< Ayyukan Manzanni 2 >

1 Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya.
And when the day of Pentecost had fully come, they were all with one consent in one place.
2 Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune.
And suddenly there came from heaven a sound as of a rushing, violent wind, and it filled the whole house in which they were sitting.
3 Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu.
And there appeared to them tongues like fire, which distributed themselves, and sat one on each of them.
4 Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.
And they were all filled with the Holy Spirit, and began to speak with other tongues, as the Spirit gave them utterance.
5 To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya.
Now there were dwelling in Jerusalem devout Jews, from every nation under heaven.
6 Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa.
When the report of this had gone abroad, the multitude came together; and they were perplexed, for each one heard them speak in his own language.
7 Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne?
They were amazed and astonished, and said one to another: Are not all these that are speaking, Galileans?
8 To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa?
And how is it that we hear, every one in our own language in which we were born―
9 Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya,
Parthians and Modes and Elamites, and we who dwell in Mesopotamia, Judea, and Cappadocia, Pontus and Asia,
10 Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma
Phrygia and Pamphylia, Egypt and the parts of Libya about Cyrene, Roman residents, Jews and proselytes,
11 (Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!”
Cretes and Arabians―we hear them speaking, in our own tongues, the wonderful works of God?
12 A ruɗe kuma cike da mamaki, suka tambayi junansu cewa, “Mene ne wannan yake nufi?”
And they were all in amazement and doubt, and said, one to another: What can this mean?
13 Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.”
But others deriding, said: They are full of new wine.
14 Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa.
But Peter standing up with the eleven, lifted up his voice and said to them: Men of Judea, and all you that dwell in Jerusalem, be this known to you, and give ear to my words.
15 Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai!
For these men are not drunk, as you suppose: for it is the third hour of the day.
16 A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa,
But this is that which was spoken of by the prophet Joel:
17 “Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe, zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane.’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, samarinku za su ga wahayoyi, dattawanku kuma za su yi mafarkai.
And it shall come to pass in the last days, says God, that I will pour out of my Spirit on all flesh; and your sons and your daughters shall prophesy, and your young men shall see visions, and your old men shall dream dreams.
18 Kai, har ma a kan bayina, maza da mata, zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki, za su kuwa yi annabci.
And also on my servants and on my handmaids, I will pour out of my Spirit in those days, and they shall prophesy.
19 Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama da alamu a nan ƙasa, jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi.
And I will show wonders in heaven above, and signs in the earth beneath, blood and fire and columns of smoke.
20 Za a mai da rana duhu, wata kuma ya zama jini, kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji.
The sun shall be turned into darkness, and the moon into blood, before that great and terrible day of the Lord comes.
21 Kuma duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’
And it shall come to pass, that whoever shall call on the name of the Lord shall be saved.
22 “Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani.
Men of Israel, hear these words: Jesus the Nazarene, clearly pointed out to you as a man from God, by mighty deeds and wonders and signs, which God did by him in your midst, as you yourselves also know,
23 An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye.
him, delivered up by the fixed purpose and foreknowledge of God, you took, and with wicked hands did crucify and slay:
24 Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya’yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.
whom God raised up, having loosed the pains of death, because it was not possible for him to be held in subjection by it.
25 Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa, “‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana. Gama yana a hannuna na dama, ba zan jijjigu ba.
For David speaks with reference to him: I saw the Lord always in my presence: for he is at my right hand, that I should not be moved.
26 Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna, jikina kuma zai kasance da bege,
Therefore my heart rejoiced, and my tongue sang praise. Moreover, my flesh shall rest in hope;
27 gama ba za ka bar ni cikin kabari ba, ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba. (Hadēs g86)
because thou wilt not leave my soul in hades, nor suffer thy Holy One to see corruption. (Hadēs g86)
28 Ka sanar da ni hanyoyin rai, za ka cika ni da farin ciki a gabanka.’
Thou didst make known to me the ways of life; thou wilt make me full of joy with thy countenance.
29 “’Yan’uwa, zan iya tabbatar muku gabagadi cewa kakanmu Dawuda ya mutu aka kuma binne shi, kabarinsa kuwa yana a nan har yă zuwa yau.
Brethren, I may say to you plainly of the patriarch David, that he died, and was buried, and his sepulcher is with us to this day.
30 Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa.
Therefore, being a prophet, and knowing that God had sworn to him with an oath, that he would cause one from the fruit of his loins to sit on his throne;
31 Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba. (Hadēs g86)
foreseeing this, he spoke of the resurrection of the Christ, that his soul was not left in hades, nor did his flesh see corruption. (Hadēs g86)
32 Allah ya tashe wannan Yesu zuwa rai, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan.
This Jesus has God raised up, of which we all are witnesses.
33 An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji.
Therefore, having been exalted to the right hand of God, and having received from his Father the promise of the Holy Spirit, he has poured out this, which you now see and hear.
34 Gama Dawuda bai hau zuwa sama ba, duk da haka ya ce, “‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana,
For David has not ascended into the heavens; but he himself says, The Lord said to my Lord, Sit at my right hand,
35 sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.”’
till I make thy enemies thy footstool.
36 “Saboda haka bari dukan Isra’ila su tabbatar da wannan. Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.”
Therefore, let all the house of Israel know assuredly, that God has made this same Jesus whom you crucified, both Lord and Christ.
37 Sa’ad da mutane suka ji wannan, sai suka soku a zuci sai suka ce wa Bitrus da sauran manzanni, “’Yan’uwa, me za mu yi?”
When they heard this, they were pierced to the heart, and said to Peter and the other apostles: Brethren, what shall we do?
38 Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki.
And Peter said to them: Repent, and be immersed, every one of you, in the name of Jesus Christ, in order to the remission of sins; and you shall receive the gift of the Holy Spirit.
39 Alkawarin dominku ne da’ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.”
For the promise is to you, and your children, and to all that are afar off, as many as the Lord our God shall call.
40 Da waɗansu kalmomi masu yawa ya gargaɗe su; ya kuma roƙe su cewa, “Ku ceci kanku daga wannan lalataccen zamani.”
And with many other words did he testify and exhort, saying: Save yourselves from this wicked generation.
41 Waɗanda suka yarda da saƙonsa kuwa aka yi musu baftisma, a ranar kuwa yawansu ya ƙaru da mutum kusan dubu uku.
Then they that gladly received his word were immersed, and on that day there were added to them about three thousand souls.
42 Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a.
And they attended constantly to the teaching of the apostles, and the fellowship, and the breaking of bread, and the prayers.
43 Kowa ya cika da tsoro, manzannin kuwa suka aikata abubuwan banmamaki da alamu masu yawa.
And fear came on every soul; and many wonders and signs were done by the apostles.
44 Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare.
And all that believed were together, and had all things in common;
45 Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa.
and they sold their possessions and goods, and distributed them to all, as each had need.
46 Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya,
And with one consent, they continued daily in the temple; and, breaking bread from house to house, they partook of their food with gladness and simplicity of heart,
47 suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.
praising God, and being in favor with all the people. And the Lord added the saved daily to the Church.

< Ayyukan Manzanni 2 >