< 2 Timoti 3 >

1 Amma fa ka san wannan, za a yi lokutan shan wahala a kwanakin ƙarshe.
Τοῦτο δὲ γίνωσκε, ὅτι ἐν ἐσχάταις ἡμέραις ἐνστήσονται καιροὶ χαλεποί·
2 Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki,
ἔσονται γὰρ οἱ ἄνθρωποι φίλαυτοι, φιλάργυροι, ἀλαζόνες, ὑπερήφανοι, βλάσφημοι, γονεῦσιν ἀπειθεῖς, ἀχάριστοι, ἀνόσιοι,
3 marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta,
ἄστοργοι, ἄσπονδοι, διάβολοι, ἀκρατεῖς, ἀνήμεροι, ἀφιλάγαθοι,
4 masu cin amana, marasa hankali, waɗanda sun cika da ɗaga kai, masu son jin daɗi a maimakon ƙaunar Allah
προδόται, προπετεῖς, τετυφωμένοι, φιλήδονοι μᾶλλον ἢ φιλόθεοι,
5 suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu yă haɗa ka da su.
ἔχοντες μόρφωσιν εὐσεβείας τὴν δὲ δύναμιν αὐτῆς ἠρνημένοι· καὶ τούτους ἀποτρέπου.
6 Irin su ne suke saɗaɗawa su shiga gidaje suna rinjayar mata marasa ƙarfin hali, waɗanda zunubai suka sha kansu, mugayen sha’awace-sha’awace kuma sun ɗauke hankulansu,
ἐκ τούτων γάρ εἰσιν οἱ ἐνδύνοντες εἰς τὰς οἰκίας καὶ αἰχμαλωτίζοντες γυναικάρια σεσωρευμένα ἁμαρτίαις, ἀγόμενα ἐπιθυμίαις ποικίλαις,
7 kullum suna koyo amma ba sa taɓa iya yarda da gaskiya.
πάντοτε μανθάνοντα καὶ μηδέποτε εἰς ἐπίγνωσιν ἀληθείας ἐλθεῖν δυνάμενα.
8 Kamar dai yadda Yannes da Yamberes suka tayar wa Musa, haka waɗannan mutane ma suke tayar wa gaskiya, mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda, in ana zancen bangaskiya ne, to, fa ba sa ciki.
ὃν τρόπον δὲ Ἰάννης καὶ Ἰαμβρῆς ἀντέστησαν Μωϋσεῖ, οὕτως καὶ οὗτοι ἀνθίστανται τῇ ἀληθείᾳ, ἄνθρωποι κατεφθαρμένοι τὸν νοῦν, ἀδόκιμοι περὶ τὴν πίστιν·
9 Sai dai ba za su yi nisa ba, don rashin hankalinsu zai bayyana ga kowa, kamar na mutanen nan biyu.
ἀλλ’ οὐ προκόψουσιν ἐπὶ πλεῖον, ἡ γὰρ ἄνοια αὐτῶν ἔκδηλος ἔσται πᾶσιν, ὡς καὶ ἡ ἐκείνων ἐγένετο.
10 Kai kam, ka san kome game da koyarwata, da halina, da niyyata, bangaskiya, haƙuri, ƙauna, jimiri,
Σὺ δὲ παρηκολούθησάς μου τῇ διδασκαλίᾳ, τῇ ἀγωγῇ, τῇ προθέσει, τῇ πίστει, τῇ μακροθυμίᾳ, τῇ ἀγάπῃ, τῇ ὑπομονῇ,
11 tsanani, shan wahala, irin abubuwan da suka faru da ni a Antiyok, Ikoniyum da kuma Listira, tsananin da na jure. Duk da haka Ubangiji ya cece ni daga dukansu.
τοῖς διωγμοῖς, τοῖς παθήμασιν, οἷά μοι ἐγένετο ἐν Ἀντιοχείᾳ, ἐν Ἰκονίῳ, ἐν Λύστροις· οἵους διωγμοὺς ὑπήνεγκα, καὶ ἐκ πάντων με ἐρύσατο ὁ κύριος.
12 Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani.
καὶ πάντες δὲ οἱ θέλοντες ζῆν εὐσεβῶς ἐν Χριστῷ Ἰησοῦ διωχθήσονται.
13 Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu.
Πονηροὶ δὲ ἄνθρωποι καὶ γόητες προκόψουσιν ἐπὶ τὸ χεῖρον, πλανῶντες καὶ πλανώμενοι.
14 Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su,
σὺ δὲ μένε ἐν οἷς ἔμαθες καὶ ἐπιστώθης, εἰδὼς παρὰ τίνων ἔμαθες,
15 da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.
καὶ ὅτι ἀπὸ βρέφους ἱερὰ γράμματα οἶδας, τὰ δυνάμενά σε σοφίσαι εἰς σωτηρίαν διὰ πίστεως τῆς ἐν Χριστῷ Ἰησοῦ.
16 Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci,
πᾶσα γραφὴ θεόπνευστος καὶ ὠφέλιμος πρὸς διδασκαλίαν, πρὸς ἐλεγμόν, πρὸς ἐπανόρθωσιν, πρὸς παιδείαν τὴν ἐν δικαιοσύνῃ,
17 domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.
ἵνα ἄρτιος ᾖ ὁ τοῦ θεοῦ ἄνθρωπος, πρὸς πᾶν ἔργον ἀγαθὸν ἐξηρτισμένος.

< 2 Timoti 3 >