< Ayyukan Manzanni 22 >
1 “’Yan’uwa da iyaye, ku saurari kāriyata yanzu.”
2 Da suka ji ya yi musu magana da Arameyik, sai suka yi tsit. Sai Bulus ya ce,
3 “Ni mutumin Yahuda ne haifaffen Tarshish na Silisiya, amma a nan birnin ne aka rene ni. Aka horar da ni sosai cikin dokokin kakanninmu a ƙarƙashin Gamaliyel ni ma dā mai himma ne cikin bauta wa Allah kamar yadda kowannenku yake a yau.
4 Na tsananta wa masu bin wannan Hanyar har ga mutuwarsu, ina kama maza da mata ina kuma jefa su cikin kurkuku,
5 kamar yadda babban firist da dukan Majalisa za su iya shaida. Na ma karɓi wasiƙu daga gare su zuwa ga’yan’uwansu a Damaskus, na kuma tafi can don in kawo waɗannan mutane a daure zuwa Urushalima don a hukunta su.
6 “Wajen tsakar rana da na yi kusa da Damaskus, ba zato ba tsammani sai wani babban haske daga sama ya haskaka kewaye da ni.
7 Sai na fāɗi a ƙasa na kuma ji wata murya ta ce mini, ‘Shawulu! Shawulu! Don me kake tsananta mini?’
8 “Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ “Ya amsa ya ce, ‘Ni ne Yesu Banazare, wanda kake tsanantawa.’
9 Abokan tafiyata suka ga hasken, amma ba su fahimci muryar mai magana da ni ba.
10 “Sai na yi tambaya, na ce, ‘Me zan yi, ya Ubangiji?’ “Ubangiji ya ce, ‘Tashi, ka tafi cikin Damaskus. A can za a faɗa maka duk abin da aka shirya za ka yi.’
11 Abokan tafiyata suka ja ni a hannu zuwa cikin Damaskus, saboda ƙarfin hasken ya makanta ni.
12 “Wani mutumin da ake kira Ananiyas ya zo ya gan ni. Shi mai ibada ne wajen kiyaye dokoki wanda dukan Yahudawan da suke zama a can suna girmama shi ƙwarai.
13 Ya tsaya kusa da ni ya ce, ‘Ɗan’uwa Shawulu, ka sami ganin garinka!’ A daidai lokacin kuwa na iya ganinsa.
14 “Sa’an nan ya ce, ‘Allah na kakanninmu ya zaɓe ka ka san nufinsa ka kuma ga Mai Adalcin nan ka kuma ji kalmomi daga bakinsa.
15 Za ka zama mai shaidarsa ga dukan mutane game da abin da ka gani ka kuma ji.
16 Yanzu me kake jira? Ka tashi, a yi maka baftisma, a wanke zunubanka, ta wurin kira bisa ga sunansa.’
17 “Sa’ad da na dawo Urushalima ina cikin addu’a a haikali, sai na ga wahayi
18 na ga Ubangiji yana magana. Ya ce mini, ‘Maza! Ka bar Urushalima, gama ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.’
19 “Na amsa na ce, ‘Ubangiji, waɗannan mutane sun san cewa na bi majami’a-majami’a na jefa waɗanda suka gaskata da kai a cikin kurkuku, in kuma yin musu dūka.
20 Sa’ad da kuma aka zub da jinin Istifanus mashaidinka, na tsaya can ina ba da goyon bayana ina kuma tsaron tufafin masu kisansa.’
21 “Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, ‘Je ka; zan aike ka can nesa a wurin Al’ummai.’”
22 Taron suka saurari Bulus sai da ya yi wannan magana. Sa’an nan suka ɗaga muryoyinsu suka yi ihu suka ce, “A raba duniya da wannan mutum! Bai cancanci yă rayu ba!”
23 Da suna ihu suna kaɗa mayafansu suna da tā da ƙura sama,
24 sai shugaban ƙungiyar sojan ya umarta a kai Bulus a barikin soja. Ya ba da umarni a yi masa bulala a kuma tambaye shi abin da ya sa mutane suke masa ihu haka.
25 Suna kwantar da shi ke nan domin a yi masa bulala, sai Bulus ya ce wa jarumin da yake tsaye a nan, “Ashe, daidai ne bisa ga doka a yi wa ɗan ƙasar Roma bulala wanda ba a ma tabbatar da laifi a kansa ba?”
26 Da jarumin ya ji haka sai ya je wurin shugaban ƙungiyar sojan ya ce masa, “Me kake so yi ne? Wannan mutum ɗan ƙasar Roma ne.”
27 Sai shugaban ƙungiyar sojan ya je ya tambayi Bulus ya ce, “Faɗa mini, kai ɗan ƙasar Roma ne?” Bulus ya ce, “I.”
28 Sai shugaban ƙungiyar sojan ya ce, “Sai da na biya kuɗi mai yawa kafin in zama ɗan ƙasa.” Bulus ya ce, “Ni kuwa an haife ni ɗan ƙasa.”
29 Waɗanda dā suke shirin yin masa tambayoyi suka ja da baya nan da nan. Shugaban ƙungiyar sojan kansa ya tsorata da ya fahimci cewa ya sa wa Bulus, ɗan ƙasar Roma sarƙa.
30 Kashegari da yake shugaban ƙungiyar sojan ya so yă tabbatar da ainihin abin da ya sa Yahudawa suke zargin Bulus, sai ya sake shi ya kuwa umarci manyan firistoci da dukan Majalisar su taru. Sa’an nan ya kawo Bulus ya sa ya tsaya a gabansu.