< Ayyukan Manzanni 5 >
1 To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa.
And a certain man, Ananias by name, with Sapphira his wife, sold a possession,
2 Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni.
and did keep back of the price — his wife also knowing — and having brought a certain part, at the feet of the apostles he laid [it].
3 Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin?
And Peter said, 'Ananias, wherefore did the Adversary fill thy heart, for thee to lie to the Holy Spirit, and to keep back of the price of the place?
4 Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”
while it remained, did it not remain thine? and having been sold, in thy authority was it not? why [is] it that thou didst put in thy heart this thing? thou didst not lie to men, but to God;'
5 Da Ananiyas ya ji wannan, sai ya fāɗi ya mutu. Sai babban tsoro kuwa ya kama duk waɗanda suka ji abin da ya faru.
and Ananias hearing these words, having fallen down, did expire, and great fear came upon all who heard these things,
6 Sai samari suka zo gaba, suka naɗe gawarsa, suka fitar da shi suka je suka binne.
and having risen, the younger men wound him up, and having carried forth, they buried [him].
7 Bayan kusan awa uku, sai matarsa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba.
And it came to pass, about three hours after, that his wife, not knowing what hath happened, came in,
8 Bitrus ya tambaye ta ya ce, “Gaya mini, kuɗin da yake da Ananiyas kuka sayar da filin ke nan?” Ta ce, “I, haka ne muka sayar.”
and Peter answered her, 'Tell me if for so much ye sold the place;' and she said, 'Yes, for so much.'
9 Bitrus ya ce mata, “Ta yaya kuka yarda ku gwada Ruhun Ubangiji? Duba! Sawun mutanen da suka binne mijinki suna bakin ƙofa, za su kuwa ɗauke ki zuwa waje ke ma.”
And Peter said unto her, 'How was it agreed by you, to tempt the Spirit of the Lord? lo, the feet of those who did bury thy husband [are] at the door, and they shall carry thee forth;'
10 Nan take ta fāɗi a ƙafafunsa ta mutu. Sai samarin suka shigo ciki, suka kuwa same ta matacciya, suka ɗauke ta suka kai ta waje suka binne ta kusa da mijinta.
and she fell down presently at his feet, and expired, and the young men having come in, found her dead, and having carried forth, they buried [her] by her husband;
11 Babban tsoro ya kama dukan ikkilisiya da kuma duk wanda ya ji game da abubuwan nan.
and great fear came upon all the assembly, and upon all who heard these things.
12 Manzannin suka yi ayyukan da alamu masu banmamaki masu yawa a cikin mutanen. Dukan masu bi kuwa sukan taru a Shirayin Solomon.
And through the hands of the apostles came many signs and wonders among the people, and they were with one accord all in the porch of Solomon;
13 Ba wanda ya yi karambanin shiga cikinsu, duk da haka mutane suna girmama su ƙwarai.
and of the rest no one was daring to join himself to them, but the people were magnifying them,
14 Duk da haka, maza da matan da suke gaskata ga Ubangiji sai ƙaruwa suke, suka kuma ƙaru a yawa.
(and the more were believers added to the Lord, multitudes both of men and women, )
15 A sakamakon haka, mutane suka kawo marasa lafiya a tituna suka kwantar da su a kan gadaje da tabarmai domin aƙalla inuwar Bitrus za tă bi kan waɗansunsu yayinda yake wucewa.
so as into the broad places to bring forth the ailing, and to lay [them] upon couches and mats, that at the coming of Peter, even [his] shadow might overshadow some one of them;
16 Jama’a ma suka tattaru daga garuruwa kewaye da Urushalima suna kawo marasa lafiyarsu da kuma waɗanda mugayen ruhohi suke damun su, dukansu kuwa suka warke.
and there were coming together also the people of the cities round about to Jerusalem, bearing ailing persons, and those harassed by unclean spirits — who were all healed.
17 Sai babban firist da dukan abokan aikinsa, waɗanda suke na ƙungiyar Sadukiyawa suka cika da kishi.
And having risen, the chief priest, and all those with him — being the sect of the Sadducees — were filled with zeal,
18 Suka kama manzannin suka sa su a kurkukun da ake sa kowa da kowa.
and laid their hands upon the apostles, and did put them in a public prison;
19 Amma da dare wani mala’ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun ya fitar da su.
and a messenger of the Lord through the night opened the doors of the prison, having also brought them forth, he said,
20 Ya ce, “Ku je ku tsaya a filin haikali ku sanar wa mutane cikakken saƙon wannan sabon rai.”
'Go on, and standing, speak in the temple to the people all the sayings of this life;'
21 Da gari ya waye, sai suka shiga filin haikali, yadda aka faɗa musu, suka kuwa fara koyar da mutane. Sa’ad da babban firist da abokan aikinsa suka iso, sai suka kira Majalisa gaba ɗaya dukan dattawan Isra’ila, suka kuma aika kurkuku a zo da manzannin.
and having heard, they did enter at the dawn into the temple, and were teaching. And the chief priest having come, and those with him, they called together the sanhedrim and all the senate of the sons of Israel, and they sent to the prison to have them brought,
22 Amma da dogarawan suka iso kurkukun, ba su same su a can ba. Saboda haka suka dawo suka ba da labari, suka ce,
and the officers having come, did not find them in the prison, and having turned back, they told,
23 “Mun iske kurkukun a kulle sosai, da masu gadi suna tsaye a bakin ƙofofin; amma da muka buɗe su, sai muka tarar ba kowa a ciki.”
saying — 'The prison indeed we found shut in all safety, and the keepers standing without before the doors, and having opened — within we found no one.'
24 Da jin wannan labari, sai shugaban masu gadin haikali da manyan firistocin suka ruɗe, suna tunanin abin da wannan al’amari zai zama.
And as the priest, and the magistrate of the temple, and the chief priests, heard these words, they were doubting concerning them to what this would come;
25 Sai wani ya zo ya ce, “Ga shi! Mutanen da kuka sa a kurkuku suna tsaye a filin haikali suna koya wa mutane.”
and coming near, a certain one told them, saying — 'Lo, the men whom ye did put in the prison are in the temple standing and teaching the people;'
26 Da wannan, shugaban ya tafi tare da dogarawansa suka kawo manzannin. Sun kawo su amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada mutane su jajjefe su da duwatsu.
then the magistrate having gone away with officers, brought them without violence, for they were fearing the people, lest they should be stoned;
27 Da suka kawo manzannin, sai suka sa su suka bayyana a gaban Majalisar don babban firist ya tuhume su.
and having brought them, they set [them] in the sanhedrim, and the chief priest questioned them,
28 Ya ce, “Mun kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa cikin wannan suna, duk da haka kun cika Urushalima da koyarwarku, har ma kuna so ku ɗora mana laifin jinin mutumin nan.”
saying, 'Did not we strictly command you not to teach in this name? and lo, ye have filled Jerusalem with your teaching, and ye intend to bring upon us the blood of this man.'
29 Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce, “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane!
And Peter and the apostles answering, said, 'To obey God it behoveth, rather than men;
30 Allahn kakanninmu ya tā da Yesu daga matattu, wanda kuka kashe ta wurin ratayewa a bisan itace.
and the God of our fathers did raise up Jesus, whom ye slew, having hanged upon a tree;
31 Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don yă kawo tuba da gafarar zunubai ga Isra’ila.
this one God, a Prince and a Saviour, hath exalted with His right hand, to give reformation to Israel, and forgiveness of sins;
32 Mu shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya ba wa waɗanda suke yin masa biyayya.”
and we are His witnesses of these sayings, and the Holy Spirit also, whom God gave to those obeying him.'
33 Da suka ji haka, sai suka yi fushi suka so su kashe su.
And they having heard, were cut [to the heart], and were taking counsel to slay them,
34 Amma wani Bafarisiyen da ake kira Gamaliyel, wani malamin doka, wanda dukan mutane ke girmamawa, ya miƙe tsaye a Majalisar ya umarta a fitar da mutanen waje na ɗan lokaci.
but a certain one, having risen up in the sanhedrim — a Pharisee, by name Gamaliel, a teacher of law honoured by all the people — commanded to put the apostles forth a little,
35 Sa’an nan ya yi musu jawabi ya ce, “Mutanen Isra’ila, ku yi kula da kyau da abin da kuke niyyar yi wa mutanen nan.
and said unto them, 'Men, Israelites, take heed to yourselves about these men, what ye are about to do,
36 Kwanan baya, Teyudas ya ɓullo, yana cewa wai shi wani mutum ne, kuma wajen mutane ɗari huɗu suka bi shi. Aka kuwa kashe shi, dukan masu binsa kuwa suka watse, kome ya wargaje.
for before these days rose up Theudas, saying, that himself was some one, to whom a number of men did join themselves, as it were four hundred, who was slain, and all, as many as were obeying him, were scattered, and came to nought.
37 Bayansa, Yahuda mutumin Galili ya ɓullo a kwanakin ƙidaya, ya jagoranci mutane cikin tawaye. Shi ma aka kashe shi, dukan mabiyansa kuma aka watsar da su.
'After this one rose up, Judas the Galilean, in the days of the enrolment, and drew away much people after him, and that one perished, and all, as many as were obeying him, were scattered;
38 Saboda haka, a wannan batu na yanzu, ina ba ku shawara. Ku ƙyale mutanen nan! Ku bar su su tafi! Gama in manufarsu ko ayyukansu na mutum ne, ai, zai rushe.
and now I say to you, Refrain from these men, and let them alone, because if this counsel or this work may be of men, it will be overthrown,
39 Amma in daga Allah ne, ba za ku iya hana waɗannan mutane ba, za ku dai sami kanku kuna gāba da Allah ne.”
and if it be of God, ye are not able to overthrow it, lest perhaps also ye be found fighting against God.'
40 Jawabinsa ya rinjaye su. Suka kira manzannin suka sa aka yi musu bulala. Sa’an nan suka kwaɓe su kada su ƙara magana a cikin sunan Yesu, suka kuma bar su suka tafi.
And to him they agreed, and having called near the apostles, having beaten [them], they commanded [them] not to speak in the name of Jesus, and let them go;
41 Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan.
they, indeed, then, departed from the presence of the sanhedrim, rejoicing that for his name they were counted worthy to suffer dishonour,
42 Kowace rana, a filin haikali da kuma gida-gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba.
every day also in the temple, and in every house, they were not ceasing teaching and proclaiming good news — Jesus the Christ.