suke bin ku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf ba.
5 Ba’ya’yanku ba ne suka gani abin da ya yi dominku a hamada har sai da kuka kai wannan wuri ba,
6 ba su ba ne suka gani abin da ya yi ga Datan da Abiram,’ya’yan Eliyab mutumin Ruben, sa’ad da ƙasa ta buɗe bakinta a tsakiyar dukan Isra’ila ta haɗiye su tare da gidajensu, tentunansu da kowane abu mai rai da yake nasu ba.
7 Amma idanunku ne suka ga dukan waɗannan manyan abubuwan da Ubangiji ya yi.
8 Saboda haka sai ku kiyaye dukan umarnan da nake ba ku a yau, don ku sami ƙarfin da za ku shiga, ku kuma karɓi ƙasar da kuke haye Urdun ku mallaka,
9 domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba su da zuriyarsu, ƙasa mai zub da madara da zuma.
10 Ƙasar da kuke shiga, ku karɓa, ba kamar ƙasar Masar ba ce, inda kuka fito, inda kuka shuka iri, ku yi ta zuwa kuna banruwa kamar lambu.
11 Amma ƙasar da kuke haye Urdun ku mallaki, ƙasa ce ta duwatsu da kwaruruka wadda ruwan sama ne yake jiƙe ta.
12 Ƙasa ce da Ubangiji Allahnku yake lura da ita; idanun Ubangiji Allahnku yana a kai daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta.
13 Saboda haka in kun yi biyayya ga umarnan da nake ba ku a yau cikin aminci, kuna ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna kuma bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku,
14 sai in aika da ruwan sama a ƙasarku a lokacinsa, ruwan saman bazara da kuma na kaka, don ku tattara hatsinku, sabon inabinku da kuma manku.
15 Zan tanadar da ciyawa a filaye don shanunku, za ku ci, ku kuma ƙoshi.
16 Ku yi hankali, kada a ruɗe ku har ku bauta wa alloli, ku kuma yi musu sujada,
17 don kada fushin Ubangiji yă ƙuna a kanku, yă rufe sammai, ku rasa ruwa, ƙasa kuma ta kāsa ba da amfaninta, da haka za ku murmutu nan da nan a kyakkyawar ƙasar da Ubangiji yake ba ku.
18 Saboda haka, sai ku riƙe waɗannan kalmomina gam a zukatanku da ranku; ku ɗaura su kamar alama a hannuwanku, da goshinku.
19 Ku koyar da su ga’ya’yanku, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
20 Ku rubuta su a kan madogaran ƙofofin gidajenku, da a kan ƙofofinku,
21 saboda kwanakinku da kwanakin’ya’yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninku, muddin sama tana bisa duniya.
22 In kuka lura, kuka kuma kiyaye dukan umarnai da nake ba ku, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma riƙe shi gam,
23 Ubangiji zai kori dukan waɗannan al’ummai a gabanku, za ku kuma kore al’umman da suka fi ku yawa da ƙarfi.
24 Duk inda tafin ƙafanku ya taka, zai zama naku; iyakarku zai kama daga hamadan Lebanon da kuma daga Kogin Yuferites zuwa Bahar Rum.
25 Babu mutumin da zai iya tsayayya da ku. Ubangiji Allahnku, zai sa razana da tsoronku a dukan ƙasar, a duk inda kuka tafi, kamar yadda ya alkawarta muku.
26 Ga shi, a yau, ina sa a gabanku albarka da kuma la’ana,
27 albarka in kun yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, da nake ba ku;
28 la’ana in ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, kuka kuma juya daga hanyar da na umarce ku, ta wurin bin waɗansu alloli, waɗanda ba ku sani ba.
29 Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da za ku shiga ku ci gādonta, sai ku yi shelar albarkun nan a dutsen Gerizim, ku kuma yi na la’ana a dutsen Ebal.
30 Waɗannan duwatsu biyu suna a hayin Urdun, yamma da hanya a ƙasar Kan’aniyawa mazaunan Araba, kusa da Gilgal wajajen manyan itatuwan More.
31 Kuna gab da ƙetare Urdun fa, ku shiga, ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Sa’ad da kuka karɓe ta, kuka kuma zauna a can,
32 ku tabbata kun yi biyayya da dukan ƙa’idodi, da kuma dokokin da nake sawa a gabanku a yau.