< Amos 6 >

1 Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona, da ku waɗanda kuke ji zama a Dutsen Samariya lafiya ne, ku manyan mutanen ƙasar da take sananniya, waɗanda mutanen Isra’ila suke zuwa!
הוי השאננים בציון והבטחים בהר שמרון נקבי ראשית הגוים ובאו להם בית ישראל
2 Ku je Kalne ku dube ta; ku wuce daga can zuwa Hamat-rabba, sa’an nan ku gangara zuwa Gat a Filistiya. Sun fi masarautunku biyu ne? Ƙasarsu ta fi taku girma?
עברו כלנה וראו ולכו משם חמת רבה ורדו גת פלשתים הטובים מן הממלכות האלה--אם רב גבולם מגבלכם
3 Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan muguwar rana kuna kuma jawo mulkin tashin hankali kusa.
המנדים ליום רע ותגשון שבת חמס
4 Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa kuna mimmiƙe a kan kujerunku. Kuna cin naman ƙibabbun raguna da na ƙosassun’yan maruƙa.
השכבים על מטות שן וסרחים על ערשותם ואכלים כרים מצאן ועגלים מתוך מרבק
5 Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi kuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe.
הפרטים על פי הנבל כדויד חשבו להם כלי שיר
6 Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi kuna kuma shafa mai mafi kyau, amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama.
השתים במזרקי יין וראשית שמנים ימשחו ולא נחלו על שבר יוסף
7 Saboda haka za ku zama na farkon da za su tafi zaman bauta; bukukkuwanku da shagulgulanku za su ƙare.
לכן עתה יגלו בראש גלים וסר מרזח סרוחים
8 Ubangiji Mai Iko Duka da kansa ya rantse, Ubangiji Allah Maɗaukaki ya furta, “Ina ƙyamar girman kan Yaƙub, ba na kuma son kagarunsa; zan ba da birnin da duk abin da yake cikinta.”
נשבע אדני יהוה בנפשו נאם יהוה אלהי צבאות מתאב אנכי את גאון יעקב וארמנתיו שנאתי והסגרתי עיר ומלאה
9 Ko da mutum goma ne suka ragu a gida guda, su ma za su mutu.
והיה אם יותרו עשרה אנשים בבית אחד--ומתו
10 In kuma wani dangi ya shiga don yă fitar da gawawwakin yă ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, “Akwai wani tare da kai?” Ya kuwa ce, “Babu,” sai yă ce, “Kul! Kada mu ambaci sunan Ubangiji.”
ונשאו דודו ומסרפו להוציא עצמים מן הבית ואמר לאשר בירכתי הבית העוד עמך ואמר אפס ואמר הס כי לא להזכיר בשם יהוה
11 Gama Ubangiji ya ba da umarni, zai kuma ragargaza babban gidan nan kucu-kucu ƙaramin gidan kuwa zai yi rugu-rugu da shi.
כי הנה יהוה מצוה והכה הבית הגדול רסיסים והבית הקטן בקעים
12 Dawakai sukan yi gudu a kan duwatsu? Wani yana iya yin noma a teku da shanun noma? Amma ga shi kun mai da gaskiya ta zama dafi amfanin adalci kuma ya zama ɗaci,
הירצון בסלע סוסים אם יחרוש בבקרים כי הפכתם לראש משפט ופרי צדקה ללענה
13 ku da kuke murna saboda an ci Lo Debar da yaƙi kuka kuma ce, “Ba da ƙarfinmu ne muka ƙwace Karnayim ba?”
השמחים ללא דבר האמרים--הלוא בחזקנו לקחנו לנו קרנים
14 Gama Ubangiji Allah Maɗaukaki ya ce, “Zan sa wata ƙasa ta tayar muku, ya ku gidan Isra’ila, wadda za tă matsa muku tun daga Lebo Hamat zuwa kwarin Araba.”
כי הנני מקים עליכם בית ישראל נאם יהוה אלהי הצבאות--גוי ולחצו אתכם מלבוא חמת עד נחל הערבה

< Amos 6 >