< Ayyukan Manzanni 26 >
1 Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “An ba ka izini ka yi magana.” Saboda haka Bulus ya yi alama da hannunsa ya fara kāriyarsa.
Hivyo, Agripa akamwambia Paulo, `Unaruhusiwa kujitetea. ' Ndipo Paulo akanyoosha mkono wake akajitetea hivi.
2 Ya ce, “Sarki Agiriffa, na yi sa’a da na tsaya a gabanka yau yayinda nake kāriyata game da dukan zargin Yahudawa,
“Najiona mwenye furaha, Mfalme Agripa, ili kufanya kesi yangu mbele yako leo dhidi ya mashtaka yote ya Wayahudi.
3 musamman ma domin ka saba sosai da dukan al’adun Yahudawa da kuma maganganunsu. Saboda haka ina roƙonka ka saurare ni da haƙuri.
Hasa, kwa sababu wewe ni mtaalamu wa desturi za Wayahudi na maswali. Hivyo naomba unisikilize kwa uvumilivu.
4 “Yahudawa duk sun san yadda na yi rayuwa tun ina yaro, daga farkon rayuwata a ƙasarmu da kuma a Urushalima.
Kweli, Wayahudi wote wanajua jinsi nilivyoishi tangu ujana wangu katika taifa langu huko Yerusalemu.
5 Sun san ni tun da daɗewa za su kuwa shaida, in suna so, cewa bisa ga ɗarikar addininmu mafi tsanani, na yi rayuwar Bafarisiye ne.
Wananijua tangu mwanzo na wanapaswa kukubali kwamba niliishi kama Mfarisayo, dhehebu lenye msimamo mkali kwenye dini yetu.
6 Yanzu kuwa saboda begena cikin abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari ne, ake mini shari’a yau.
Sasa nimesimama hapa nihukumiwe kwa sababu mimi naliangalia ahadi ambayo Mungu aliifanya na baba zetu.
7 Wannan shi ne alkawarin da kabilanmu goma sha biyu suke bege su ga cikawarsa, yayinda suke bauta wa Allah da himma dare da rana. Ya Sarki, saboda wannan bege ne fa Yahudawa suke zargena.
Hii ni ahadi ambayo makabila yetu kumi na mbili yanatumaini kupokea kama wakimwabudu Mungu kwa bidii usiku na mchana. Ni kwa ajili ya tumaini hili, mfalme Agripa, kwamba Wayahudi wananishitaki.
8 Don me wani a cikinku zai yi shakka cewa Allah yana tā da matattu?
Kwa nini yeyote kati yenu anafikiri ni ajabu kwamba Mungu hufufua wafu?
9 “Ni ma a dā na tabbata cewa ya kamata in yi duk abin da zan iya yi domin in yi gāba da sunan Yesu Banazare.
Wakati mmoja nilifikiria mwenyewe kwamba ningefanya mambo mengi dhidi ya jina la Yesu wa Nazareti.
10 Abin da na yi ke nan a Urushalima. Da izinin manyan firistoci na sa tsarkaka da yawa a kurkuku, sa’ad da kuma ake kashe su, nakan ka da ƙuri’ata gāba da su.
Nilifanya haya katika Yerusalemu; Niliwafunga waamini wengi gerezani, na nilikuwa na mamlaka kutoka kwa wakuu wa makuhani kufanya hivyo; na wakati wanauawa, nilipiga kura dhidi yao.
11 Sau da dama nakan bi majami’a-majami’a, in sa a yi musu hukunci. Na kuma yi ƙoƙarin tilasta su su yi saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.
Mara nyingi niliwaadhibu katika masinagogi yote na nilijaribu kuwafanya waikane imani yao. Nilikuwa na hasira sana juu yao na niliwafukuza hata katika miji ya ugenini.
12 “A cikin irin tafiye-tafiyen nan ne ina kan hanya zuwa Damaskus tare da izini daga manyan firistoci.
Wakati nilipokuwa nikifanya haya, nilienda Dameski, nikiwa na mamlaka na maagizo kutoka kwa makuhani wakuu;
13 Da tsakar rana, ya sarki, sa’ad da nake kan hanya, sai na ga wani haske daga sama, fiye da hasken rana, yana haskakawa kewaye da ni da abokan tafiyata.
nilipokuwa njiani wakati wa mchana, Mfalme, niliona mwanga kutoka mbinguni uliokuwa mkali kuliko jua na uling'aa kutuzunguka mimi na watu waliokuwa wakisafiri pamoja nami.
14 Dukanmu muka fāɗi ƙasa, na kuwa ji wata murya tana ce mini da harshen Arameyik, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Yana da wuya ka shuri tsinken tsokanar dabba.’
Sisi sote tulipoanguka chini, nalisikia sauti ikizungumza na mimi ikisema katika lugha ya Kiebrania: `Sauli, Sauli! Kwa nini unanitesa? Ni vigumu kwako kuupiga teke mchokoo.
15 “Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ “Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.
Ndipo nikasema, 'Wewe ni nani, Bwana?' Bwana akajibu, 'Mimi ni Yesu ambaye unanitesa.
16 Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka.
Sasa inuka usimame kwa miguu yako; sababu kwa kusudi hili mimi nimeonekana kwako, nimekuteua kuwa mtumishi na shahidi juu ya mambo ambayo unajua kuhusu mimi sasa na mambo nitakayokuonyesha baadaye;
17 Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Al’ummai. Ina aikan ka zuwa gare su domin
na Nitakuokoa kutoka kwa watu na watu wa Mataifa ambapo ninakutuma,
18 ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’
kufungua macho yao na kuwatoa gizani kwenda kwenye mwanga na kutoka kwenye nguvu za shetani wamgeukie Mungu; ili wapate kupokea kutoka kwa Mungu msamaha wa dhambi na urithi ambao nimewapa wale niliowatenga kwa imani iliyo kwangu.
19 “Saboda haka fa, Sarki Agiriffa, ban yi rashin biyayya ga wahayin nan daga sama ba.
Hivyo, mfalme Agripa, sikuweza kuasi maono ya mbinguni,
20 Da farko ga waɗanda suke a Damaskus, sa’an nan ga waɗanda suke a Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya, da kuma ga Al’ummai su ma, na yi wa’azi don su tuba su juyo ga Allah su kuma tabbatar da tubansu ta wurin ayyukansu.
lakini, kwa wale walio katika Dameski kwanza, na kisha Yerusalemu na nchi yote ya Yudea, na pia kwa watu wa mataifa mengine, nilihubiri kwamba watubu na kumgeukia Mungu, wafanye matendo yanayostahili toba.
21 Shi ya sa Yahudawa suka kama ni a filin haikali suka kuma yi ƙoƙarin kashe ni.
Kwa sababu hiyo Wayahudi walinikamata hekaluni, wakajaribu kuniua.
22 Amma na sami taimakon Allah har yă zuwa yau. Yanzu ga ni a tsaye a nan, ina shaida ga babba da yaro. Ba na faɗin kome fiye da abin da annabawa da Musa suka ce zai faru,
Mungu amenisaidia mpaka sasa, hivyo nasimama na kushuhudia kwa watu wa kawaida na kwa wale wakubwa juu ya yale ambayo manabii na Musa walisema yatatokea na si vingine;
23 cewa Kiristi zai sha wahala, kuma a matsayin wanda yake na fari da zai tashi daga matattu, zai yi shelar haske ga mutanensa da kuma Al’ummai.”
kwamba Kristo lazima atateseka na atakuwa wa kwanza kufufuka kutoka kwa wafu na kutangaza mwanga kwa Wayahudi na watu wa mataifa.
24 A nan ne fa Festus ya tsai da kāriyar Bulus. Ya yi ihu ya ce, “Bulus! Kai dai ruɗaɗɗe ne, yawan karatunka yana juya maka kai.”
Paulo alipomaliza kujitetea, Festo alisema kwa sauti kubwa, 'Paulo, wewe ni mwendawazimu! masomo yako yamekufanya uwe mwendawazimu.
25 Bulus ya amsa ya ce, “Ba na hauka, ya mafifici Festus. Abin da nake faɗi gaskiya ne da kuma mai kyau.
Lakini Paulo akasema, Mimi si mwendawazimu, mheshimiwa Festo; lakini kwa ujasiri nasema maneno ya ukweli mtupu.
26 Sarki ya san waɗannan abubuwa, ina kuma iya yin magana da shi a sake. Na tabbata cewa ba ɗaya daga cikin waɗannan da ya kuɓuce saninsa, domin ba a ɓoye aka yi shi ba.
Kwa kuwa mfalme anajua kuhusu mambo haya; na hivyo, ninaongea kwa uhuru kwake, kwa maana nina hakika kwamba hakuna lolote lililofichwa kwake; kwa kuwa hili halijafanywa pembeni.
27 Sarki Agiriffa ka gaskata da annabawa? Na san ka gaskata.”
Je, unaamini manabii, Mfalme Agripa? Najua kwamba unaamini. '
28 Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “Kana tsammani cewa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kana so ka mai da ni Kirista?”
Agripa akamwambia Paulo, 'Kwa muda mfupi unaweza kunishawishi mimi na kunifanya Mkristo?
29 Bulus ya amsa ya ce, “Ko a ɗan lokaci, ko a lokaci mai yawa, ina addu’a ga Allah cewa, ba kai kaɗai ba amma duk waɗanda suke saurare ni a yau su zama abin da nake, sai dai ban da sarƙoƙin nan.”
Paulo akasema, '“Namwomba Mungu kwamba, kwa muda mfupi au mrefu, si wewe tu, bali pia wote wanaonisikia leo, wawe kama mimi, lakini bila hii minyororo ya gerezani.”
30 Sai sarki ya tashi, haka kuma gwamna da Bernis da kuma waɗanda suke zaune tare da su.
Ndipo mfalme alisimama, na liwali, na Bernike pia, na wale waliokuwa wamekaa pamoja nao,
31 Suka bar ɗakin, kuma yayinda suke magana da juna, sai suka ce, “Wannan mutum ba ya yin kome da ya isa kisa ko dauri.”
walipoondoka ukumbini, walizungumzia wao kwa wao na kusema, 'Mtu huyu hastahili kifo wala kifungo.'
32 Sai Agiriffa ya ce wa Festus, “Da ba don wannan mutum ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba da an sake shi.”
Agripa akamwambia Festo, “Mtu huyu angeweza kuwekwa huru kama asingekata rufani kwa Kaisari.”