< Amos 5 >

1 Ku ji wannan magana, ya gidan Isra’ila, ina makokin nan dominku.
שמעו את הדבר הזה אשר אנכי נשא עליכם קינה--בית ישראל
2 “Budurwa Isra’ila ta fāɗi, ba za tă ƙara tashi ba, an yashe ta a ƙasarta, ba wanda zai ɗaga ta.”
נפלה לא תוסיף קום בתולת ישראל נטשה על אדמתה אין מקימה
3 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Birnin da ta fitar da masu ƙarfi dubbai don Isra’ila guda ɗari kaɗai za su dawo; garin da ya fitar da masu ƙarfi ɗari kuwa goma kaɗai za su dawo.”
כי כה אמר אדני יהוה העיר היצאת אלף תשאיר מאה והיוצאת מאה תשאיר עשרה לבית ישראל
4 Ga abin da Ubangiji ya ce wa gidan Isra’ila. “Ku neme ni ku rayu;
כי כה אמר יהוה לבית ישראל דרשוני וחיו
5 kada ku nemi Betel, kada ku je Gilgal, kada ku yi tafiya zuwa Beyersheba. Gama ba shakka Gilgal za tă tafi bauta, za a kuwa mai da Betel ba kome ba.”
ואל תדרשו בית אל והגלגל לא תבאו ובאר שבע לא תעברו כי הגלגל גלה יגלה ובית אל יהיה לאון
6 Ku nemi Ubangiji ku kuma rayu, ko kuwa zai ratsa yă share gidan Yusuf kamar wuta; zai cinye Betel kuwa ba zai sami wanda zai kashe ta ba.
דרשו את יהוה וחיו פן יצלח כאש בית יוסף ואכלה ואין מכבה לבית אל
7 Ku ne masu mai da gaskiya ta koma ɗaci ku kuma zubar da adalci.
ההפכים ללענה משפט וצדקה לארץ הניחו
8 (Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare, wanda ya mai da duhu ya zama haske ya kuma baƙanta rana ta zama dare, yakan kwashe ruwan teku ya zubar a ƙasa, Ubangiji ne sunansa,
עשה כימה וכסיל והפך לבקר צלמות ויום לילה החשיך הקורא למי הים וישפכם על פני הארץ--יהוה שמו
9 yakan kawo hallaka a mafaka mai ƙarfi yakan kuma mai da birnin mai katanga ya zama kufai).
המבליג שד על עז ושד על מבצר יבוא
10 Ba ku son mai yin gaskiya a ɗakin shari’a kuna ƙin mai faɗar gaskiya.
שנאו בשער מוכיח ודבר תמים יתעבו
11 Kuna matsa wa matalauta kuna sa su dole su ba ku hatsi. Saboda haka, ko da yake kun gina gidajen duwatsu, ba za ku zauna a cikinsu ba; ko da yake kun nome gonaki masu kyau, ba za ku sha ruwan inabinsu ba.
לכן יען בושסכם על דל ומשאת בר תקחו ממנו--בתי גזית בניתם ולא תשבו בם כרמי חמד נטעתם ולא תשתו את יינם
12 Gama na san yawan laifofinku da kuma girman zunubanku. Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa.
כי ידעתי רבים פשעיכם ועצמים חטאתיכם צררי צדיק לקחי כפר ואביונים בשער הטו
13 Saboda haka mai hankali yakan yi shiru a lokuta kamar haka, gama lokutan mugaye ne.
לכן המשכיל בעת ההיא--ידם כי עת רעה היא
14 Ku yi nagarta, ba mugunta ba; don ku rayu sa’an nan Ubangiji Allah Maɗaukaki zai kasance da ku, kamar yadda kuka ce zai yi.
דרשו טוב ואל רע למען תחיו ויהי כן יהוה אלהי צבאות אתכם--כאשר אמרתם
15 Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta; ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a. Mai yiwuwa Ubangiji Allah Maɗaukaki zai ji tausayin raguwar Yusuf.
שנאו רע ואהבו טוב והציגו בשער משפט אולי יחנן יהוה אלהי צבאות--שארית יוסף
16 Saboda haka ga abin da Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa, “Za a yi kururuwa a dukan tituna a kuma yi kuka don azaba a dukan wuraren da jama’a sukan taru. Za a yi kira ga manoma su yi kuka masu makoki kuma su yi kuka.
לכן כה אמר יהוה אלהי צבאות אדני בכל רחבות מספד ובכל חוצות יאמרו הו הו וקראו אכר אל אבל ומספד אל יודעי נהי
17 Za a yi kuka a dukan gonakin inabi, gama zan ratsa a cikinku,” in ji Ubangiji.
ובכל כרמים מספד כי אעבר בקרבך אמר יהוה
18 Kaitonku masu son ganin ranar Ubangiji! Don me kuke son ganin ranar Ubangiji? Za a duhunta ranan nan, ba haske ba.
הוי המתאוים את יום יהוה למה זה לכם יום יהוה הוא חשך ולא אור
19 Za ku zama kamar mutanen da suka guje wa zaki sai suka fāɗa a hannun beyar, ko kuma kamar wanda ya shiga gida ya dāfa hannu a bango sai maciji ya sare shi.
כאשר ינוס איש מפני הארי ופגעו הדב ובא הבית--וסמך ידו על הקיר ונשכו הנחש
20 Ashe, ranar Ubangiji ba duhu ba ce, a maimakon haske, duhu wuluk, ba tare da ko ɗan haske ba.
הלא חשך יום יהוה ולא אור ואפל ולא נגה לו
21 “Na ƙi, ina kuma ƙyamar bukukkuwanku na addini; ba na son ganin tarurrukanku.
שנאתי מאסתי חגיכם ולא אריח בעצרתיכם
22 Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi, ba zan karɓa ba. Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta, ba zan ɗauke su a bakin kome ba.
כי אם תעלו לי עלות ומנחתיכם לא ארצה ושלם מריאיכם לא אביט
23 Ku tashi daga nan da surutan waƙoƙinku! Ba zan saurari kaɗe-kaɗe da bushe bushenku ba.
הסר מעלי המון שריך וזמרת נבליך לא אשמע
24 Amma bari gaskiya ta kwararo kamar kogi, adalci kuma kamar rafin da ba ya taɓa bushewa!
ויגל כמים משפט וצדקה כנחל איתן
25 “Kun kawo mini hadayu da sadakoki shekaru arba’in a cikin jeji, ya ku gidan Isra’ila?
הזבחים ומנחה הגשתם לי במדבר ארבעים שנה--בית ישראל
26 Kun ɗaga masujadar sarkinku, siffofin gumakanku, tauraron allahnku, wanda kuka yi wa kanku.
ונשאתם את סכות מלככם ואת כיון צלמיכם--כוכב אלהיכם אשר עשיתם לכם
27 Saboda haka zan tura ku zaman bauta gaba da Damaskus,” in ji Ubangiji, wanda sunansa ne Allah Mai Iko.
והגליתי אתכם מהלאה לדמשק אמר יהוה אלהי צבאות שמו

< Amos 5 >