< 2 Tessalonikawa 3 >
1 A ƙarshe,’yan’uwa, ku yi mana addu’a domin saƙon Ubangiji yă yi saurin bazuwa a kuma girmama shi, kamar yadda yake a wurinku.
Finally, brethren, pray for us, that the word of the Lord may rapidly spread, and be glorified, even as among you.
2 Ku kuma yi addu’a yadda za a cece mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama ba kowa ba ne yake da bangaskiya.
And that we may be delivered from unreasonable and wicked men; for all men have not faith.
3 Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan.
But the Lord is faithful, who will establish and keep you from the evil one.
4 Muna da tabbaci cikin Ubangiji cewa kuna bin umarnai da muka yi muku, za ku kuma ci gaba da yin abubuwan da muka umarta.
For we have confidence in the Lord concerning you, that you both do, and will do, the things which we command you.
5 Bari Ubangiji yă bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.
And may the Lord direct your hearts into the love of God and into the patience of Christ.
6 A cikin sunan Ubangiji Yesu Kiristi, muna muku umarni,’yan’uwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗan’uwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar da kuka karɓa daga wurinmu.
Now, we command you, brethren, by the name of our Lord Jesus Christ, that you withdraw yourselves from every brother who walks disorderly, and not according to the tradition which he received from us.
7 Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza sa’ad da muke tare da ku ba,
For yourselves know how you ought to imitate us--that we did not walk disorderly among you;
8 ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku.
but with labor and toil we wrought night and day, that we might not be burdensome to any of you.
9 Mun yi wannan, ba don ba mu da’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi.
Not because we have not a right, but that we might give ourselves to you for a pattern, to imitate us.
10 Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”
And, therefore, when we were with you, this we commanded you, that if any one will not work, neither let him eat.
11 Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum.
For we hear that there are some who still walk among you disorderly, not working at all, but prying into other people's affairs.
12 Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.
Now, them who are such, we command and beseech by our Lord Jesus Christ, that with quietness they work, and eat their own bread.
13 Game da ku kuma’yan’uwa, kada ku gaji da yin abin da yake daidai.
And you, brethren, be not weary in well doing.
14 In wani bai yi biyayya da umarninmu a wannan wasiƙa ba, sai fa ku lura da shi. Kada ku haɗa kai da shi, don yă ji kunya.
Now, if one do not obey our command in this letter, point out that man, and keep no company with him, that he may be ashamed.
15 Duk da haka kada ku mai da shi abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a matsayin ɗan’uwa.
Yet do not count him as an enemy, but admonish him as a brother.
16 Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yă ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yă kasance tare da ku duka.
And may the Lord of peace himself give you peace always, in every event. The Lord be with you all.
17 Ni, Bulus, nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna, wannan ce shaida a kowace wasiƙata, haka nake rubutu.
The salutation of Paul, with my own hand, which is the token in every epistle: thus I write.
18 Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku duka.
The favor of our Lord Jesus Christ be with you all. Amen.