< Ayyukan Manzanni 12 >

1 Kusan a wannan lokaci ne Sarki Hiridus ya kama waɗansu da suke na ikkilisiya, da niyya ya tsananta musu.
当时君王希律开始迫害教会成员。
2 Ya sa aka kashe Yaƙub, ɗan’uwan Yohanna, da takobi.
他用剑处决了约翰的哥哥雅各,
3 Sa’ad da ya ga wannan ya faranta wa Yahudawa rai, sai ya kama Bitrus shi ma. Wannan ya faru kwanakin Bikin Burodi Marar Yisti.
由于此举受到了犹太人的支持,于是他又在除酵节期间捉拿彼得。
4 Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shari’a a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa.
他们逮捕了彼得后将其投入监牢,由四班士兵看守,每班四个人。君王希律打算逾越节过后,就对他进行公审。
5 Saboda haka aka tsare Bitrus a kurkuku, amma ikkilisiya ta nace da addu’a ga Allah dominsa.
彼得在监牢期间,教会开始为他虔诚地祈求上帝。
6 A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shari’a, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, daure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa.
就在希律打算将他公审的前一夜,彼得被安排睡在两名士兵中间,手腕上的两条锁链分别与两人栓在一起,还有卫兵守在门前。
7 Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa.
忽然,一名天使出现,光芒照亮了牢房。天使将彼得唤醒,说:“快点!起来吧!”于是彼得手上的锁链就脱落了。
8 Sa’an nan mala’ikan ya ce masa, “Ka sa rigunarka da takalmanka.” Bitrus kuwa ya sa. Mala’ikan ya faɗa masa cewa, “Ka yafa mayafinka ka bi ni.”
天使对他说:“穿上衣服和鞋!”彼得照做了。天使又对他说:“披上外衣,跟我走!”
9 Bitrus ya bi shi suka fita kurkukun, amma bai ma san cewa abin da mala’ikan yake yi tabbatacce ne ba; yana tsammani wahayi yake gani.
于是彼得就跟着天使走出去,但他只是以为看到了异象,没有意识到天使所做的一切都在真实发生。
10 Suka wuce masu gadi na fari da na biyu, suka kuma isa ƙofar ƙarfe ta shiga birni. Ƙofar kuwa ta buɗe musu da kanta, suka kuma wuce. Sa’ad da suka yi tafiya tsawon wani titi, nan take mala’ikan ya bar shi.
他们经过第一队和第二队守卫,来到通往城内的铁门,门便自动给他们打开。他们出来后沿着街道行走,天使忽然就离开了。
11 Sai Bitrus ya dawo hankalinsa ya ce, “Yanzu na sani ba shakka Ubangiji ne ya aiki mala’ikansa yă cece ni daga hannun Hiridus da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”
彼得这时候才明白,说:“现在我知道怎么回事了!主派天使将我从希律的权势中拯救出来,让我躲过犹太人的阴谋。”
12 Da ya gane haka, sai ya tafi gidan Maryamu uwar Yohanna, wanda ake kuma kira Markus, inda mutane da yawa suka taru suna addu’a.
明白这一切,他就到约翰(又名马可)的母亲玛利亚家中,很多信徒聚在那里祷告。
13 Bitrus ya ƙwanƙwasa ƙofar waje, sai wata mai aiki a gidan da ake kira Roda ta zo tă ji ko wane ne.
彼得敲了敲大门,一位名叫罗大的侍女出来准备开门。
14 Da ta gane muryar Bitrus, ta cika da murna ta gudu ta koma ba tare da ta buɗe ƙofar ba, sai ta koma a guje ta ce da ƙarfi, “Ga Bitrus a bakin ƙofa!”
但认出是彼得的声音后,她兴奋的顾不上开门就跑进屋,大声喊:“彼得就在门外!。”
15 Sai suka ce mata, “Kina hauka.” Da ta nace cewa shi ne, sai suka ce, “To, lalle, mala’ikansa ne.”
大家说:“你疯了!”她却坚持地说这是真的。他们说:“那一定是他的天使!”
16 Amma Bitrus ya yi ta ƙwanƙwasawa. Da suka buɗe ƙofar suka kuma gan shi, sai suka yi mamaki.
彼得继续敲门,他们最终打开了门,一见是他,非常惊讶。
17 Bitrus ya yi musu alama da hannunsa su yi shiru sai ya bayyana yadda Ubangiji ya fitar da shi daga kurkuku. Ya ce, “Ku gaya wa Yaƙub da kuma’yan’uwa game da wannan,” sa’an nan ya tashi ya tafi wani wuri.
彼得向他们举起手示意安静,然后对他们解释主如何带他走出监牢。他又说:“把这事告诉雅各和众兄弟。”然后就离开去往别处了。
18 Da safe, hargitsin da ya tashi tsakanin sojojin ba ƙarami ba ne, a kan abin da ya sami Bitrus.
天亮的时候,士兵们惊慌不已,不知彼得去了哪里。
19 Bayan Hiridus ya neme shi bai same shi ba, sai ya tuhumi masu gadin, ya kuma ba da umarni a kashe su. Sa’an nan Hiridus ya tashi daga Yahudiya ya tafi Kaisariya ya kuma yi’yan kwanaki a can.
希律开始四处搜索他,但始终没有找到。于是就审问卫兵,然后下令把他们处死。随后希律便离开犹太去往该撒利亚,在那里住下。
20 Yana da rashin jituwa da mutanen Taya da na Sidon; sai suka haɗa kai suka nemi ganawa da shi. Bayan suka sami goyon bayan Bilastus, amintaccen bawan sarki, sai suka nemi salama, domin sun dogara ga ƙasar sarkin don samun abincinsu.
此刻的希律对推罗和西顿人充满了愤怒。这两个地方的人派了一个联合代表团来见他,设法拉拢了国王的个人助理伯拉斯。这个代表团希望向希律求和,因为这两地在粮食供应商都依赖希律的国家。
21 A ranar da aka shirya Hiridus, sanye da kayan sarautarsa, ya zauna a gadon sarautarsa ya kuma ya wa mutanen jawabi.
到了约定见面的日期,希律穿上国王的长袍,坐在王座上,向众人讲话。
22 Suka tā da murya suka ce, “Wannan muryar wani allah ne, ba ta mutum ba.”
人群中有人大声说:“这是上帝的声音,不是人的声音!”
23 Nan take, domin Hiridus bai yi wa Allah yabo ba, wani mala’ikan Ubangiji ya buge shi, tsutsotsi kuwa suka cinye shi ya kuma mutu.
但由于他没有将荣耀归于上帝,主的使者将他击倒。 他被虫吃掉了,死了。
24 Amma maganar Allah ta ci gaba da ƙaruwa ta kuma bazu.
但上帝之道却开始传播,信徒的数量越来越多。
25 Sa’ad da Barnabas da Shawulu suka kammala aikinsu, sai suka komo daga Urushalima, tare da Yohanna, wanda ake kira Markus.
巴拿巴和扫罗完成了送捐款的任务,就带着约翰(马克)从耶路撒冷返回。

< Ayyukan Manzanni 12 >