< Kolossiyawa 4 >
1 Masu bayi, ku riƙe bayinku da kyau da kuma daidai, domin kun san cewa ku ma kuna da Ubangiji a sama.
2 Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya.
3 Ku kuma yi mana addu’a, mu ma, don Allah yă buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi.
4 Ku yi addu’a yadda zan yi shelarsa, yadda ya kamata.
5 Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi.
6 Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.
7 Tikikus shi ne ƙaunataccen ɗan’uwan nan, wanda ya yi aiki da aminci a hidimar Ubangiji tare da mu, zai kuwa faɗa muku dukan labari game da ni.
8 Ina aikansa shi a gare ku musamman domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya.
9 Yana zuwa tare da Onesimus, ƙaunatacce da kuma amintaccen mai bin nan, wanda yake ɗaya daga cikinku. Za su gaya muku dukan abin da yake faruwa a nan.
10 Aristarkus yana a kurkuku tare da ni. Yana gaishe ku, haka ma Markus, wanda kakansa ɗaya ne da Barnabas. (Shi ne na riga na yi magana a kansa, na ce muku in ya zo, ku karɓe shi hannu biyu-biyu.)
11 Yesu, wannan da muke kira Yustus, shi ma yana gaisuwa. Waɗannan ne kaɗai Yahudawa masu bi a cikin abokan aikina saboda mulkin Allah. Sun kuma zama da taimako a gare ni.
12 Efafaras naku, mai hidimar Kiristi Yesu, yana gaisuwa. Kullum yana addu’a dominku sosai, don ku san cikakken abin da Allah yake so ku yi don kuma ku yi shi cikakke.
13 Na tabbatar muku, cewa yana aiki ƙwarai dominku da kuma domin waɗanda suke a Lawodiseya da Hiyerafolis.
14 Luka ƙaunataccen likitan nan, da kuma Demas suna gaishe ku.
15 Ku miƙa gaisuwata ga’yan’uwan da suke a Lawodiseya, musamman ga Nimfa da kuma ikkilisiyar da take taru a gidanta.
16 Bayan an karanta muku wannan wasiƙa, ku tabbata an karanta ta kuma a ikkilisiyar Lawodiseyawa; ku ma ku karanta wasiƙar da ta zo daga Lawodiseya.
17 Ku faɗa wa Arkiffus yă tabbata ya ƙarasa aikin da ya karɓa cikin Ubangiji.
18 Ni Bulus ne nake rubuta muku wannan gaisuwa da hannuna. Ku tuna da sarƙoƙina. Alherin Allah yă kasance tare da ku.