< Amos 7 >

1 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji yana shirya cincirindon fāri bayan da aka ƙarasa yankan rabon hatsin da yake na sarki, hatsi na biyu kuma yake tohuwa.
This is what the Lord GOD showed me: He was preparing swarms of locusts just after the king’s harvest, as the late spring crop was coming up.
2 Sa’ad da suka cinye kome, sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ka gafarta! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”
And when the locusts had eaten every green plant in the land, I said, “Lord GOD, please forgive! How will Jacob survive, since he is so small?”
3 Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa. “Wannan ba zai faru ba,” in ji Ubangiji.
So the LORD relented from this plan. “It will not happen,” He said.
4 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji Mai Iko Duka yana shirin hukunta da wuta; wutar ta ƙone teku ta kuma ƙone ƙasa.
This is what the Lord GOD showed me: The Lord GOD was calling for judgment by fire. It consumed the great deep and devoured the land.
5 Sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ina roƙonka ka dakata! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”
Then I said, “Lord GOD, please stop! How will Jacob survive, since he is so small?”
6 Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa. “Wannan ma ba zai faru ba,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
So the LORD relented from this plan. “It will not happen either,” said the Lord GOD.
7 Ga abin da ya nuna mini. Ubangiji yana tsaye kusa da bangon da aka gina, bisa ga awon igiyar gwada gini, da kuma magwaji a hannunsa.
This is what He showed me: Behold, the Lord was standing by a wall true to plumb, with a plumb line in His hand.
8 Sai Ubangiji ya tambaye ni, “Me kake gani, Amos?” Sai na amsa, “Igiyar gwada gini.” Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Duba, zan sa igiyan nan a cikin mutanena Isra’ila; ba zan ƙara barinsu ba.
“Amos, what do you see?” asked the LORD. “A plumb line,” I replied. “Behold,” said the Lord, “I am setting a plumb line among My people Israel; I will no longer spare them:
9 “Za a hallakar da wuraren sujada na Ishaku kuma tsarkakan wurare na Isra’ila za su zama kango; da takobina zan tayar wa gidan Yerobowam.”
The high places of Isaac will be deserted, and the sanctuaries of Israel will be laid waste; and I will rise up against the house of Jeroboam with My sword.”
10 Sai Amaziya firist na Betel ya aika da saƙo zuwa wurin Yerobowam sarkin Isra’ila. “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a tsakiyar Isra’ila. Ƙasar ba za tă iya ɗauka abubuwan da yake faɗi ba.
Then Amaziah the priest of Bethel sent word to Jeroboam king of Israel, saying, “Amos has conspired against you in the midst of the house of Israel. The land cannot bear all his words,
11 Gama ga abin da Amos yake cewa, “‘Yerobowam zai mutu ta wurin takobi, kuma tabbatacce Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’”
for this is what Amos has said: ‘Jeroboam will die by the sword, and Israel will surely go into exile, away from their homeland.’”
12 Sai Amaziya ya ce wa Amos, “Tafi daga nan, mai duba kawai! Koma ƙasar Yahuda. Ka nemi abin zaman garinka a can ka kuma yi annabcinka a can.
And Amaziah said to Amos, “Go away, you seer! Flee to the land of Judah; earn your bread there and do your prophesying there.
13 Kada ka ƙara yin annabci a Betel, gama nan wuri mai tsarki ne na sarki da kuma haikalin ƙasar.”
But never prophesy at Bethel again, because it is the sanctuary of the king and the temple of the kingdom.”
14 Amos ya amsa wa Amaziya, “Ni ba annabi ba ne ko ɗan annabi, amma ni makiyayi ne, kuma ina lura da itatuwan al’ul.
“I was not a prophet,” Amos replied, “nor was I the son of a prophet; rather, I was a herdsman and a tender of sycamore-fig trees.
15 Amma Ubangiji ya ɗauke ni daga kiwon dabbobi ya ce mini, ‘Je ka, ka yi wa mutanena Isra’ila annabci.’
But the LORD took me from following the flock and said to me, ‘Go, prophesy to My people Israel.’
16 Yanzu fa, sai ka ji maganar Ubangiji. Ka ce, “‘Kada in yi annabci a kan Isra’ila, kuma in daina yin wa’azi a kan gidan Ishaku.’
Now, therefore, hear the word of the LORD. You say: ‘Do not prophesy against Israel; do not preach against the house of Isaac.’
17 “Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “‘Matarka za tă zama karuwa a cikin birni, kuma da takobi za a kashe’ya’yanka maza da mata. Za a auna ƙasarka a kuma raba ta, kai kuma za ka mutu a ƙasar arna. Ba shakka Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’”
Therefore this is what the LORD says: ‘Your wife will become a prostitute in the city, and your sons and daughters will fall by the sword. Your land will be divided by a measuring line, and you yourself will die on pagan soil. And Israel will surely go into exile, away from their homeland.’”

< Amos 7 >