< Ayyukan Manzanni 1 >

1 A littafina na farko, Tiyofilus, na rubuta game da dukan abin da Yesu ya fara yi, da abin da ya koyar
Dear Theophilus, in my previous book I wrote about all that Jesus did and taught from the beginning
2 har zuwa ranar da aka ɗauke shi zuwa sama, bayan ya ba da umarnai ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa.
until the day he was taken up to heaven. This was after he'd given instructions through the Holy Spirit to his chosen apostles.
3 Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arba’in ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah.
Over the course of forty days after the death he suffered, he showed himself to them, proving that he was alive with convincing evidence. He appeared to them, and told them about the kingdom of God.
4 A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni, “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai.
While he was still with them he instructed them, “Do not leave Jerusalem. Wait to receive what the Father promised, just as you heard it from me.
5 Gama Yohanna ya yi baftisma daruwa, amma a cikin’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”
It's true that John baptized with water, but in just a few days' time you will be baptized by the Holy Spirit.”
6 Saboda haka, sa’ad da suka taru, sai suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci za ka mayar da mulki ga Isra’ila?”
So when the disciples met with Jesus, they asked him, “Lord, is this the time when you will re-establish Israel's kingdom?”
7 Ya ce musu, “Ba naku ba ne ku san lokuta ko ranakun da Uban ya shirya cikin ikonsa.
“You don't need to know about the dates and times that are set by the Father's authority,” he told them.
8 Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.”
“But you will be given power when the Holy Spirit comes upon you, and you will be my witnesses in Jerusalem, throughout Judea and Samaria, and to the farthest places on earth.”
9 Bayan ya faɗi wannan, sai aka ɗauke shi sama a idanunsu sai wani girgije ya rufe shi daga ganinsu.
After Jesus had told them this, he was taken up as they were watching and a cloud hid him from their sight.
10 Suna zuba ido a bisa, zuwa cikin sararin sama yayinda yake tafiya, nan da nan, sai ga mutane biyu saye da fararen riguna tsaye kusa da su.
While they were staring intently at the sky as he ascended, two men dressed in white were suddenly standing beside them.
11 Sai suka ce, “Mutanen Galili, don me kuke tsaye a nan kuna duban sararin sama? Wannan Yesu, wanda aka ɗauke daga gare ku zuwa sama, zai komo daidai yadda kuka ga ya tafi sama.”
“Men of Galilee, why are you standing here staring at the sky?” they asked. “This same Jesus who has been taken up from you to heaven shall come in the same way you saw him go into heaven.”
12 Sai suka koma Urushalima daga tudun da ake kira Dutsen Zaitun, tafiyar ranar Asabbaci guda daga birnin.
Then the disciples went back to Jerusalem from the Mount of Olives which is about a Sabbath day's walk from Jerusalem.
13 Da suka iso, sai suka hau gidan sama, zuwa ɗakin da suke zama. Waɗanda suka kasance kuwa su ne, Bitrus, Yohanna, Yaƙub da Andarawus; Filibus da Toma; Bartolomeyu da Mattiyu; Yaƙub ɗan Alfayus da Siman Zilot, da kuma Yahuda ɗan Yaƙub.
When they arrived, they went upstairs to the upper room where they were staying: Peter, John, James and Andrew; Philip and Thomas; Bartholomew and Matthew; James the son of Alphaeus, Simon the Zealot, and Judas the son of James.
14 Waɗannan duka suka duƙufa cikin addu’a, tare da waɗansu mata da Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma tare da’yan’uwansa.
They all joined together in prayer, together with the women and Mary, Jesus' mother, and his brothers.
15 A waɗancan kwanakin Bitrus ya miƙe tsaye cikin’yan’uwa masu bi (taron da ya yi kusan mutum ɗari da ashirin)
At this time Peter stood up and addressed a crowd of around one hundred and twenty believers who had gathered together.
16 ya ce, “’Yan’uwana, dole a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana tun da daɗewa ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya zama jagora ga waɗanda suka kama Yesu
“My brothers and sisters,” he said, “The Scriptures, spoken by the Holy Spirit through David, had to be fulfilled regarding Judas, who guided those who arrested Jesus.
17 dā shi ɗaya ne cikinmu, ya kuma yi hidima a cikin aikin nan.”
He was counted as one of us, and shared in this ministry.”
18 (Da ladar da ya samu saboda muguntarsa Yahuda ya sayi wani fili; a can ya fāɗi da kā, jikinsa ya fashe, hanjinsa kuma duk suka zubo.
(Judas had bought a field with his ill-gotten gains. There he fell down headfirst, and his body burst apart, spilling out all his intestines.
19 Kowa a Urushalima ya ji game da wannan, saboda haka suka kira wannan filin Akeldama, da yarensu, wato, Filin Jini.)
Everybody who lived in Jerusalem heard about this so that the field was called in their language “Akeldama,” which means, “Field of blood.”)
20 Bitrus ya ce, “Gama yana a rubuce a cikin Littafin Zabura cewa, “‘Bari wurinsa yă zama babu kowa; kada kowa ya zauna a cikinsa,’ kuma, “‘Bari wani ya ɗauki matsayinsa na shugabanci.’
As it's written in the book of Psalms, “Let his home be abandoned, and no-one live there;” and “Let someone else take over his position.”
21 Saboda haka dole a zaɓi ɗaya daga cikin mutanen da suke tare da mu duk lokacin da Ubangiji Yesu yake shiga da fita a cikinmu,
“So now we have to choose someone who has been with us the whole time that Jesus was with us,
22 farawa daga baftisma ta Yohanna har zuwa sa’ad da aka ɗauke Yesu daga gare mu. Gama dole ɗaya daga waɗannan ya zama shaidar tashinsa daga matattu tare da mu.”
from the time John was baptizing up until the day Jesus was taken up to heaven from us. One of these must be chosen to join together with us as we witness, giving evidence of Jesus' resurrection.”
23 Saboda haka suka gabatar da mutane biyu. Yusuf mai suna Barsabbas (da aka kuma sani da Yustus) da kuma Mattiyas.
Two names were put forward: Joseph Justus, also known as Barsabbas, and Matthias.
24 Sai suka yi addu’a suka ce, “Ubangiji, ka san zuciyar kowa. Nuna mana wanne a cikin waɗannan biyu da ka zaɓa
They prayed together and said, “Lord, you know everyone's thoughts please show us which of these two you have chosen
25 ya karɓi wannan aikin manzanci, wanda Yahuda ya bari don yă tafi wurin da yake nasa.”
to replace Judas as an apostle in this ministry that he gave up to go to where he belongs.”
26 Sa’an nan suka jefa ƙuri’u, ƙuri’ar kuwa ta fāɗo a kan Mattiyas; sai aka sa shi cikin manzannin nan goma sha ɗaya.
They cast lots, and Matthias was chosen. He was counted as an apostle with the other eleven.

< Ayyukan Manzanni 1 >