< Amos 8 >
1 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji ya nuna mini kwandon nunannun’ya’yan itace.
2 Ya yi tambaya ya ce, “Me ka gani Amos?” Sai na amsa na ce, “Kwandon nunannun’ya’yan itace.” Sai Ubangiji ya ce mini, “Lokaci ya yi wa mutanena Isra’ila da ba zan ƙara barinsu ba.
3 “A ranan nan,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “Waƙoƙin a haikali za su koma makoki. Za a ga gawawwaki a ko’ina! Shiru!”
4 Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata kuka kori matalautan ƙasar.
5 Kuna cewa, “Yaushe Sabon Wata zai wuce don mu sayar da hatsi, Asabbaci ta wuce, don mu sayar da alkama?” Mu yi awo da ma’aunin zalunci mu ƙara kuɗin kaya mu kuma cutar da mai saya,
6 mu sayi matalauta da azurfa masu bukata kuma da takalmi, mu sayar da alkamar haɗe da yayi.
7 Ubangiji ya rantse da Girman Yaƙub, “Ba zan taɓa mantawa da duk wani abin da suka yi ba.
8 “Shin, ƙasar ba za tă yi rawan jiki saboda wannan ba, kuma duk masu zama a cikinta ba za su yi makoki ba? Ƙasar duka za tă hau ta sauka kamar Nilu; za a dama ta sa’an nan ta nutse kamar kogin Masar.
9 “A wannan rana,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “Zan sa rana ta fāɗi da tsakar rana in kuma duhunta duniya da rana tsaka.
10 Zan mai da bukukkuwanku na addini su zama makoki kuma dukan waƙoƙinku su zama kuka. Zan sa dukanku ku sa rigunan makoki za ku kuma aske kawunanku. Zan sa wannan lokaci yă zama kamar lokacin da ake makokin ɗan tilon da ake da shi kuma ƙarshenta kamar rana mai ɗaci.
11 “Ranakun suna zuwa,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “sa’ad da zan aika da yunwa cikin ƙasar, ba yunwar abinci ko ta ƙishirwa ba, sai dai yunwa ta jin maganar Ubangiji.
12 Mutane za su yi ta tangaɗi daga teku zuwa teku suna yawo daga arewa zuwa kudu, suna neman maganar Ubangiji, amma ba za su samu ba.
13 “A wannan rana “kyawawan’yan mata da kuma samari masu ji da ƙarfi za su suma don ƙishirwa.
14 Waɗanda suka yi rantsuwa da abin kunya na Samariya, ko kuma su ce, ‘Muddin allahnku yana a raye, ya Dan,’ ko kuwa, ‘Muddin allahn Beyersheba yana a raye,’ za su fāɗi, ba kuwa za su ƙara tashi ba.”