< Ayyukan Manzanni 15 >
1 Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa’yan’uwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga al’ada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.”
In pride jih nekaj iz Judeje, in učili so brate: Če se ne obrežete po šegi Mojzesovej, ne morete zveličati se.
2 Wannan ya kai Bulus da Barnabas suka shiga babban gardama da muhawwara da su. Saboda haka aka naɗa Bulus da Barnabas tare da waɗansu masu bi, su haura zuwa Urushalima don su ga manzanni da dattawa a kan wannan magana.
Ko je torej nastal razpor, in se Pavel in Barnaba nista malo prepirala ž njimi, sklenejo, da naj odidejo Pavel in Barnaba in nekteri drugi izmed njih gor k aposteljnom in starešinam v Jeruzalem, za voljo tega vprašanja.
3 Ikkilisiya ta raka su suka tafi, yayinda suke ratsawa ta Funisiya da Samariya, suka ba da labari yadda Al’ummai suka tuba. Wannan labarin ya sa dukan’yan’uwa suka yi murna ƙwarai.
Oni torej spremljeni od cerkve, šli so skozi Fenicijo in Samarijo, pripovedovaje izpreobrnenje poganov; in delali so veliko radost vsem bratom.
4 Sa’ad da suka isa Urushalima, sai ikkilisiya da manzanni da kuma dattawa suka marabce su, sai suka ba su rahoton dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu.
Ko so pa prišli v Jeruzalem, sprejela jih je cerkev in aposteljni in starešine, in sporočili so, koliko rečî je Bog ž njima storil.
5 Sai waɗansu daga cikin masu bin da suke na ƙungiyar Farisiyawa suka miƙe tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa Al’ummai kaciya a kuma bukace su su yi biyayya da dokokin Musa.”
Ali vstalo jih je nekaj od ločinke Farizejske, kteri so bili verovali, in govorili so: Obrezovati se morajo, in naročiti se mora, naj postavo Mojzesovo izpolnjujejo.
6 Sai manzanni da dattawa suka taru don su duba maganar.
In aposteljni in starešine se zberó, da to reč presodijo.
7 Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi ya ce, “’Yan’uwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Al’ummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata.
Ko so se pa veliko prepirali, vstane Peter in jim reče: Možjé bratje! vi véste, da je od prvih dnî Bog izmed nas izbral, da so iz mojih ust slišali pogani besedo evangelja, in so verovali.
8 Allah, wanda ya san zuciya, ya nuna cewa ya karɓe su ta wurin ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.
In Bog, kteri pozná srca, popričal jim je, davši jim Duha svetega, kakor tudi nam.
9 Bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsarkake zukatansu ta wurin bangaskiya.
In nobenega razločka ni postavil med nami in njimi, ko je po veri očistil njih srca.
10 To, fa, don me kuke ƙoƙari ku gwada Allah ta wurin ɗora wa almajiran nan kayan da mu ko kakanninmu ba mu iya ɗauka ba?
Sedaj torej, kaj izkušate Boga, da nakladate učencem jarem na vrat, kterega ne očetje naši, ne mi nismo mogli ponesti?
11 A’a! Mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”
Nego po milosti Gospoda Jezusa Kristusa verujemo, da se bomo zveličali, kakor tudi oni.
12 Sai duk taron suka yi tsit yayinda suke sauraron Barnabas da Bulus suna ba da labari game da ayyuka da kuma abubuwan banmamakin da Allah ya yi a cikin Al’ummai ta wurinsu.
Tedaj je vsa množica umolknila, in poslušali so Barnaba in Pavla, ktera sta pripovedovala, kolika znamenja in čudeže je Bog storil po njima med pogani.
13 Da suka gama, sai Yaƙub ya yi magana ya ce, “’Yan’uwa, ku saurare ni.
Ko sta umolknila, odgovorí Jakob, govoreč: Možjé bratje, čujte me!
14 Siman ya bayyana mana yadda Allah da farko ya nuna damuwarsa ta wurin ɗaukan mutane daga cikin Al’ummai su zama nasa.
Simon je povedal, kako je Bog najprej obiskal pogane, da bi prejel iž njih ljudstvo imenu svojemu;
15 Kalmomin annabawa sun yi daidai da wannan, kamar yadda yake a rubuce cewa,
In s tem se vjemajo besede prerokov, kakor je pisano:
16 “‘Bayan wannan zan koma in kuma sāke gina tentin Dawuda da ya rushe. Kufansa zan sāke gina, in kuma mai da shi,
"Po tem se bom vrnil, in sezidal bom zopet dom Davidov, ki je padel; in razvalino njegovo bom zopet sezidal, in povzdignil ga bom:
17 don ragowar mutane su nemi Ubangiji, kuma duk Al’umman da suke kira bisa sunana, in ji Ubangiji, wanda yake yin waɗannan abubuwa’
Da ljudjé, kteri ostanejo, poiščejo Gospoda, in vsi narodi, na ktere se je ime moje poklicalo: pravi Gospod, kteri vse to dela."
18 da aka sani tun zamanai. (aiōn )
Bogu so od vekomaj znana vsa dela njegova. (aiōn )
19 “Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa Al’ummai waɗanda suke juyowa ga Allah.
Za to jaz sodim, naj se ne nadlegujejo, kteri se od poganov obračajo k Bogu.
20 A maimakon haka, ya kamata mu rubuta musu cewa, su guji abincin da alloli suka ƙazantar, da fasikanci, da naman dabbar da aka murɗe da kuma jini.
Nego piše naj jim se, da naj se zdržujejo ognjušenja od malikov in kurbarije in udavljenega in krvi:
21 Gama Musa ya yi wa’azi a kowace birni tun zamanin dā, ana kuma karanta shi a majami’u kowane Asabbaci.”
Kajti Mojzes jih od starodavnih časov po vseh mestih ima, kteri ga oznanjujejo, ko se po shajališčih vsako soboto bere.
22 Sai manzanni da dattawa, tare da dukan ikkilisiya, suka yanke shawara su zaɓi waɗansu daga cikin mutanensu su kuma aike su zuwa Antiyok tare da Bulus da Barnabas. Sai suka zaɓi Yahuda (wanda ake kira Barsabbas) da kuma Sila, mutum biyu da suke shugabanni cikin’yan’uwa.
Tedaj so aposteljni in starešine z vso cerkvijo sklenili izvoliti možé izmed sebe, in poslali v Antijohijo s Pavlom in Barnabom: Juda s priimkom Barsaba, in Sila, znamenita moža med brati.
23 Tare da su suka aika da wannan wasiƙa. Daga manzanni da dattawa,’yan’uwanku. Zuwa ga Al’ummai masu bi a Antiyok, Suriya da Silisiya. Gaisuwa.
In pisali so po njunih rokah to: Aposteljni in starešine in bratje pozdravljajo brate izmed poganov, kteri so po Antijohiji in Siriji in Ciliciji.
24 Mun ji cewa, waɗansu da sun fita daga cikinmu ba tare da izininmu ba suka kuma dame ku, suna tā da hankalinku ta wurin abin da suka ce.
Ker smo slišali, da so nekteri izmed nas izšli, in so vas zbegali z besedami, in zmotili duše vaše, govoreč, da se obrezujte in izpolnjujte postavo, kterim nismo zapovedali;
25 Saboda haka dukanmu mun yarda mu zaɓi waɗansu mutane mu kuma aike su wurinku tare da ƙaunatattun abokanmu Barnabas da Bulus
Sklenili smo ene misli zbrani izvoliti možé in poslati k vam, z ljubljenima našima Barnabom in Pavlom,
26 mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi.
Človekoma, ktera sta dala duši svoji za ime Gospoda našega Jezusa Kristusa.
27 Saboda haka muna aika Yahuda da Sila don su tabbatar muku da baki abin da muka rubuta.
Poslali smo torej Juda in Sila, ktera bosta tudi sama z besedo povedala ravno to.
28 Ya gamshe Ruhu Mai Tsarki da mu ma kada a ɗora muku nauyi fiye da na waɗannan abubuwa.
Dopadlo je namreč svetemu Duhu in nam, nobenega bremena več ne nakladati vam, razen teh potrebnih rečî:
29 Ku guji abincin da aka yi wa alloli hadaya, da jini, da naman dabbar da aka murɗe da kuma fasikanci. Za ku kyauta in kun kiyaye waɗannan abubuwa. Ku huta lafiya.
Da se zdržujte malikom darovanega in krví in udavljenega in kurbarije. Če se boste tega varovali, boste prav delali. Zdravi!
30 Aka sallami mutanen sai suka gangara zuwa Antiyok, inda suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da wasiƙar.
In ko so jih bili odpravili, prišli so v Antijohijo; in zbravši množico, izročili so pismo.
31 Mutanen suka karantata suka kuma yi farin ciki saboda saƙonta mai ƙarfafawa.
Ko so pa prebrali, razveselili so se tolažbe.
32 Yahuda da Sila, waɗanda su kansu annabawa ne, suka yi magana sosai don su gina su kuma ƙarfafa’yan’uwa.
A Juda in Sila, ktera sta bila tudi preroka, utolažila sta z mnogimi besedami brate, in utrdila.
33 Bayan suka yi’yan kwanaki a can, sai’yan’uwa suka sallame su da albarkar salama su dawo wurin waɗanda suka aike su.
In ko sta tu nekaj časa prebila, odpustili so ju bratje v miru k aposteljnom.
Sklenil je pa Sila tam ostati.
35 Amma Bulus da Barnabas kuwa suka dakata a Antiyok, inda su da waɗansu da yawa suka yi koyarwa suka kuma yi wa’azin maganar Ubangiji.
A Pavel in Barnaba sta živela v Antijohiji, in učila sta in oznanjevala, tudi z mnogimi drugimi, besedo Gospodovo.
36 Bayan’yan kwanaki sai Bulus ya ce wa Barnabas, “Mu koma mu ziyarci’yan’uwa a duk garuruwan da muka yi wa’azin bisharar Ubangiji mu ga yadda suke.”
A črez nekoliko dnî reče Pavel Barnabu: Vrniva se in obiščiva brate svoje po vseh mestih, v kterih sva oznanila besedo Gospodovo, kako se imajo.
37 Barnabas ya so Yohanna, wanda ake kira Markus ya tafi tare da su,
Barnaba je pa hotel, da bi vzela s seboj Janeza, ki se je imenoval Marka.
38 amma Bulus bai ga ya kyautu ya tafi da shi ba, domin ya yashe su a Famfiliya bai kuwa ci gaba tare da su a aikin ba.
Ali Pavlu se je za dobro zdelo, da tega, ki se je ločil od nju iz Pamfilije, in ni šel ž njima na delo, ne bi jemala s seboj.
39 Suka sami saɓanin ra’ayi tsakaninsu har suka rabu. Barnabas ya ɗauki Markus suka shiga jirgin ruwa zuwa Saifurus,
Za to vstane razpor, tako, da sta se ločila eden od drugega, in je Barnaba vzel Marka, in se je odpeljal po morji na Ciper;
40 amma Bulus ya zaɓi Sila suka kuwa tashi, bayan’yan’uwa suka danƙa su ga alherin Ubangiji.
A Pavel izbere Sila, in izide, priporočen milosti Božjej od bratov.
41 Ya ratsa ta Suriya da Silisiya, yana ƙarfafa ikkilisiyoyi.
In hodil je po Siriji in Ciliciji, in utrjeval je cerkve.