< 2 Tessalonikawa 2 >

1 Game da dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi da game da tattara mu gare shi, muna roƙonku,’yan’uwa,
Ἐρωτῶμεν δὲ ὑμᾶς, ἀδελφοί, ὑπὲρ τῆς παρουσίας τοῦ Κυρίου ἡμῶν Ἰησοῦ Χριστοῦ, καὶ ἡμῶν ἐπισυναγωγῆς ἐπ᾽ αὐτόν,
2 kada ku yi saurin jijjiguwa ko kuwa hankalinku yă tashi ta wurin wani annabci, rahoto ko wasiƙar da an ce daga wurinmu ne, cewa ranar Ubangiji ta riga ta zo.
εἰς τὸ μὴ ταχέως σαλευθῆναι ὑμᾶς ἀπὸ τοῦ νοός, μήτε θροεῖσθαι, μήτε διὰ πνεύματος, μήτε διὰ λόγου, μήτε δι᾽ ἐπιστολῆς ὡς δι᾽ ἡμῶν, ὡς ὅτι ἐνέστηκεν ἡ ἡμέρα τοῦ Χριστοῦ·
3 Kada ku bar wani yă ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za tă zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka.
μή τις ὑμᾶς ἐξαπατήσῃ κατὰ μηδένα τρόπον· ὅτι ἐὰν μὴ ἔλθῃ ἡ ἀποστασία πρῶτον, καὶ ἀποκαλυφθῇ ὁ ἄνθρωπος τῆς ἁμαρτίας, ὁ υἱὸς τῆς ἀπωλείας,
4 Zai yi gāba yă kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yă kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne.
ὁ ἀντικείμενος καὶ ὑπεραιρόμενος ἐπὶ πάντα λεγόμενον θεὸν ἢ σέβασμα, ὥστε αὐτὸν εἰς τὸν ναὸν τοῦ Θεοῦ ὡς Θεὸν καθίσαι, ἀποδεικνύντα ἑαυτὸν ὅτι ἐστὶ Θεός.
5 Ba ku tuna ba cewa sa’ad da nake tare da ku nakan gaya muku waɗannan abubuwa?
Οὐ μνημονεύετε ὅτι ἔτι ὢν πρὸς ὑμᾶς, ταῦτα ἔλεγον ὑμῖν;
6 Yanzu kuwa kun san abin da yake hana shi, wannan yana faruwa ne don a bayyana shi a daidai lokaci.
Καὶ νῦν τὸ κατέχον οἴδατε, εἰς τὸ ἀποκαλυφθῆναι αὐτὸν ἐν τῷ ἑαυτοῦ καιρῷ.
7 Gama ikon asirin tawaye ya riga ya fara aiki; sai dai wannan da yake hana shi zai ci gaba da yin haka sai an kau da shi.
Τὸ γὰρ μυστήριον ἤδη ἐνεργεῖται τῆς ἀνομίας· μόνον ὁ κατέχων ἄρτι, ἕως ἐκ μέσου γένηται,
8 Sa’an nan za a bayyana mai tawayen, Ubangiji Yesu kuwa zai hamɓare shi da numfashin bakinsa yă kuma hallaka shi da darajar dawowarsa.
καὶ τότε ἀποκαλυφθήσεται ὁ ἄνομος, ὃν ὁ Κύριος ἀναλώσει τῷ πνεύματι τοῦ στόματος αὐτοῦ, καὶ καταργήσει τῇ ἐπιφανείᾳ τῆς παρουσίας αὐτοῦ·
9 Zuwan mai tawayen nan zai zama ta wurin aikin Shaiɗan da aka bayyana cikin kowane irin ayyukan banmamaki, alamu da abubuwan banmamaki na ƙarya,
οὗ ἐστιν ἡ παρουσία κατ᾽ ἐνέργειαν τοῦ Σατανᾶ ἐν πάσῃ δυνάμει καὶ σημείοις καὶ τέρασι ψεύδους,
10 da kuma cikin kowace irin muguntar da take ruɗin waɗanda suke hallaka. Sun hallaka ne domin sun ƙi su ƙaunaci gaskiya don su sami ceto.
καὶ ἐν πάσῃ ἀπάτῃ τῆς ἀδικίας ἐν τοῖς ἀπολλυμένοις, ἀνθ᾽ ὧν τὴν ἀγάπην τῆς ἀληθείας οὐκ ἐδέξαντο εἰς τὸ σωθῆναι αὐτούς.
11 Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya
Καὶ διὰ τοῦτο πέμψει αὐτοῖς ὁ Θεὸς ἐνέργειαν πλάνης, εἰς τὸ πιστεῦσαι αὐτοὺς τῷ ψεύδει·
12 don kuma a hukunta dukan waɗanda ba su gaskata gaskiyar ba sai dai suke jin daɗin mugunta.
ἵνα κριθῶσι πάντες οἱ μὴ πιστεύσαντες τῇ ἀληθείᾳ, ἀλλ᾽ εὐδοκήσαντες ἐν τῇ ἀδικίᾳ.
13 Amma dole kullum mu gode wa Allah dominku,’yan’uwa waɗanda Ubangiji ya ƙaunace, domin daga farko Allah ya zaɓe ku don a cece ku ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu da kuma ta wurin gaskatawa da gaskiya.
Ἡμεῖς δὲ ὀφείλομεν εὐχαριστεῖν τῷ Θεῷ πάντοτε περὶ ὑμῶν, ἀδελφοὶ ἠγαπημένοι ὑπὸ Κυρίου, ὅτι εἵλετο ὑμᾶς ὁ Θεὸς ἀπ᾽ ἀρχῆς εἰς σωτηρίαν ἐν ἁγιασμῷ πνεύματος, καὶ πίστει ἀληθείας·
14 Ya kira ku ga wannan ta wurin bishararmu, don ku sami rabo a cikin ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Kiristi.
εἰς ὃ ἐκάλεσεν ὑμᾶς διὰ τοῦ εὐαγγελίου ἡμῶν, εἰς περιποίησιν δόξης τοῦ Κυρίου ἡμῶν Ἰησοῦ Χριστοῦ.
15 Saboda haka fa,’yan’uwa, sai ku tsaya daram ku riƙe koyarwar da muka miƙa muku, ko ta wurin maganar baki ko kuma ta wurin wasiƙa.
Ἄρα οὖν, ἀδελφοί, στήκετε, καὶ κρατεῖτε τὰς παραδόσεις ἃς ἐδιδάχθητε, εἴτε διὰ λόγου, εἴτε δι᾽ ἐπιστολῆς ἡμῶν.
16 Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege, (aiōnios g166)
Αὐτὸς δὲ ὁ Κύριος ἡμῶν Ἰησοῦς Χριστός, καὶ ὁ Θεὸς καὶ πατὴρ ἡμῶν ὁ ἀγαπήσας ἡμᾶς, καὶ δοὺς παράκλησιν αἰωνίαν καὶ ἐλπίδα ἀγαθὴν ἐν χάριτι, (aiōnios g166)
17 yă ƙarfafa zukatanku yă kuma gina ku cikin kowane aikin nagari da kuma magana.
παρακαλέσαι ὑμῶν τὰς καρδίας, καὶ στηρίξαι ὑμᾶς ἐν παντὶ λόγῳ καὶ ἔργῳ ἀγαθῷ.

< 2 Tessalonikawa 2 >