< Daniyel 3 >
1 Sarki Nebukadnezzar ya yi gunkin zinariya, tsawonsa kamu tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tara ne, ya kafa shi a filin Dura a yankin Babilon.
2 Sa’an nan ya aika a kira hakimai da wakilai da gwamnoni da mashawarta, da ma’aji, da alƙalai, da marubutan kotu, da dukan sauran ma’aikatan yankunan, suka hallara domin a rusuna wa wannan siffar da ya kafa.
3 Saboda haka sai hakimai, da wakilai da gwamnoni, mashawarta da ma’aji da alƙalai, da marubutan alƙalai, da kuma dukan ma’aikatan yankunan suka tattaru domin kaddamar da siffar da Nebukadnezzar ya kafa, suka kuma tsaya a gabansa.
4 Sai mai shela ya daga murya da ƙarfi ya ce, “Wannan shi ne abin da aka umarce ku ku yi, ya ku mutane da al’umma da kowane yare.
5 Da zarar kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya da goge da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ku rusuna ku yi sujada ga wannan gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa.
6 Duk wanda bai rusuna ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a cikin tendarun wuta.”
7 Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa.
8 A wannan lokaci sai waɗansu masanan taurari suka zo gaba suka yi karar Yahudawa.
9 Suka ce wa sarki Nebukadnezzar, “Ran sarki yă daɗe,
10 Ya sarki, ka fitar da doka, cewa duk wanda ya ji karar ƙaho, da sarewa, da garayu da goge, da molo da algaita da kowane irin kayan kaɗe-kaɗe da bushe-bushe sai yă rusuna yă yi sujada ga siffar zinariya,
11 kuma cewa duk wanda bai rusuna ya yi sujadar ba za a jefa shi cikin tanderun wuta.
12 Amma sai ga waɗansu Yahudawa waɗanda ka ɗora su a kan harkokin yankin Babilon, wato, Shadrak, Meshak da Abednego waɗanda ba su kula da umarninka ba, ya sarki. Ba su bauta wa allolin ba balle su yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa.”
13 Cikin fushi da hasala, Nebukadnezzar ya aika a kira Shadrak, Meshak da Abednego. Aka kawo waɗannan mutane a gaban sarki,
14 sai Nebukadnezzar ya ce musu, “Gaskiya ne Shadrak, Meshak da Abednego, cewa kun ƙi ku bauta wa alloli kuka kuma ƙi yi sujada ga gunkin da na kafa?
15 Yanzu sa’ad da kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, in kuna a shirye ku rusuna ƙasa ku yi wa wannan gunkin da na yi sujada, to, da kyau. Amma in ba ku yi sujada ba, za a je fa ku yanzu a cikin tanderun wutar nan. In ga kowane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”
16 Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka amsa wa sarki suka ce, “Ya Nebukadnezzar, ba mu bukata mu kāre kanmu a gabanka a kan wannan batu.
17 In an jefa mu cikin tanderun wutar nan, Allahn da muke bauta wa zai iya cetonmu daga ita, kuma ya sarki, zai cece mu daga hannunka.
18 Amma ko da bai cece mu ba, muna so ka sani, ya sarki; cewa ba za mu bauta wa allolinka ba ko kuma mu yi sujada ga gunkin zinariyar da ka kafa ba.”
19 Sai Nebukadnezzar ya husata da Shadrak, Meshak da Abednego, sai al’amuransa a kansu ya canja. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar har sau bakwai domin tă yi zafi fiye da yadda take a dā.
20 Kuma ya umarci waɗansu ƙarfafan sojoji a cikin rundunarsa su daure Shadrak, Meshak da Abednego su jefa su cikin tanderun wutar.
21 Waɗannan mutanen suna sanye da riguna, da wanduna, da rawani da waɗansu kayan sawa, aka daure su, aka jefa su cikin tanderun wuta.
22 Sarki ya ba da umarnin da gaggawa kuma wutar ta yi zafi ƙwarai har harshen wutar ya kashe sojojin nan da suka ɗauki Shadrak, Meshak da Abednego,
23 waɗannan mutane uku kuma a daure, suka fāɗa cikin tanderun wutar.
24 Sai Sarki Nebukadnezzar ya miƙe tsaye, cike da mamaki ya tambayi mashawartansa, “Shin ba mutum uku ba ne muka daure muka jefa cikin wutar?” Suka amsa, “Tabbatacce haka yake ya sarki.”
25 Sai ya ce, “Ku duba ina ganin mutum huɗu suna tafiya suna yawo a cikin wutar, a sake kuma babu abin da ya same su, na huɗun sai ka ce ɗan alloli.”
26 Sai Nebukadnezzar ya matsa kusa da ƙofar tanderun wutar ya yi kira da ƙarfi, “Shedrak, Meshak da Abednego, bayin Allah Mafi Ɗaukaka ku fito! Ku zo nan!” Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka fita daga cikin wutar,
27 Sa’an nan hakimai, da wakilai, da gwamnoni da masu ba wa sarki shawara suka kewaya su. Suka ga wutar ba tă yi musu wani lahani a jikinsu ba, babu ko gashin kansu da ya ƙuna; ko warin wuta ma ba su yi ba.
28 Sa’an nan Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allahn Shadrak, Meshak da Abednego wanda ya aiko da mala’ikansa ya ceci bayinsa da suka dogara matuƙa a gare shi, suka ki bin umarnin sarki kuma su na a shirye domin su ba da ransu da suka ƙi bauta ko su yi sujada ga wani allah sai dai Allahnsu.
29 Domin haka ina ba da doka cewa duk mutane da kowace al’umma ko kowane yaren da ya ce wani abu mummuna a kan Allahn Shadrak, Meshak da Abednego za a yanka shi gunduwa-gunduwa kuma gidansu zai zama wurin zuba shara, domin babu wani allahn da zai iya ceto ta irin wannan hanya.”
30 Sa’an nan sarki ya ƙara wa su Shadrak, Meshak da Abednego girma a yankin Babilon.