< Amos 2 >

1 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Mowab, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Gama ya ƙone ƙasusuwan sarkin Edom suka zama sai ka ce toka.
כה אמר יהוה על שלשה פשעי מואב ועל ארבעה לא אשיבנו על שרפו עצמות מלך אדום לשיד
2 Zan sa wuta a Mowab da za tă ƙone kagarun Keriyot Mowab za tă gangara cikin hayaniya mai girma cikin kururuwar yaƙi da kuma ƙarar ƙaho.
ושלחתי אש במואב ואכלה ארמנות הקריות ומת בשאון מואב בתרועה בקול שופר
3 Zan hallaka mai mulkinta zan kuma kashe shugabanninta.”
והכרתי שופט מקרבה וכל שריה אהרוג עמו אמר יהוה
4 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Yahuda, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Gama sun ƙi bin dokar Ubangiji ba su kuma yi biyayya da ƙa’idodinsa ba, domin allolin ƙarya sun ruɗe su, allolin da kakanninsu suka bauta.
כה אמר יהוה על שלשה פשעי יהודה ועל ארבעה לא אשיבנו על מאסם את תורת יהוה וחקיו לא שמרו ויתעום כזביהם אשר הלכו אבותם אחריהם
5 Zan sa wuta a Yahuda da za tă ƙone kagarun Urushalima.”
ושלחתי אש ביהודה ואכלה ארמנות ירושלם
6 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Isra’ila, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun sayar da adalai waɗanda suka kāsa biyan bashinsu. Sun kuma sayar da matalauta waɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba.
כה אמר יהוה על שלשה פשעי ישראל ועל ארבעה לא אשיבנו על מכרם בכסף צדיק ואביון בעבור נעלים
7 Sun tattake kawunan matalauta kamar yadda suke taka laka suka kuma danne wa marasa galihu gaskiya. Uba da ɗa su na kwana da yarinya guda, suna kuma ɓata sunana mai tsarki.
השאפים על עפר ארץ בראש דלים ודרך ענוים יטו ואיש ואביו ילכו אל הנערה למען חלל את שם קדשי
8 Suna kwanciya kurkusa da kowane bagade a kan tufafin da suka karɓe jingina. A gidajen allolinsu sukan sha ruwan inabin da suka karɓo daga wurin waɗanda suka ci wa tara.
ועל בגדים חבלים יטו אצל כל מזבח ויין ענושים ישתו בית אלהיהם
9 “Na hallaka mutumin Amoriyawa a gabansu, ko da yake ya yi dogo kamar itacen al’ul kuma mai ƙarfi kamar itacen oak. Na hallaka’ya’yan itatuwansa daga sama, da kuma jijiyoyinsa daga ƙasa.
ואנכי השמדתי את האמרי מפניהם אשר כגבה ארזים גבהו וחסן הוא כאלונים ואשמיד פריו ממעל ושרשיו מתחת
10 Na fitar da ku daga ƙasar Masar, na kuma bishe ku tsawon shekaru arba’in a cikin hamada don in ba ku ƙasar Amoriyawa.
ואנכי העליתי אתכם מארץ מצרים ואולך אתכם במדבר ארבעים שנה לרשת את ארץ האמרי
11 “Na kuma tā da annabawa daga cikin’ya’yanku maza waɗansu kuma su zama keɓaɓɓu daga cikin samarinku. Ba haka ba ne, mutanen Isra’ila?” In ji Ubangiji.
ואקים מבניכם לנביאים ומבחוריכם לנזרים האף אין זאת בני ישראל נאם יהוה
12 “Amma kuka sa keɓaɓɓun suka sha ruwan inabi kuka kuma umarci annabawa kada su yi annabci.
ותשקו את הנזרים יין ועל הנביאים צויתם לאמר לא תנבאו
13 “Saboda haka, yanzu zan murƙushe ku kamar yadda amalanke yakan murƙushe sa’ad da aka yi masa labtun hatsi.
הנה אנכי מעיק תחתיכם כאשר תעיק העגלה המלאה לה עמיר
14 Masu gudu da sauri ba za su tsira ba, masu ƙarfi ba za su iya yin amfani da ƙarfinsu ba, jarumi kuma ba zai iya ceton ransa ba.
ואבד מנוס מקל וחזק לא יאמץ כחו וגבור לא ימלט נפשו
15 ’Yan baka ba za su iya dāgewa ba, masu saurin gudu ba za su tsira ba mahayin dawakai kuma ba zai tsere da ransa ba.
ותפש הקשת לא יעמד וקל ברגליו לא ימלט ורכב הסוס לא ימלט נפשו
16 Ko jarumawa mafi jaruntaka za su gudu tsirara a ranan nan,” in ji Ubangiji.
ואמיץ לבו בגבורים--ערום ינוס ביום ההוא נאם יהוה

< Amos 2 >