< Kolossiyawa 2 >
1 Ina so ku san irin famar da nake yi saboda ku da kuma waɗanda suke a Lawodiseya, da kuma saboda dukan waɗanda ba su taɓa ganina ido da ido ba.
For I want you to know how much I am struggling for you and for those at Laodicea, and for all who have not met me face to face,
2 Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa,
that they may be encouraged in heart, knit together in love, and filled with the full riches of complete understanding, so that they may know the mystery of God, namely Christ,
3 a cikinsa ne aka ɓoye dukkan dukiya ta hikima da ta sani.
in whom are hidden all the treasures of wisdom and knowledge.
4 Ina faɗa muku wannan ne don kada wani yă ruɗe ku da daɗin baki.
I say this so that no one will deceive you by smooth rhetoric.
5 Gama ko da yake ba na nan tare da ku a cikin jiki, ina tunaninku kullum, ina kuma farin ciki da gani kuna rayuwa yadda ya kamata, kuna kuma dāgewarku a kan bangaskiyarku a cikin Kiristi.
For although I am absent from you in body, I am present with you in spirit, and I delight to see your orderly condition and firm faith in Christ.
6 To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa,
Therefore, just as you have received Christ Jesus as Lord, continue to walk in Him,
7 ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya.
rooted and built up in Him, established in the faith as you were taught, and overflowing with thankfulness.
8 Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba.
See to it that no one takes you captive through philosophy and empty deception, which are based on human tradition and the spiritual forces of the world rather than on Christ.
9 Gama a cikin Kiristi cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata,
For in Christ all the fullness of the Deity dwells in bodily form.
10 an kuma mai da ku cikakku a cikin Kiristi, wanda yake shi ne kai a kan kowane iko da kuma hukuma.
And you have been made complete in Christ, who is the head over every ruler and authority.
11 A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Kiristi ya yi muku, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka.
In Him you were also circumcised, in the putting off of your sinful nature, with the circumcision performed by Christ and not by human hands.
12 Da yake an binne ku tare da shi cikin baftisma haka kuma aka tashe ku tare da shi ta wurin bangaskiyarku a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu.
And having been buried with Him in baptism, you were raised with Him through your faith in the power of God, who raised Him from the dead.
13 Kun zama matattu saboda ku masu zunubi ne kuma saboda halin zunubanku aka ware. Sa’an nan Allah ya sa kuka rayu tare da Kiristi. Ya gafarta mana dukan zunubanmu.
When you were dead in your trespasses and in the uncircumcision of your sinful nature, God made you alive with Christ. He forgave us all our trespasses,
14 Ya soke rubutacciyar doka tare da ƙa’idodinta, wadda take gāba da mu, take kuma hamayya da mu; ya kuma kawar da ta, ya kafe ta a kan gicciye.
having canceled the debt ascribed to us in the decrees that stood against us. He took it away, nailing it to the cross!
15 Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye.
And having disarmed the powers and authorities, He made a public spectacle of them, triumphing over them by the cross.
16 Saboda haka kada ku bar wani yă shari’anta ku a kan abin da kuke ci ko sha, ko bisa ga abin da ya shafi wani bikin addini, ko Bikin Sabon Wata ko na ranar Asabbaci.
Therefore let no one judge you by what you eat or drink, or with regard to a feast, a New Moon, or a Sabbath.
17 Waɗannan su ne hoton abubuwan da za su zo; amma Kiristi ne ainihinsu.
These are a shadow of the things to come, but the body that casts it belongs to Christ.
18 Kada ku yarda wani yă ɓata ku, cewa shi wani abu ne don yă ga wahayi. Irin mutumin nan yakan nuna ƙasƙancin kai na ƙarya, yă kuma ce yana yi wa mala’iku sujada. Irin mutumin nan yana kumbura kansa ba dalili, sai son zuciya irin na halin mutuntaka.
Do not let anyone who delights in false humility and the worship of angels disqualify you with speculation about what he has seen. Such a person is puffed up without basis by his unspiritual mind.
19 Ya yanke dangantaka da Kiristi wanda yake kai, wanda ta gare shi ne dukan jiki yake a haɗe, yake tsaye ta wurin taimakon gaɓoɓi da jijiyoyi, yana kuma girma kamar yadda Allah yake sa yă yi girma.
He has lost connection to the head, from whom the whole body, supported and knit together by its joints and ligaments, grows as God causes it to grow.
20 Kun mutu tare da Kiristi. Yanzu ƙa’idodin wannan duniya ba su da iko a kanku. Don me kuke zama har yanzu kamar ku nasu ne? Kuna biyayya da umarnansu cewa,
If you have died with Christ to the spiritual forces of the world, why, as though you still belonged to the world, do you submit to its regulations:
21 “Kada ka kama! Kada ka ɗanɗana! Kada ka taɓa”?
“Do not handle, do not taste, do not touch!”?
22 Irin waɗannan dokoki suna magana a kan abubuwan da ba sa daɗewa. Su ayyukan mutane ne, sun kuma fito daga koyarwar mutane.
These will all perish with use, because they are based on human commands and teachings.
23 Yin biyayya da irin waɗannan ƙa’idodi za su yi kamar su ne abu mafi kyau da za a yi. Sukan yi kamar suna sa a ƙaunaci Allah sosai a kuma kasance da sauƙinkai a kuma kasance da kamunkai. Amma ba su da wani iko a kan sha’awace-sha’awacenmu.
Such restrictions indeed have an appearance of wisdom, with their self-prescribed worship, their false humility, and their harsh treatment of the body; but they are of no value against the indulgence of the flesh.