< Amos 4 >
1 Ku kasa kunne ga wannan, ya ku shanun Bashan a kan Dutsen Samariya, ku matan da kuke cin zalin matalauta, kuke kuma danne matalauta, kuna kuma ce wa mazanku, “Ku kawo mana abin sha!”
2 Ubangiji Mai Iko Duka ya rantse da tsarkinsa. “Tabbatacce lokaci yana zuwa da za a jawo ku da ƙugiyoyi, na ƙarshenku za a kama da ƙugiyar kifi.
3 Dukanku za ku wuce ta kai tsaye ta inda katangar ta tsage, za a jefar da ku a Harmon,” in ji Ubangiji.
4 “Ku tafi Betel ku yi ta aikata zunubi; ku je Gilgal ku ƙara yin zunubi. Ku kawo hadayunku kowace safiya, zakkarku kowace shekara uku.
5 Ku ƙona burodinku mai yisti kamar hadaya ta godiya, ku yi fariya game da hadayunku na yarda rai, ku yi taƙama game da su, ya ku Isra’ilawa, gama abin da kuke jin daɗin aikata ke nan,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
6 “Na bar ku da yunwa a kowace birni, da kuma rashin abinci a kowane gari, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.
7 “Na kuma hana muku ruwan sama tun shuke-shuken suna wata uku kafin lokacin girbi. Na sa aka yi ruwan sama a wani gari, sai na hana a yi a wani gari. Wata gona ta sami ruwan sama; wata gona kuma ta bushe.
8 Mutane suna tangaɗi daga gari zuwa gari suna neman ruwa amma ba su sami isashen ruwan sha ba, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.
9 “Sau da yawa na ɓata gonakinku da fumfuna da kuma cuta. Fāri suka cinye itatuwanku na inabi da na ɓaure, da na zaitun duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.
10 “Na aiko muku annoba yadda na yi a Masar. Na karkashe samarinku da takobi, tare da kamammun dawakanku. Na cika hancinku da warin sansaninku, duk da haka ba ku juyo gare ni ba” in ji Ubangiji.
11 “Na hallaka waɗansunku kamar yadda na hallaka Sodom da Gomorra. Kuna kama da itace mai cin wutar da na cire daga cikin wuta, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.
12 “Saboda haka ga abin da zan yi da ku, ya Isra’ila, don kuwa zan yi muku haka, sai ku yi shirin gamuwa da Allahnku, ya Isra’ila.”
13 Shi wanda ya yi duwatsu, ya halicci iska, ya kuma bayyana wa mutum tunaninsa, shi wanda ya juya safiya ta zama duhu yana takawa a wurare masu tsawo na duniya, Ubangiji Allah Maɗaukaki ne sunansa.