< Ayyukan Manzanni 14 >
1 A Ikoniyum Bulus da Barnabas suka shiga majami’ar Yahudawa yadda suka saba. A can suka yi magana gabagadi har Yahudawa da Al’ummai masu yawa suka gaskata.
And it came to pass in Iconium, that they went together into the synagogue of the Jews, and so spoke that a great multitude of the Jews and Greeks believed.
2 Amma Yahudawan da suka ƙi ba da gaskata, suka zuga Al’ummai suka sa ɓata tsakaninsu da’yan’uwa.
But the unbelieving Jews excited and embittered the minds of the Gentiles against the brethren.
3 Bulus da Barnabas kuwa suka daɗe sosai a can, suna magana gabagadi saboda Ubangiji, wanda kuwa ya tabbatar da saƙon alherinsa ta wurinsa su su aikata ayyuka da alamu masu banmamaki.
Therefore, they continued a long time, and spoke boldly in the Lord, who gave testimony to the word of his grace, by granting signs and wonders to be done by their hands.
4 Mutanen birnin suka rarrabu, waɗansu suka goyi bayan Yahudawa, waɗansu kuma suka goyi bayan manzannin.
But the multitude of the city were divided; and some were with the Jews, and some with the apostles.
5 Yahudawa da Al’ummai tare da shugabanninsu suka ƙulla shawara a tsakaninsu, domin su wulaƙanta su su kuma jajjefe su da duwatsu.
But when there was a violent purpose on the part of the Gentiles and of the Jews, with their rulers, to outrage and to stone them,
6 Amma suka sami labari suka kuma gudu zuwa biranen Ikoniyum na Listira da Derbe da kuma ƙauyukan kewaye,
being aware of it, they fled to the cities of Lycaonia, Lystra, and Derbe, and to the region round about,
7 inda suka ci gaba da wa’azin labari mai daɗi.
and there they preached the gospel.
8 A Listira kuwa akwai wani gurgu zaune a ƙafafunsa, wanda gurgu ne tun haihuwa, kuma bai taɓa tafiya ba.
And there was a certain man in Lystra, without strength in his feet, who sat, for he was a cripple from his mother’s womb, and had never walked.
9 Ya kasa kunne yayinda Bulus yake magana. Bulus kuma ya kafa masa ido, ya lura cewa yana da bangaskiyar da za tă warkar da shi
This man heard Paul speak, who, looking earnestly on him, and seeing that he had faith to be saved,
10 sai ya ɗaga murya ya ce, “Tashi ka tsaya kan ƙafafunka!” Da jin haka, sai mutumin ya yi wuf ya kuma fara tafiya.
said, with a loud voice: Stand erect upon your feet. And he leaped and walked.
11 Sa’ad da taron suka ga abin da Bulus ya yi, sai suka ihu da harshen Likayoniyawa, suna cewa, “Alloli sun sauka mana da siffar mutane!”
When the multitude saw what Paul had done, they lifted up their voice, and said, in the Lycaonian language: The Gods have come down to us in the likeness of men.
12 Sai suka ba wa Barnabas, sunan Zeyus, Bulus kuma suka kira Hermes domin shi ne shugaban magana.
And they called Barnabas, Jupiter, and Paul, Mercury, for he was the chief speaker.
13 Firist na Zeyus, wanda haikalinsa ke bayan birni, ya kawo bijimai da furanni a ƙofofin birni domin shi da taron mutanen sun so su miƙa musu hadayu.
Then the priest of Jupiter, whose temple was before the city, having brought bulls and garlands to the entrance, intended to offer sacrifice, with the multitudes.
14 Amma da manzannin nan Barnabas da Bulus suka ji haka, sai suka yayyage tufafinsu suka ruga cikin taron, suna ihu suna cewa,
But when the apostles, Barnabas and Paul, heard of it, they rent their clothes, and ran in among the multitude, crying out,
15 “Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai,’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu.
and saying: Men, why are you doing these things? We also are human beings, with passions like your own, and we preach the gospel to you, that you may turn from these vanities to the living God, who made the heaven, and the earth, and the sea, and all things that are in them;
16 A zamanin dā, ya bar dukan ƙasashe su yi yadda suka ga dama.
who, in past generations, permitted all the nations to walk in their own ways;
17 Duk da haka bai bar kansa babu shaida ba. Ya nuna alheri ta wurin ba ku ruwan sama da kuma amfanin gona a lokutansu; ya ba ku abinci mai yawa ya kuma cika zukatanku da farin ciki.”
and yet he did not leave himself without testimony, doing good, and giving you rain from heaven, and fruitful seasons, filling your hearts with food and gladness.
18 Ko da waɗannan kalmomi ma, da ƙyar suka hana jama’an nan yin musu hadaya.
And with these words they hardly restrained the multitudes from offering sacrifice to them.
19 Sai waɗansu Yahudawa suka zo daga Antiyok da Ikoniyum suka sha kan taron. Suka jajjefi Bulus da duwatsu suka kuma ja shi bayan birni, suna tsammani ya mutu.
Then came thither, from Antioch and Iconium, Jews, who persuaded the multitudes; and having stoned Paul, they dragged him out of the city, supposing that he was dead.
20 Amma bayan da almajiran suka taru kewaye da shi, sai ya tashi ya koma cikin birni. Kashegari shi da Barnabas suka tashi zuwa Derbe.
But while the disciples were standing around him, he arose, and went into the city. And on the next day, he departed with Barnabas to Derbe;
21 Suka yi wa’azin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok,
and when they had preached the gospel to that city, and had made many disciples, they returned to Lystra, and to Iconium, and to Antioch,
22 suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.”
strengthening the souls of the disciples, exhorting them to continue in the faith, and saying, that through many afflictions we mast enter the kingdom of God.
23 Bulus da Barnabas suka naɗa musu dattawa a kowace ikkilisiya, tare da addu’a da azumi, suka miƙa su ga Ubangiji, wanda suka dogara da shi.
And when they had appointed elders for them in every church, with prayer and fasting, they commended them to the Lord, on whom they believed.
24 Bayan sun bi ta Fisidiya, sai suka zo cikin Famfiliya,
And having passed through Pisidia, they came into Pamphylia;
25 kuma sa’ad da suka yi wa’azi a Ferga, sai suka gangara zuwa Attaliya.
and when they had preached the word in Perga, they went down to Attalia:
26 Daga Attaliya kuma suka shiga jirgin ruwa suka koma Antiyok, inda dā aka danƙa su ga alherin Allah saboda aikin da suka kammala yanzu.
thence they sailed to Antioch, from which place they had been commended to the grace of God, for the work which they had accomplished.
27 Da isarsu a can, sai suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da rahoton duk abin da Allah ya aikata ta wurinsu da kuma yadda ya buɗe ƙofar bangaskiya domin Al’ummai.
And having come and called together the church, they reported all that God had done with them, and that he had opened the door of faith to the Gentiles.
28 Suka kuma jima a can tare da almajirai.
And they continued a long time with the disciples.