< Amos 3 >

1 Ku ji wannan maganar da Ubangiji ya yi game da ku, ya ku jama’ar Isra’ila, a kan dukan iyalin da na fitar daga Masar.
שמעו את הדבר הזה אשר דבר יהוה עליכם--בני ישראל על כל המשפחה אשר העליתי מארץ מצרים לאמר
2 “Ku ne kaɗai na zaɓa cikin dukan al’umman duniya; saboda haka zan hukunta ku saboda dukan zunubanku.”
רק אתכם ידעתי מכל משפחות האדמה על כן אפקד עליכם את כל עונתיכם
3 Mutum biyu za su iya yin tafiya tare in ba su yarda su yi haka ba?
הילכו שנים יחדו בלתי אם נועדו
4 Zaki yakan yi ruri a jeji in bai sami kama nama ba? Zai yi gurnani a cikin kogonsa in bai kama kome ba?
הישאג אריה ביער וטרף אין לו היתן כפיר קולו ממענתו בלתי אם לכד
5 Tsuntsu yakan fāɗa a tarko a ƙasa inda ba a sa tarko ba, ko tarko yakan zargu daga ƙasa in ba abin da ya taɓa shi?
התפל צפור על פח הארץ ומוקש אין לה היעלה פח מן האדמה ולכוד לא ילכוד
6 Idan aka busa ƙaho a ciki birni mutane ba sa yin rawar jiki? Sa’ad da bala’i ya auko wa birni, ba Ubangiji ne ya sa a kawo shi ba?
אם יתקע שופר בעיר ועם לא יחרדו אם תהיה רעה בעיר ויהוה לא עשה
7 Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.
כי לא יעשה אדני יהוה דבר כי אם גלה סודו אל עבדיו הנביאים
8 Zaki ya yi ruri, wa ba zai tsorata ba? Ubangiji Mai Iko Duka ya yi magana, wa ba zai yi annabci ba?
אריה שאג מי לא יירא אדני יהוה דבר מי לא ינבא
9 Ku yi shela ga kagarun Ashdod da kuma ga kagarun Masar. “Ku tara kanku a tuddan Samariya; ku ga rashin jituwar da take a cikinta, da kuma zaluncin da ake yi a cikin mutanenta.”
השמיעו על ארמנות באשדוד ועל ארמנות בארץ מצרים ואמרו האספו על הרי שמרון וראו מהומת רבות בתוכה ועשוקים בקרבה
10 “Ba su ma san yadda za su yi abin da yake daidai ba,” in ji Ubangiji, “sun ɓoye ganima da abubuwan da suka washe a cikin kagarunsu.”
ולא ידעו עשות נכחה נאם יהוה האוצרים חמס ושד בארמנותיהם
11 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Abokin gāba zai ƙwace ƙasar, zai saukar da mafakarku, zai washe kagarunku.”
לכן כה אמר אדני יהוה צר וסביב הארץ והוריד ממך עזך ונבזו ארמנותיך
12 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zaki ƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya, haka za a ceci Isra’ilawa, masu zama a Samariya da kan gado kawai da kuma a ɗan ƙyalle a kan dogayen kujerunsu.”
כה אמר יהוה כאשר יציל הרעה מפי הארי שתי כרעים או בדל אזן--כן ינצלו בני ישראל הישבים בשמרון בפאת מטה ובדמשק ערש
13 “Ku ji wannan ku kuma yi wa gidan Yaƙub gargaɗi,” in ji Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki.
שמעו והעידו בבית יעקב--נאם אדני יהוה אלהי הצבאות
14 “A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta, zan hallaka bagadan Betel; za a yayyanka ƙahonin bagadan za su fāɗa ƙasa
כי ביום פקדי פשעי ישראל--עליו ופקדתי על מזבחות בית אל ונגדעו קרנות המזבח ונפלו לארץ
15 Zan rushe gidan rani da na damina; gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe su haka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,” in ji Ubangiji.
והכיתי בית החרף על בית הקיץ ואבדו בתי השן וספו בתים רבים--נאם יהוה

< Amos 3 >