< Ayyukan Manzanni 18 >

1 Bayan haka, Bulus ya bar Atens ya tafi Korint.
随后保罗离开雅典,来到哥林多,
2 A can ya sadu da wani mutumin Yahuda mai suna Akwila, ɗan garin Fontus, wanda ya je can ba da daɗewa ba daga Italiya tare da matarsa Firiskila, gama Kalaudiyus ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya tafi yă gan su,
在这里遇到一位老家在本都的犹太人亚居拉。由于革老丢命令所有犹太人离开罗马,所以他最近和妻子百基拉从意大利来到这里,于是保罗去见他们。
3 da yake shi ma mai ɗinkin tenti ne kamar su, sai ya zauna ya yi aiki tare da su.
由于他们和保罗一样都是以做帐棚为生,于是保罗在他们家住了下来。
4 Kowace Asabbaci kuwa yakan yi muhawwara a majami’a, yana ƙoƙari yă rinjayi Yahudawa da Hellenawa.
每逢安息日,保罗都会到会堂进行辩论,劝导犹太人和希腊人。
5 Sa’ad da Sila da Timoti suka iso daga Makidoniya, sai Bulus ya ba da kansa ga yin wa’azi kaɗai, yana tabbatar wa Yahudawa cewa Yesu shi ne Kiristi.
西拉和提摩太从马其顿赶到这里与保罗会和,保罗就可以专心传扬主的道,向犹太人证明耶稣就是基督。
6 Amma sa’ad da Yahudawa suka yi hamayya da Bulus suka kuma shiga zaginsa, sai ya karkaɗe tufafinsa a cikin rashin yarda, ya ce musu, “Alhakinku yana a kanku! Ba ni da wani laifi. Daga yanzu zan tafi wajen Al’ummai.”
当犹太人反对他、诅咒他时,他就会抖动衣服,对他们说:“你们的罪由你们自己承担,与我无关。从现在起,我要到异教徒那里去了。”
7 Sai Bulus ya bar majami’ar ya kuma tafi ƙofar da take kusa da gidan Titus Yustus, mai yi wa Allah sujada.
于是他离开那里,住到了敬拜上帝的提多·犹士都的家中,就在会堂的隔壁。
8 Kirisbus, shugaban majami’a, da dukan iyalinsa suka gaskata Ubangiji; Korintiyawa masu yawa kuwa da suka ji shi suka gaskata, aka kuwa yi musu baftisma.
会堂主管基利司布和全家人信了主,很多哥林多人也在听了道之后信了主,接受了施洗。
9 Wata rana da dad dare, Ubangiji ya yi magana da Bulus a cikin wahayi ya ce, “Kada ka ji tsoro; ka ci gaba da yin magana, kada ka yi shiru.
夜里,主通过异象对保罗说:“不要怕,大胆宣讲,不要保持沉默!
10 Gama ina tare da kai, ba kuma wanda zai fāɗa maka ya cuce ka, domin ina da mutane da yawa a wannan birni.”
因为我与你同在,没有人会攻击你,因为在这座城里有许多人都追随我。”
11 Saboda haka Bulus ya zauna a nan har shekara ɗaya da rabi, yana koya musu maganar Allah.
保罗在那里住了一年零六个月,想向众人传授上帝之道。
12 Yayinda Galliyo yake muƙaddas Akayya, Yahudawa suka haɗa kai suka tasar wa Bulus, suka kuwa kawo shi cikin kotu.
但在迦流担任亚该亚省长期间,犹太人一致起来攻击保罗,将他带到了法院,
13 Suka yi zarge cewa, “Wannan mutum yana rarrashin mutane su yi wa Allah sujada a hanyoyin da suka saɓa wa doka.”
说:“此人劝大家以违反律法的方式敬拜上帝。”
14 A daidai sa’ad da Bulus yana shirin yin magana, sai Galliyo ya ce wa Yahudawan, “Da a ce ku Yahudawa kuna gunaguni game da munafunci, ko kuma wani babban laifi, da sai in iya sauraronku.
保罗刚要开口为自己辩护,迦流就对犹太人说:“如果你们犹太人想要指控犯法或严重违法行为,我一定会听你们的讲述。
15 Amma da yake ya shafi gardama ce game da kalmomi da sunaye da kuma dokarku, sai ku ji da ita da kanku. Ni ba zan zama mai shari’a kan irin waɗannan abubuwa ba.”
但你们争论的只是文字、名字和你们的律法,那你们应当自己处理。我不会审判此类案子。”
16 Saboda haka ya kore su.
说罢,迦流就把他们从法院赶了出去。
17 Sai duk suka juya kan Sostenes shugaban majami’a suka yi masa dūka a gaban kotun. Amma Galliyo ko yă kula.
随后众人转向攻击会堂主管苏提尼,在法院门外殴打他,但迦流对此完全不予理会。
18 Bulus kuwa ya ci gaba da zama a Korint na’yan kwanaki. Sa’an nan ya bar’yan’uwa ya shiga jirgin ruwa zuwa Suriya tare da Firiskila da Akwila. Kafin ya tashi, ya aske kansa a Kenkireya saboda alkawarin da ya yi.
保罗在这里住了一段时间后,便辞别了信徒,乘船去叙利亚,百基拉和亚居拉与他同行。因为他之前许下承诺,他就在坚革里剃光了头发。
19 Suka isa Afisa, inda Bulus ya bar Firiskila da Akwila. Shi kansa ya shiga majami’a ya kuma yi muhawwara da Yahudawa.
一行人抵达以弗所后,保罗离开众人自己去了会堂,在那里跟犹太人辩论。
20 Sa’ad da suka roƙe shi ya ƙara’yan kwanaki da su, bai yarda ba.
众人请他多住一段时间,但被他拒绝了。
21 Amma da yake barin wurin, ya yi alkawari cewa, “Zan dawo in Allah ya yarda.” Sa’an nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.
他辞别众人,在以弗所乘船离开。临行前他告诉众人:“如果上帝允许,我还会回来。”
22 Sa’ad da ya sauka a Kaisariya, sai ya haura ya gai da ikkilisiya sa’an nan ya gangara zuwa Antiyok.
他在该撒利亚下船,与教会成员见了一面,然后启程去往安提阿。
23 Bayan ya yi’yan kwanaki a Antiyok, Bulus ya tashi daga can ya zaga ko’ina a yankin Galatiya da Firjiya, yana ƙarfafa dukan almajirai.
他在那里住了一段时间后,继续走遍加拉太地区和弗吕加的各个城镇,为众信徒带去鼓舞激励。
24 Ana cikin haka sai wani mutumin Yahuda mai suna Afollos, ɗan ƙasar Alekzandariya, ya zo Afisa. Shi masani ne, yana da cikakken sani na Nassosi.
与此同时,一位名叫亚波罗的犹太人来到以弗所。他老家在亚历山太,颇有口才,非常了解圣经。
25 An horar da shi a hanyar Ubangiji, ya kuma himma ƙwarai a magana, ya kuma yi koyarwa game da Yesu, daidai, ko da yake baftismar Yohanna ce kaɗai ya sani.
他曾接受主之道的教诲,内心充满热情,无论讲话还是授道,都能准确讲述耶稣,但他只知晓约翰施洗之事。
26 Sai ya fara magana gabagadi a majami’a. Sa’ad da Firiskila da Akwila suka ji shi, sai suka gayyace shi gidansu suka ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai.
他开始在会堂里公开讲道。百基拉和亚居拉听说了他,就邀请他加入,更全面地解读上帝之道。
27 Sa’ad da Afollos ya so ya tafi Akayya, sai’yan’uwa suka ƙarfafa shi suka kuma rubuta wa almajiran da suke can da su marabce shi. Da isowarsa, ya zama da taimako ƙwarai ga waɗanda ta wurin alheri suka gaskata.
后来他决定去亚该亚,信徒们就鼓励他,还给那里的使徒写信,请他们接待他。抵达亚该亚后,在当地人蒙受恩典相信上帝的过程中,他起了很大的作用,
28 Gama da ƙwazo ya ƙaryata Yahudawa a muhawwara a fili, yana tabbatar daga Nassosi cewa Yesu shi ne Kiristi.
因为他能在公开辩论种有力驳斥犹太人,通过圣经证明耶稣既是基督。

< Ayyukan Manzanni 18 >