< 2 Timoti 1 >

1 Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai wanda yake cikin Kiristi Yesu,
本信函来自保罗,是上帝所选、耶稣基督的使徒。这封信函是为了讲述在基督耶稣的真正生命中所讲述的承诺。
2 Zuwa ga Timoti, ƙaunataccen ɗana. Alheri, jinƙai da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.
这封信写给我亲爱的儿子提摩太,愿你们拥有来自父上帝和我们主基督耶稣的恩惠、怜悯和平安。
3 Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina.
我如此感谢上帝,就像我的祖先一样,以干净的良心事奉他。我始终都在想着你,在祈祷中提到你。
4 Sa’ad da na tuna da hawayenka, nakan yi marmarin ganinka, don in cika da farin ciki.
我记得你哭泣的样子,就更渴望见你,这会让我真正的感到幸福。
5 An tunashe ni da sahihiyar bangaskiyarka, wadda a farko ta kasance a cikin kakarka Loyis da kuma mahaifiyarka Yunis yanzu kuwa na tabbata tana cikinka.
我记得你对上帝真诚的信,你外祖母罗以和你母亲友尼基也有着同样的信,我知道这信也会在你心中延续。
6 Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwan nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗibiya maka hannuwana.
因此我想要提醒你,那时候我对你按手,你要把上帝借此赠给你的恩典礼物,赋予更多的力量。
7 Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.
因为上帝赐给我们的不是让我们胆怯的灵,而是有能力、爱心和理智的灵。
8 Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaida game da Ubangijinmu, ko kuwa ka ji kunyata, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi. Sai dai ka haɗa kai tare da ni cikin shan wahala saboda bishara ta wurin ikon Allah,
所以,不要因向其他人讲述我们的主而感到羞愧,也不要因为我而感到羞愧。你要准备好为福音而受磨难,因为上帝给了你力量。
9 wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal, (aiōnios g166)
他拯救了我们,呼唤我们过圣洁的生活,但不是通过我们的所作所为,而是通过上帝自己的计划,通过他的恩典。 (aiōnios g166)
10 amma yanzu an bayyana ta ta wurin bayyanuwar Mai Cetonmu, Kiristi Yesu, wanda ya hallaka mutuwa ya kuma kawo rai da rashin mutuwa a sarari ta wurin bishara.
早在开天辟地之时,他就通过基督耶稣将这恩典赐予我们,但直到现在才通过我们救世主基督耶稣的出现而显化。通过福音,他摧毁死亡,通过福音让生命和不朽变得无比清晰。
11 A wannan bishara ce, aka naɗa ni mai shela da manzo da kuma malami.
我是指派讲作为这福音的讲述者、使徒和教师。
12 Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa amana don wancan rana.
我也因此而受到这些苦,但我不以为耻,因为我知道所信是谁,也深信他能呵护我对他的托付,直到他再来的那一天。
13 Abin da ka ji daga gare ni, ka kiyaye shi kamar tsarin sahihiyar koyarwa, cikin bangaskiya da ƙauna cikin Kiristi Yesu.
你从我这里学到好的建议,以之为模范予以效仿,心怀信任和爱耶稣基督的态度。
14 Ka kiyaye kyakkyawar ajiyan nan da aka danƙa maka amana, ka lura da ita da taimakon Ruhu Mai Tsarki wanda yake raye a cikinmu.
你应通过住在我们心中的圣灵,保护托付给你的真理。
15 Ka san cewa kowa a lardin Asiya ya juya mini baya, har da Figelus da Hermogenes.
你已知道,所有亚西亚人都背弃了我,包括腓吉路和黑摩其尼。
16 Bari Ubangiji yă yi wa iyalin Onesiforus jinƙai, domin sau da dama yakan wartsakar da ni, bai kuma ji kunyar sarƙoƙina ba.
愿主怜悯阿尼色弗一家,因为他多次照顾我,也不因我关入监牢而为耻;
17 A maimakon haka ma, sa’ad da yake a Roma, ya neme ni ido a rufe sai da ya same ni.
他在罗马时,排除万难寻找我,最终找到了。
18 Bari Ubangiji yă sa yă sami jinƙai daga Ubangiji a wancan ranar! Ka sani sarai yadda ya taimake ni a hanyoyi dabam-dabam a Afisa.
愿主在审判日为他赐福。(提摩太,你很清楚在以弗所时,他为我做了很多)。

< 2 Timoti 1 >