< Daniyel 7 >
1 A shekara ta fari ta mulkin Belshazar sarkin Babilon, Daniyel ya yi mafarki, wahayoyi kuma suka ratsa tunaninsa a sa’ad da yake a kwance a gadonsa. Sai ya rubuta abin da mafarkin ya ƙunsa.
2 Daniyel ya ce, “A cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga kusurwoyi huɗu na sama suna gurɓata babban teku.
3 Sai ga dabbobi huɗu, kowannensu ya yi dabam da sauran, suna fitowa daga teku.
4 “Na farkon ya yi kamar zaki kuma yana da fikafikai kamar gaggafa. Ina kallo, sai aka fizge fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum.
5 “A gabana kuma ga dabba ta biyu, wadda ta yi kamar beyar. Aka ɗaga ta a gefenta guda, tana kuwa da haƙarƙarai uku a bakinta a tsakanin haƙoranta. Aka faɗa mata, ‘Tashi ki cika cikinki da ɗanyen nama!’
6 “Bayan haka, na duba, a gabana kuwa ga wata dabba wadda ta yi kamar Damisa, a bayanta kuma tana da fikafikai huɗu irin na tsuntsu. Wannan dabbar tana da kawuna huɗu, aka kuma ba ta iko tă yi mulki.
7 “Bayan haka, a cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga dabba ta huɗu, wadda take da bantsoro da banrazana da kuma iko ƙwarai. Tana da manyan haƙoran ƙarfe; ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta. Ta bambanta da dukan sauran dabbobin da suka riga ta, tana kuma da ƙahoni goma.
8 “Yayinda nake cikin tunani game da ƙahonin nan, a gabana kuwa ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙani, wanda ya fito daga cikinsu; kuma an tumɓuke uku daga cikin ƙahonin farko kafin wannan. Wannan ƙaho yana da idanu kamar na mutum da kuma bakin da yake maganganun fariya.
9 “Ina cikin dubawa, “sai aka ajiye kursiyoyi, sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa. Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara; gashin kansa sun yi fari kamar ulu. Kursiyinsa kuma harshen wuta, dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne.
10 Kogin wuta yana gudu, yana fitowa daga gabansa. Dubun dubbai sun yi masa hidima; dubu goma sau dubu goma sun tsaya a gabansa. Aka zauna don shari’a, aka kuma buɗe littattafai.
11 “Sa’an nan na ci gaba da kallo saboda kalmomin fariyar da wannan ƙaho yake furtawa. Na yi ta kallo har sai da aka yanke dabbar, aka kuma hallaka jikinta a cikin wuta.
12 (An tuɓe sauran dabbobin daga mulkinsu, amma aka bar su su rayu na wani lokaci.)
13 “A wahayina na dare, na ga a gabana wani kamar ɗan mutum yana saukowa tare da gizagizan sama. Ya kusaci Wannan wanda yake Tun fil azal aka kuma kai shi gabansa.
14 Aka ba shi mulki, daraja da kuma mafificin iko; dukan mutane, da al’ummai, da mutane daga kowane harshe suka yi masa sujada. Mulkinsa kuwa dawwammamen mulki ne da ba zai ƙare ba, sarautarsa kuma ba ta taɓa lalacewa.
15 “Ni, Daniyel, ruhuna ya damu ƙwarai, kuma wahayin da ya ratsa tunanina ya dame ni.
16 Sai na matsa kusa da ɗaya daga cikin waɗanda suke tsaye a can, na tambaye shi gaskiya ma’anar waɗannan al’amura. “Don haka sai ya faɗa mini, ya kuma ba ni fassarar waɗannan al’amura.
17 ‘Waɗannan manyan dabbobi huɗu, Masarautai ne huɗu waɗanda za su taso a duniya.
18 Amma tsarkaka na Mafi Ɗaukaka za su karɓi wannan sarauta, za su kuwa mallake ta har abada, I, har abada abadin.’
19 “Sa’an nan kuma sai na so in san ma’anar wannan dabba ta huɗu, wadda ta yi dabam da sauran dabbobin da suke da matuƙar bantsoro, da take da haƙoran ƙarfe da kuma farcen tagulla, dabbar ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta.
20 Na kuma so in gane game da ƙahonin nan guda goma da suke a kanta da kuma game da ƙahon nan da ya fito, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa, ƙahon nan da yake da idanu da bakin da yake furta manyan maganganun fariya, wanda ya yi kamar ya fi sauran girma.
21 Ina cikin dubawa, sai ga wannan ƙaho yana yaƙi da tsarkaka yana kuma cin nasara a kansu,
22 sai da Wannan wanda yake tun fil azal ya zo ya furta hukunci, aka kuma ba tsarkaka na Mafi Ɗaukaka gaskiya, lokaci kuwa ya cika sai suka karɓi mulki.
23 “Sai ya ba ni wannan bayani, ‘Dabbar nan ta huɗu, ita ce mulki na huɗu da zai bayyana a duniya. Zai bambanta da dukan sauran mulkoki, zai kuma cinye dukan duniya, yă tattake ta, yă kuma ragargaje ta.
24 Ƙahonin nan goma, sarakuna ne goma waɗanda za su taso daga wannan mulki. Bayansu kuma, wani sarki zai taso, wanda ya sha dabam da waɗanda suka riga shi. Zai rinjayi sarakunan nan uku.
25 Zai yi maganar saɓo a kan Mafi Ɗaukaka, zai kuma tsananta wa tsarkaka yă kuma yi ƙoƙarin sāke lokuta da shari’u. Za a miƙa tsarkaka a hannunsa na wani lokaci, lokuta da kuma rabin lokaci.
26 “‘Amma majalisa za tă yi zama, za a karɓe ikonsa, a kuma hallaka shi gaba ɗaya har abada.
27 Sa’an nan za a ba da mulki, iko da girma na mulkokin da suke a ƙarƙashin dukan sammai ga tsarkaka, mutane na Mafi Ɗaukaka. Mulkinsa kuwa mulki ne marar matuƙa, kuma dukan masu mulki za su yabe shi, su kuma yi masa biyayya.’
28 “Wannan shi ne ƙarshen batun. Ni, Daniyel na damu ƙwarai da irin tunanina, kuma fuskata ta rikice, amma na riƙe batun a zuciyata.”