< Ayyukan Manzanni 24 >

1 Bayan kwana biyar sai Ananiyas babban firist ya tafi Kaisariya tare da waɗansu daga cikin dattawa da kuma wani lauya mai suna Tertullus, suka kawo ƙararsu game da Bulus a gaban gwamna.
Five days later the high priest Ananias came down with some elders and a lawyer named Tertullus, who presented to the governor their case against Paul.
2 Sa’ad da aka shigo da Bulus, sai Tertullus ya shiga kai ƙararsa a gaban Felis yana cewa, “Mun daɗe muna zaman lafiya a ƙarƙashinka, hangen nesanka kuma ya kawo gyare-gyare a wannan ƙasa.
When Paul had been called in, Tertullus opened the prosecution: “Because of you, we have enjoyed a lasting peace, and your foresight has brought improvements to this nation.
3 Ko’ina da kuma a kowace hanya, ya mafifici Felis, mun amince da wannan da godiya marar iyaka.
In every way and everywhere, most excellent Felix, we acknowledge this with all gratitude.
4 Amma don kada in ƙara gajiyar da kai, ina roƙonka ka yi haƙuri ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabinmu.
But in order not to burden you any further, I beg your indulgence to hear us briefly.
5 “Mun tarar da wannan mutum fitinanne ne, yana tā-da-na-zaune-tsaye a tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya. Shi shugaban ɗarikar Nazarawa
We have found this man to be a pestilence, stirring up dissension among the Jews all over the world. He is a ringleader of the sect of the Nazarenes,
6 har ma ya yi ƙoƙari ya ƙazantar da haikali; shi ya sa muka kama shi.
and he even tried to desecrate the temple; so we seized him.
7
8 Ta wurin bincika shi da kanka za ka gane gaskiyar game da dukan waɗannan zargin da muke kawo a kansa.”
By examining him yourself, you will be able to learn the truth about all our charges against him.”
9 Yahudawa ma suka goyi bayan zargin, suna tabbatar cewa waɗannan abubuwa haka suke.
The Jews concurred, asserting that these charges were true.
10 Da gwamna ya yi masa alama yă yi magana, sai Bulus ya amsa ya ce, “Na san cewa ka yi shekaru da yawa kana mulki a wannan ƙasa; saboda haka ina farin ciki in kāre kaina.
When the governor motioned for Paul to speak, he began his response: “Knowing that you have been a judge over this nation for many years, I gladly make my defense.
11 Da sauƙi za ka iya tabbatar cewa, bai fi kwana goma sha biyu da suka wuce ne na tafi Urushalima, domin yin sujada ba.
You can verify for yourself that no more than twelve days ago I went up to Jerusalem to worship.
12 Masu zargina ba su same ni ina gardama da kowa a haikali, ko kuma ina tā da hankalin jama’a a majami’u ko kuwa wani wuri dabam a cikin birni ba.
Yet my accusers did not find me debating with anyone in the temple or riling up a crowd in the synagogues or in the city.
13 Ba kuwa za su iya tabbatar maka ƙarar da suke yi yanzu a kaina ba.
Nor can they prove to you any of their charges against me.
14 Amma na yarda cewa ina bauta wa Allah na kakanninmu a matsayin mai bin Hanyar da suke kira ɗarika. Na gaskata dukan abin da ya amince da Doka da yake kuma a rubuce cikin Annabawa,
I do confess to you, however, that I worship the God of our fathers according to the Way, which they call a sect. I believe everything that is laid down by the Law and written in the Prophets,
15 ina kuma da irin bege ɗaya ga Allah yadda mutanen nan suke da shi, cewa akwai tashin matattu masu adalci da masu mugunta duka.
and I have the same hope in God that they themselves cherish, that there will be a resurrection of both the righteous and the wicked.
16 Saboda haka, ina ƙoƙari kullum in kasance da lamiri mai tsabta a gaban Allah da mutane.
In this hope, I strive always to maintain a clear conscience before God and man.
17 “Bayan’yan shekaru da dama da ba na nan, sai na dawo Urushalima don in kawo wa mutanena kyautai saboda matalauta in kuma yi sadaka.
After several years, then, I returned to Jerusalem to bring alms to my people and to present offerings.
18 Ni tsarkake ne sa’ad da suka same ni cikin filin haikalin ina yin haka. Babu taro tare da ni, ba kuwa ina tā da hankali ba.
At the time they found me in the temple, I was ceremonially clean and was not inciting a crowd or an uproar. But there are some Jews from the province of Asia
19 Amma akwai waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya, waɗanda ya kamata suna a nan a gabanka su kawo ƙara in suna da wani a kaina.
who ought to appear before you and bring charges, if they have anything against me.
20 Ko kuwa waɗannan da suke a nan su faɗi laifin da suka same ni da shi sa’ad da na tsaya a gaban Majalisa,
Otherwise, let these men state for themselves any crime they found in me when I stood before the Sanhedrin,
21 sai ko wannan abu ɗaya kaɗai da na ɗaga murya na faɗi yayinda nake tsaye a gabansu cewa, ‘A game da tashin matattu ake mini shari’a a gabanku yau.’”
unless it was this one thing I called out as I stood in their presence: ‘It is concerning the resurrection of the dead that I am on trial before you today.’”
22 Sai Felis, wanda yake da cikakken sani game da Hanyar, ya ɗaga sauraron ƙarar. Ya ce, “In Lisiyas shugaban ƙungiyar soja ya iso, zan yanke muku shari’a.”
Then Felix, who was well informed about the Way, adjourned the hearing and said, “When Lysias the commander comes, I will decide your case.”
23 Ya yi wa jarumin umarni yă tsare Bulus amma yă ba shi’yanci yă kuma bar abokansa su lura da bukatunsa.
He ordered the centurion to keep Paul under guard, but to allow him some freedom and permit his friends to minister to his needs.
24 Bayan’yan kwanaki da dama sai Felis ya zo da matarsa Durusilla, mutuniyar Yahuda. Sai ya aika a zo da Bulus ya kuma saurare shi da yake magana game da bangaskiya cikin Kiristi Yesu.
After several days, Felix returned with his wife Drusilla, who was a Jewess. He sent for Paul and listened to him speak about faith in Christ Jesus.
25 Da Bulus ya ci gaba jawabi a kan adalci, kamunkai da kuma hukunci mai zuwa, sai Felis ya tsorata ya ce, “Yanzu kam, ya isa haka! Kana iya tafi. In na sami zarafi, zan kira ka.”
As Paul expounded on righteousness, self-control, and the coming judgment, Felix became frightened and said, “You may go for now. When I find the time, I will call for you.”
26 A wani fanni yana sa rai cewa Bulus zai ba shi toshiyar baki, saboda haka ya yi ta aika a kira masa Bulus yă yi magana da shi.
At the same time, he was hoping that Paul would offer him a bribe. So he sent for Paul frequently and talked with him.
27 Da shekaru biyu suka wuce, sai Forsiyus Festus, ya gāji Felis, amma domin Felis ya so yă biya wa Yahudawa bukata, sai ya bar Bulus a kurkuku.
After two years had passed, Felix was succeeded by Porcius Festus. And wishing to do the Jews a favor, Felix left Paul in prison.

< Ayyukan Manzanni 24 >