< Amos 1 >

1 Kalmomin Amos, ɗaya daga cikin makiyayan Tekowa, abubuwan da ya gani game da Isra’ila shekaru biyu kafin a yi girgizar ƙasa, a lokacin da Uzziya yake sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yowash kuma yake sarkin Isra’ila.
verba Amos qui fuit in pastoralibus de Thecuae quae vidit super Israhel in diebus Oziae regis Iuda et in diebus Hieroboam filii Ioas regis Israhel ante duos annos terraemotus
2 Ya ce, “Ubangiji ya yi ruri daga Sihiyona ya kuma yi tsawa daga Urushalima; wuraren kiwo duk sun bushe, dutsen Karmel kuma ya yi yaushi.”
et dixit Dominus de Sion rugiet et de Hierusalem dabit vocem suam et luxerunt speciosa pastorum et exsiccatus est vertex Carmeli
3 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Damaskus, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Domin sun ci zalunci Gileyad zalunci mai tsanani,
haec dicit Dominus super tribus sceleribus Damasci et super quattuor non convertam eum eo quod trituraverint in plaustris ferreis Galaad
4 zan sa wuta a gidan Hazayel, da za tă ƙona kagarun Ben-Hadad.
et mittam ignem in domum Azahel et devorabit domos Benadad
5 Zan kakkarye ƙofofin Bet-Damaskus; zan hallaka sarkin da yake cikin Kwarin Awen da kuma mai riƙe da sandar mulkin Bet-Eden. Mutanen Aram za su je bauta a ƙasar Kir,” in ji Ubangiji.
et conteram vectem Damasci et disperdam habitatorem de campo Idoli et tenentem sceptrum de domo Voluptatis et transferetur populus Syriae Cyrenen dicit Dominus
6 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Gaza, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun sayar wa Edom,
haec dicit Dominus super tribus sceleribus Gazae et super quattuor non convertam eum eo quod transtulerit captivitatem perfectam ut concluderet eam in Idumea
7 Zan aika da wuta a katangar Gaza ta ƙone duk kagarunta.
et mittam ignem in murum Gazae et devorabit aedes eius
8 Zan hallaka sarkin Ashdod da kuma mai riƙe da sandar mulki na Ashkelon. Zan hukunta Ekron, har sai dukan Filistiyawa sun mutu,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
et disperdam habitatorem de Azoto et tenentem sceptrum de Ascalone et convertam manum meam super Accaron et peribunt reliqui Philisthinorum dicit Dominus Deus
9 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Taya, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom, ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar’yan’uwa ba,
haec dicit Dominus super tribus sceleribus Tyri et super quattuor non convertam eum eo quod concluserint captivitatem perfectam in Idumea et non sint recordati foederis fratrum
10 zan aika da wuta a Taya, da za tă ƙone kagarunta.”
et emittam ignem in murum Tyri et devorabit aedes eius
11 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Edom, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi, babu tausayi, domin ya ci gaba da fusata bai yarda yă huce daga fushinsa ba.
haec dicit Dominus super tribus sceleribus Edom et super quattuor non convertam eum eo quod persecutus sit in gladio fratrem suum et violaverit misericordiam eius et tenuerit ultra furorem suum et indignationem suam servaverit usque in finem
12 Zan aika wuta a Teman da za tă ƙone kagarun Bozra.”
mittam ignem in Theman et devorabit aedes Bosrae
13 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Ammon, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu don kawai yă ƙwace ƙasar.
haec dicit Dominus super tribus sceleribus filiorum Ammon et super quattuor non convertam eum eo quod dissecuerit praegnantes Galaad ad dilatandum terminum suum
14 Zan sa wuta a katangar Rabba da za tă ƙone kagarunta za a yi kururuwa a ranar yaƙi, faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri.
et succendam ignem in muro Rabbae et devorabit aedes eius in ululatu in die belli et in turbine in die commotionis
15 Sarkinta zai je bauta, shi da ma’aikatansa,” in ji Ubangiji.
et ibit Melchom in captivitatem ipse et principes eius simul dicit Dominus

< Amos 1 >