< Daniyel 5 >
1 Sarki Belshazar ya yi babban biki domin dubban hakimansa ya kuma sha ruwan inabi tare da su.
伯沙撒王為他的一千大臣設擺盛筵,與這一千人對面飲酒。
2 Yayinda Belshazar yake shan ruwan inabi, sai ya umarta a kawo zinariya da azurfan da Nebukadnezzar mahaifinsa ya kwaso daga haikali a Urushalima, saboda sarki da hakimansa, da matansa da ƙwarƙwaransa su sha da su.
伯沙撒歡飲之間,吩咐人將他父尼布甲尼撒從耶路撒冷殿中所掠的金銀器皿拿來,王與大臣、皇后、妃嬪好用這器皿飲酒。
3 Sai suka kawo kayan zinariyan nan da aka kwaso daga haikalin Allah a Urushalima, sarki kuwa da hakimansa, da matansa, da ƙwarƙwaransa suka yi ta sha da su.
於是他們把耶路撒冷上帝殿庫房中所掠的金器皿拿來,王和大臣、皇后、妃嬪就用這器皿飲酒。
4 Yayinda suke shan ruwan inabin, sai suka yabi allolin zinariya da azurfa, da na tagulla, da na ƙarfe, da na itace da kuma na dutse.
他們飲酒,讚美金、銀、銅、鐵、木、石所造的神。
5 Nan da nan sai ga yatsotsin hannun mutum sun bayyana, suna yin rubutu a kan shafen bangon, kusa da wurin da ake ajiye fitilar fadar sarki. Sarki kuwa yana ganin hannun yayinda yake rubutu.
當時,忽有人的指頭顯出,在王宮與燈臺相對的粉牆上寫字。王看見寫字的指頭
6 Sai fuskarsa ta ruɗe, ya kuma ji tsoro ƙwarai har gwiwoyinsa suka yi ta bugun juna, ƙafafunsa kuma suka rasa ƙarfi.
就變了臉色,心意驚惶,腰骨好像脫節,雙膝彼此相碰,
7 Sai sarki ya kira masu dabo, masanan taurari da masu duba, a kawo su, ya kuma ce wa masu hikima na Babilon, “Duk wanda ya karanta wannan rubutu ya kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”
大聲吩咐將用法術的和迦勒底人並觀兆的領進來,對巴比倫的哲士說,誰能讀這文字,把講解告訴我,他必身穿紫袍,項帶金鍊,在我國中位列第三。
8 Sa’an nan sai dukan masu hikima suka zo ciki, amma ba su iya karanta rubutun ba ko su faɗa wa sarki abin da yake nufi.
於是王的一切哲士都進來,卻不能讀那文字,也不能把講解告訴王。
9 Saboda haka Sarki Belshazar ya firgita ƙwarai kuma fuskarsa ta ƙara ruɗewa. Hakimansa kuma suka rikice.
伯沙撒王就甚驚惶,臉色改變,他的大臣也都驚奇。
10 Sai sarauniya, da jin muryoyi na sarki da na hakimansa, ta shiga babban ɗakin liyafar. Ta ce, “Ya sarki, ranka yă daɗe! Kada ka firgita! Kada fuskarka ta ruɗe!
太后因王和他大臣所說的話,就進入宴宮,說:「願王萬歲!你心意不要驚惶,臉面不要變色。
11 Akwai wani mutum a masarautarka wanda yake da ruhun alloli masu tsarki a cikinsa. A zamanin mahaifinka an gane cewa yana da basira da hazaka da hikima kamar na alloli. Sarki Nebukadnezzar mahaifinka, mahaifinka sarki, na ce, ya naɗa shugaban masu dabo, da masu sihiri, masanan taurari da kuma masu duba.
在你國中有一人,他裏頭有聖神的靈,你父在世的日子,這人心中光明,又有聰明智慧,好像神的智慧。你父尼布甲尼撒王,就是王的父,立他為術士、用法術的,和迦勒底人,並觀兆的領袖。
12 Wannan mutum Daniyel, wanda sarki ya kira Belteshazar, an gane yana da ruhu nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma’anar kacici-kacici, da warware al’amura masu wuya. Ka kira Daniyel shi kuwa zai faɗa maka abin da rubutun nan yake nufi.”
在他裏頭有美好的靈性,又有知識聰明,能圓夢,釋謎語,解疑惑。這人名叫但以理,尼布甲尼撒王又稱他為伯提沙撒,現在可以召他來,他必解明這意思。」
13 Saboda haka aka kawo Daniyel a gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda mahaifina sarki ya kawo daga Yahuda?
但以理就被領到王前。王問但以理說:「你是被擄之猶大人中的但以理嗎?就是我父王從猶大擄來的嗎?
14 Na sami labari cewa kana da ruhun alloli a cikinka da kuma basira, da hazaka da kuma fitacciyar hikima.
我聽說你裏頭有神的靈,心中光明,又有聰明和美好的智慧。
15 An kawo masu hikima da masu dabo a gabana domin su karanta wannan rubutu su kuma faɗa mini abin da yake nufi, amma ba su iya ba.
現在哲士和用法術的都領到我面前,為叫他們讀這文字,把講解告訴我,無奈他們都不能把講解說出來。
16 Na sami labari cewa kana iya ba da fassara da kuma warware matsaloli masu wuya. In har ka iya karanta wannan rubutun ka kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa maka riga shunayya, a kuma sa sarƙar zinariya a wuyanka. Za ka zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”
我聽說你善於講解,能解疑惑;現在你若能讀這文字,把講解告訴我,就必身穿紫袍,項戴金鍊,在我國中位列第三。」
17 Sai Daniyel ya amsa wa sarki ya ce, “Za ka iya ajiye kyautar wa kanka ko kuma ka ba wa wani. Duk da haka, zan karanta wa sarki rubutun, in kuma faɗa abin da yake nufi.
但以理在王面前回答說:「你的贈品可以歸你自己,你的賞賜可以歸給別人;我卻要為王讀這文字,把講解告訴王。
18 “Ya sarki, Allah Mafi Ɗaukaka ya ba mahaifinka Nebukadnezzar sarauta, da girma, da ɗaukaka, da martaba.
王啊,至高的上帝曾將國位、大權、榮耀、威嚴賜與你父尼布甲尼撒;
19 Saboda irin matsayin da ya ba shi, dukan mutane da al’ummai da kuma dukan harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani.
因上帝所賜他的大權,各方、各國、各族的人都在他面前戰兢恐懼。他可以隨意生殺,隨意升降。
20 Amma da lokacin da zuciyarsa ta cika da girman kai ta kuma taurare, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.
但他心高氣傲,靈也剛愎,甚至行事狂傲,就被革去王位,奪去榮耀。
21 Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.
他被趕出離開世人,他的心變如獸心,與野驢同居,吃草如牛,身被天露滴濕,等他知道至高的上帝在人的國中掌權,憑自己的意旨立人治國。
22 “Amma kai ɗansa, Ya Belshazar, ba ka ƙasƙantar da kanka ba, ko da yake ka san wannan duka.
伯沙撒啊,你是他的兒子,你雖知道這一切,你心仍不自卑,
23 A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.
竟向天上的主自高,使人將他殿中的器皿拿到你面前,你和大臣、皇后、妃嬪用這器皿飲酒。你又讚美那不能看、不能聽、無知無識、金、銀、銅、鐵、木、石所造的神,卻沒有將榮耀歸與那手中有你氣息,管理你一切行動的上帝。
24 Saboda haka ya aiko da hannun da ya yi rubutun nan.
因此從上帝那裏顯出指頭來寫這文字。
25 “Wannan shi ne rubutun da aka yi, Mene, mene, tekel, farsin
「所寫的文字是:『彌尼,彌尼,提客勒,烏法珥新。』
26 “Abin da kalmomin nan suke nufi shi ne, “Mene, Allah ya ƙayyade yawan kwanakin mulkinka ya kuma kawo su ga ƙarshe.
講解是這樣:彌尼,就是上帝已經數算你國的年日到此完畢。
27 “Tekel, An kuma auna ka a ma’auni aka tarar ka kāsa.
提客勒,就是你被稱在天平裏,顯出你的虧欠。
28 “Feres, An raba mulkinka aka ba wa Medes da Farisa.”
毗勒斯,就是你的國分裂,歸與米底亞人和波斯人。」
29 Sai Belshazar ya umarta, aka sa wa Daniyel riga mai shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.
伯沙撒下令,人就把紫袍給但以理穿上,把金鍊給他戴在頸項上,又傳令使他在國中位列第三。
30 A wannan dare aka kashe Belshazar, sarkin Babiloniyawa,
當夜,迦勒底王伯沙撒被殺。
31 Dariyus mutumin Medes kuwa ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu.
米底亞人大流士年六十二歲,取了迦勒底國。