< 2 Tessalonikawa 1 >

1 Bulus, da Sila, da Timoti, Zuwa ga ikkilisiya ta Tessalonikawa ta Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi.
パウロ、シルヴァノ及びチモテオ、我父にて在す神、及び主イエズス、キリストに在るテサロニケ人の教會に[書簡を贈る]。
2 Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.
願はくは我父にて在す神、及び主イエズス、キリストより、恩寵と平安とを汝等に賜はらん事を。
3 Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku,’yan’uwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba-gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa.
兄弟等よ、我等は絶えず汝等に就きて相當に神に感謝せざるべからず。是汝等の信仰益増加して、面々の愛情も皆互に豊なればなり。
4 Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da daurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha.
然れば我等自らも汝等を以て、即ち其忍べる凡ての迫害及び患難に於る忍耐と信仰とを以て、神の諸教會の間に誇とす。
5 Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala.
此患難は神の正しき審判の徴にして、汝等が神の國の為に苦しみて之に入るに足る者とせられん為なり。
6 Allah mai adalci ne, Zai sāka wa masu ba ku wahala da wahala
其は汝等を悩ます人々に悩を以て報い給ふは、神に取りて正當の事なれば、
7 yă kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru sa’ad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da mala’ikunsa masu iko.
悩める汝等にも我等と共に安息を賜ふ事正當なり。是主イエズス、其能力の天使等を随へて天より顕れ給ふ時の事にして、
8 Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba.
即ち焔の中に於て、神を知らざる人々、我主イエズス、キリストの福音に從はざる人々に報い給ふ時に當りて、
9 Za a hukunta su da madawwamiyar hallaka a kuma kau da su daga gaban Ubangiji da kuma daga ɗaukakar ikonsa (aiōnios g166)
彼等は主の御顔と其能力の光榮とを離れて終なき亡の罰を受けん、 (aiōnios g166)
10 a ranar da zai dawo don a ɗaukaka shi a cikin mutanensa masu tsarki, yă kuma zama abin banmamaki ga dukan waɗanda suka gaskata. Wannan ya haɗa har da ku, domin kun gaskata shaidar da muka yi muku.
其時主來り給ひて、其聖徒によりて光榮を受け給ひ、信じたる凡ての人より誉を得給ふべし、是我等の證する所、汝等に信ぜられたればなり。
11 Sane da wannan, kullum muna addu’a saboda ku, don Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ta wurin ikonsa kuma yă cika kowace manufarku mai kyau da kuma kowane aikin da bangaskiyarku ta iza.
故に我等常に汝等の為に祈りて、我神汝等をして其召に適はしめ、且及ぶ限り凡ての善意と信仰の業とを全うし給はん事を願ひ奉る。
12 Muna wannan addu’a don sunan Ubangijinmu Yesu yă sami ɗaukaka a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu da na Ubangiji Yesu Kiristi.
是我神と主イエズス、キリストとの恩寵に由りて、我主イエズス、キリストの御名汝等の中に光榮を着せられ、汝等も彼に在りて光榮を得ん為なり。

< 2 Tessalonikawa 1 >