< Ayyukan Manzanni 4 >
1 Sai firistoci da shugaban masu gadin haikalin da kuma Sadukiyawa suka hauro wurin Bitrus da Yohanna yayinda suke cikin magana da mutane.
While Peter and John were speaking to the people, the priests and the captain of the temple guard and the Sadducees came up to them,
2 Sun damu ƙwarai da gaske domin manzannin suna koya wa mutane suna kuma shela a cikin Yesu cewa akwai tashin matattu.
greatly disturbed that they were teaching the people and proclaiming in Jesus the resurrection of the dead.
3 Sai suka kama Bitrus da Yohanna, amma da yake yamma ta riga ta yi sai suka sa su cikin kurkuku sai kashegari.
They seized Peter and John, and because it was evening, they put them in custody until the next day.
4 Amma da yawa da suka ji saƙon suka gaskata, yawan mutanen kuwa ya ƙaru ya kai wajen dubu biyar.
But many who heard the message believed, and the number of men grew to about five thousand.
5 Kashegari, sai masu mulki, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru a Urushalima.
The next day the rulers, elders, and scribes assembled in Jerusalem,
6 Annas babban firist yana nan, haka ma Kayifas Yohanna, Alekzanda da kuma sauran mutanen da suke iyalin babban firist.
along with Annas the high priest, Caiaphas, John, Alexander, and many others from the high priest’s family.
7 Suka sa aka kawo Bitrus da Yohanna a gabansu suka kuma fara yin musu tambayoyi cewa, “Da wane iko ko da wane suna kuka yi wannan?”
They had Peter and John brought in and began to question them: “By what power or what name did you do this?”
8 Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki ya ce musu, “Masu mulki da dattawan mutane!
Then Peter, filled with the Holy Spirit, said to them, “Rulers and elders of the people!
9 In ana tuhumarmu ne yau saboda alherin da aka yi wa gurgun nan da kuma yadda aka warkar da shi,
If we are being examined today about a kind service to a man who was lame, to determine how he was healed,
10 to, sai ku san wannan, ku da dukan mutanen Isra’ila cewa da sunan Yesu Kiristi Banazare, wanda kuka gicciye amma wanda Allah ya tasar daga matattu ne, wannan mutum yake tsaye a gabanku lafiyayye.
then let this be known to all of you and to all the people of Israel: It is by the name of Jesus Christ of Nazareth, whom you crucified but whom God raised from the dead, that this man stands before you healed.
11 Shi ne, “‘dutsen da ku magina kuka ƙi, wanda kuwa ya zama dutsen kusurwar gini.’
This Jesus is ‘the stone you builders rejected, which has become the cornerstone.’
12 Ba a samun ceto ta wurin wani dabam, gama babu wani suna a ƙarƙashin sama da aka ba wa mutane wanda ta wurinsa dole mu sami ceto.”
Salvation exists in no one else, for there is no other name under heaven given to men by which we must be saved.”
13 Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu.
When they saw the boldness of Peter and John and realized that they were unschooled, ordinary men, they marveled and took note that these men had been with Jesus.
14 Amma da yake sun ga mutumin da aka warkar yana tsaye a wurin tare da su, sai suka rasa abin faɗi.
And seeing the man who had been healed standing there with them, they had nothing to say in response.
15 Saboda haka suka umarta a fitar da su daga Majalisar, sa’an nan suka yi shawara da juna.
So they ordered them to leave the Sanhedrin and then conferred together.
16 Suka ce, “Me za mu yi da waɗannan mutane? Kowa da yake zama a Urushalima ya san sun yi abin banmamaki, kuma ba za mu iya yin mūsu wannan ba.
“What shall we do with these men?” they asked. “It is clear to everyone living in Jerusalem that a remarkable miracle has occurred through them, and we cannot deny it.
17 Amma don a hana wannan abu daga ƙara bazuwa cikin mutane, dole mu kwaɓe mutanen nan kada su ƙara yi wa kowa magana cikin wannan suna.”
But to keep this message from spreading any further among the people, we must warn them not to speak to anyone in this name.”
18 Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu.
Then they called them in again and commanded them not to speak or teach at all in the name of Jesus.
19 Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shari’anta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah.
But Peter and John replied, “Judge for yourselves whether it is right in God’s sight to listen to you rather than God.
20 Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.”
For we cannot stop speaking about what we have seen and heard.”
21 Bayan ƙarin barazana sai suka bar su su tafi. Ba su iya yanke shawara yadda za a hore su ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.
After further threats they let them go. They could not find a way to punish them, because all the people were glorifying God for what had happened.
22 Gama mutumin da ya sami warkarwar banmamaki, shekarunsa sun fi arba’in.
For the man who was miraculously healed was over forty years old.
23 Da aka sake su, Bitrus da Yohanna suka koma wajen mutanensu suka ba da labarin duk abin da manyan firistoci da dattawa suka faɗa musu.
On their release, Peter and John returned to their own people and reported everything that the chief priests and elders had said to them.
24 Sa’ad da suka ji wannan, sai suka ɗaga muryoyinsu gaba ɗaya cikin addu’a ga Allah, suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai ka halicci sama da ƙasa da kuma teku, da kome da yake cikinsu.
When the believers heard this, they lifted up their voices to God with one accord. “Sovereign Lord,” they said, “You made the heaven and the earth and the sea and everything in them.
25 Ka yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin bawanka, kakanmu Dawuda cewa, “‘Don me ƙasashe suke fushi, mutane kuma suke ƙulla shawara a banza?
You spoke by the Holy Spirit through the mouth of Your servant, our father David: ‘Why do the nations rage and the peoples plot in vain?
26 Sarakunan duniya sun ja dāgā, masu mulki kuma sun taru gaba ɗaya, suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.’
The kings of the earth take their stand and the rulers gather together against the Lord and against His Anointed One.’
27 Tabbatacce Hiridus da Buntus Bilatus suka haɗu tare da Al’ummai da kuma mutanen Isra’ila a wannan birni ce don su ƙulla gāba da bawanka mai tsarki Yesu, wanda ka shafe.
In fact, this is the very city where Herod and Pontius Pilate conspired with the Gentiles and the people of Israel against Your holy servant Jesus, whom You anointed.
28 Sun aikata abin da ikonka da kuma nufinka ya riga ya shirya tuntuni zai faru.
They carried out what Your hand and will had decided beforehand would happen.
29 Yanzu, Ubangiji, ka dubi barazanansu ka kuma sa bayinka su furta maganarka da iyakar ƙarfin hali.
And now, Lord, consider their threats, and enable Your servants to speak Your word with complete boldness,
30 Ka miƙa hannunka don ka warkar ka kuma yi ayyukan banmamaki da alamu masu banmamaki ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.”
as You stretch out Your hand to heal and perform signs and wonders through the name of Your holy servant Jesus.”
31 Bayan suka yi addu’a, sai inda suka taru ya jijjigu. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta shaidar maganar Allah babu tsoro.
After they had prayed, their meeting place was shaken, and they were all filled with the Holy Spirit and spoke the word of God boldly.
32 Dukan masu bi kuwa zuciyarsu ɗaya ne, nufinsu kuwa ɗaya. Babu wani da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, amma sun raba kome da suke da shi.
The multitude of believers was one in heart and soul. No one claimed that any of his possessions was his own, but they shared everything they owned.
33 Da iko mai ƙarfi manzanni suka ci gaba da shaidar tashin matattu na Ubangiji Yesu, alheri mai yawa kuwa yana bisansu duka.
With great power the apostles continued to give their testimony about the resurrection of the Lord Jesus. And abundant grace was upon them all.
34 Babu mabukata a cikinsu. Lokaci-lokaci waɗanda suke da gonaki ko gidaje sukan sayar da su, su kawo kuɗi daga abin da suka sayar,
There were no needy ones among them, because those who owned lands or houses would sell their property, bring the proceeds from the sales,
35 su ajiye a sawun manzannin, a kuma raba wa kowa gwargwadon bukatarsa.
and lay them at the apostles’ feet for distribution to anyone as he had need.
36 Yusuf, wani Balawe daga Saifurus, wanda manzanni suke kira Barnabas (wanda yake nufin Ɗan Ƙarfafawa)
Joseph, a Levite from Cyprus, whom the apostles called Barnabas (meaning Son of Encouragement),
37 ya sayar da wata gonar da ya mallaki ya kuma kawo kuɗin ya ajiye a sawun manzanni.
sold a field he owned, brought the money, and laid it at the apostles’ feet.