< Ayyukan Manzanni 11 >
1 Manzanni da’yan’uwa ko’ina a Yahudiya suka ji cewa Al’ummai ma sun karɓi maganar Allah.
Now the apostles and the brothers who were in Judea heard that the non-Jewish people had also received the word of God.
2 Saboda haka sa’ad da Bitrus ya haura zuwa Urushalima, masu bin da suke da kaciya suka zarge shi
When Peter had come up to Jerusalem, those who were of the circumcision contended with him,
3 suka ce, “Ka je gidan mutanen da suke marasa kaciya ka kuwa ci tare da su.”
saying, "You went in to uncircumcised men, and ate with them."
4 Bitrus ya fara yin musu bayani dalla-dalla yadda ya faru cewa,
But Peter began, and explained to them in order, saying,
5 “Ina a birnin Yoffa ina addu’a, sai ga wahayi ya zo mini. Na ga ana sauko da wani abu kamar babban mayafi daga sama ta kusurwansa huɗu, ya kuma sauko inda nake.
"I was in the city of Joppa praying, and in a trance I saw a vision: a certain container descending, like it was a great sheet let down from heaven by four corners. It came as far as me.
6 Na duba cikinsa na ga dabbobi masu ƙafa huɗu na duniya, da namun jeji, da masu ja da ciki, da kuma tsuntsayen sararin sama.
When I had looked intently at it, I considered, and saw the four-footed animals of the earth, wild animals, crawling creatures, and birds of the sky.
7 Sa’an nan na ji wata murya tana ce mini, ‘Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.’
I also heard a voice saying to me, 'Rise, Peter, kill and eat.'
8 “Na amsa na ce, ‘Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.’
But I said, 'Not so, Lord, for nothing unholy or unclean has ever entered into my mouth.'
9 “Sai muryar daga sama ta yi magana sau na biyu, ta ce, ‘Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.’
But a voice answered the second time out of heaven, 'What God has cleansed, do not call unclean.'
10 Wannan ya faru har sau uku, sa’an nan duk aka sāke ɗauke shi zuwa sama.
This was done three times, and all were drawn up again into heaven.
11 “Nan take sai ga mutum uku da aka aika wurina daga Kaisariya a tsaye a ƙofar gidan da nake.
And look, immediately three men stood before the house where we were, having been sent from Caesarea to me.
12 Ruhu ya ce mini kada in yi wata-wata game da tafiya tare da su. Waɗannan’yan’uwa guda shida su ma suka rako ni, muka kuwa shiga gidan mutumin.
The Spirit told me to go with them, without discriminating. These six brothers also accompanied me, and we entered into the man's house.
13 Ya kuma gaya mana yadda wani mala’ika ya bayyana a gidansa ya ce masa, ‘Ka aika zuwa Yoffa a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus.
He told us how he had seen the angel standing in his house, and saying to him, 'Send to Joppa, and get Simon, whose surname is Peter,
14 Zai kawo maka saƙo wanda ta wurinsa kai da dukan iyalinka za ku sami ceto.’
who will speak to you words by which you will be saved, you and all your house.'
15 “Na fara magana ke nan, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu yadda ya sauko mana a farko.
As I began to speak, the Holy Spirit fell on them, even as on us at the beginning.
16 Sa’an nan na tuna da abin da Ubangiji ya ce, ‘Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma za a yi muku baftisma daRuhu Mai Tsarki.’
I remembered the word of the Lord, how he said, 'John indeed baptized in water, but you will be baptized in the Holy Spirit.'
17 To, in Allah ya ba su kyauta yadda ya ba mu, mu da muka gaskata da Ubangiji Yesu Kiristi, wane ni da zan yi hamayya da Allah?”
If then God gave to them the same gift as us, when we believed in the Lord Jesus Christ, who was I, that I could withstand God?"
18 Sa’ad da suka ji haka, ba su ƙara yin faɗa ba, suka kuma ɗaukaka Allah, suna cewa, “To, fa, har Al’ummai ma Allah ya sa suka tuba zuwa rai.”
When they heard these things, they held their peace, and glorified God, saying, "Then God has also granted to the non-Jews repentance to life."
19 To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin da ya tashi a kan batun Istifanus suka tafi har Funisiya, Saifurus da kuma Antiyok, suna ba da saƙon ga Yahudawa kaɗai.
They therefore who were scattered abroad by the oppression that arose about Stephen traveled as far as Phoenicia, Cyprus, and Antioch, speaking the word to no one except to Jews only.
20 Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Hellenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu.
But there were some of them, men of Cyprus and Cyrene, who, when they had come to Antioch, spoke to the Greeks, proclaiming the good news of the Lord Jesus.
21 Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji.
The hand of the Lord was with them, and a great number believed and turned to the Lord.
22 Labari wannan abu ya kai kunnuwan ikkilisiya a Urushalima, sai suka aiki Barnabas zuwa Antiyok.
And the report concerning them was heard by the church in Jerusalem, so they sent Barnabas to Antioch,
23 Da ya iso ya kuma ga tabbacin alherin Allah, sai ya yi farin ciki ya kuma ƙarfafa su duka su tsaya da gaskiya cikin Ubangiji da dukan zukatansu.
who, when he had come, and had seen the grace of God, was glad. He exhorted them all, that with purpose of heart they should remain true to the Lord.
24 Mutum ne nagari, cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, mutane masu yawan gaske kuwa suka juya ga Ubangiji.
For he was a good man, and full of the Holy Spirit and of faith, and many people were added to the Lord.
25 Sa’an nan Barnabas ya tafi Tarshish don yă nemi Shawulu,
Barnabas went out to Tarsus to look for Saul.
26 sa’ad da ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antiyok. Ta haka shekara guda cur Barnabas da Shawulu suka yi suna taruwa da ikkilisiya, suka kuma koya wa mutane masu yawan gaske. A Antiyok ne aka fara kiran almajirai da suna Kirista.
When he had found him, he brought him to Antioch. It happened, that for a whole year they were gathered together with the church, and taught many people. The disciples were first called Christians in Antioch.
27 A wannan lokaci waɗansu annabawa sun zo Antiyok daga Urushalima.
Now in these days, prophets came down from Jerusalem to Antioch.
28 Ɗaya daga cikinsu mai suna Agabus, ya miƙe tsaye ya yi annabci ta wurin Ruhu cewa za a yi yunwa mai tsanani wadda za tă bazu a dukan duniyar Romawa (Wannan ya faru a zamanin mulkin Kalaudiyus.)
One of them named Agabus stood up, and indicated by the Spirit that there should be a great famine all over the world, which also happened in the days of Claudius.
29 Kowanne a cikin almajiran, gwargwadon azancinsa, ya yanke shawara ya ba da gudummawa ga’yan’uwan da suke zama a Yahudiya.
As any of the disciples had plenty, each determined to send relief to the brothers who lived in Judea;
30 Haka kuwa suka yi, suka aika da kyautarsa wa dattawan ikkilisiyar ta hannu Barnabas da Shawulu.
which they also did, sending it to the elders by the hands of Barnabas and Saul.