< 2 Sama’ila 7 >
1 Bayan sarki ya kama zama a fadansa Ubangiji kuma ya hutashe shi daga dukan abokan gābansa da suke kewaye da shi,
And it came to pass, when the king dwelt in his house, and the LORD had given him rest from all his enemies round about,
2 sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar katakon al’ul, amma akwatin alkawarin Allah yana zaune a tenti.”
that the king said unto Nathan the prophet: 'See now, I dwell in a house of cedar, but the ark of God dwelleth within curtains.'
3 Natan ya amsa wa sarki ya ce, “Duk abin da yake a zuciyarka, sai ka yi, gama Ubangiji yana tare da kai.”
And Nathan said to the king: 'Go, do all that is in thy heart; for the LORD is with thee.'
4 A daren nan maganar Ubangiji ta zo wa Natan cewa,
And it came to pass the same night, that the word of the LORD came unto Nathan, saying:
5 “Je ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, kai ne za ka gina mini gida in zauna?
'Go and tell My servant David: Thus saith the LORD: Shalt thou build Me a house for Me to dwell in?
6 Ban taɓa zama a gida ba tun daga ranar da na fito da Isra’ilawa daga Masar har yă zuwa yau. Ina dai kai da kawowa a tenti, a matsayin mazaunina.
for I have not dwelt in a house since the day that I brought up the children of Israel out of Egypt, even to this day, but have walked in a tent and in a tabernacle.
7 A cikin kaiwa da kawowar da nake yi cikin dukan Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani shugabanninsu wanda na umarta su lura da mutanena Isra’ila, “Don me ba ku gina mini mazauni da katakon al’ul ba?”’
In all places wherein I have walked among all the children of Israel, spoke I a word with any of the tribes of Israel, whom I commanded to feed My people Israel, saying: Why have ye not built Me a house of cedar?
8 “Yanzu, ka gaya wa bawana Dawuda ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauko ka daga makiyaya, daga kuma garken tumaki ka zama sarki bisan mutane Isra’ila.
Now therefore thus shalt thou say unto My servant David: Thus saith the LORD of hosts: I took thee from the sheepcote, from following the sheep, that thou shouldest be prince over My people, over Israel.
9 Na kasance tare da kai duk inda ka tafi, na kuma kawar da dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka yă shahara kamar sunayen shahararrun mutanen duniya.
And I have been with thee whithersoever thou didst go, and have cut off all thine enemies from before thee; and I will make thee a great name, like unto the name of the great ones that are in the earth.
10 Zan kuma tanada wa mutanena Isra’ila wuri, in kuma dasa su yadda za su kasance da gida kansu ba tare da an ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba,
And I will appoint a place for My people Israel, and will plant them, that they may dwell in their own place, and be disquieted no more; neither shall the children of wickedness afflict them any more, as at the first,
11 yadda suka yi tun lokacin da na naɗa shugabanni bisan mutanena Isra’ila, zan kuma hutashe ka daga hannun abokan gābanka. “‘Ubangiji ya furta maka cewa Ubangiji kansa zai kafa maka gida.
even from the day that I commanded judges to be over My people Israel; and I will cause thee to rest from all thine enemies. Moreover the LORD telleth thee that the LORD will make thee a house.
12 Sa’ad da kwanakinka suka ƙare, za ka huta tare da kakanninka, zan tā da zuriyarka, na cikinka, zan kuma sa mulkinsa ya kahu.
When thy days are fulfilled, and thou shalt sleep with thy fathers, I will set up thy seed after thee, that shall proceed out of thy body, and I will establish his kingdom.
13 Shi zai gina gida domin Sunana, zan kuwa kafa gadon sarautarsa har abada.
He shall build a house for My name, and I will establish the throne of his kingdom for ever.
14 Zan zama Ubansa, shi kuma yă zama ɗana. Idan ya yi laifi, zan yi amfani da mutane in hukunta shi. Mutane ne za su zama bulalata.
I will be to him for a father, and he shall be to Me for a son; if he commit iniquity, I will chasten him with the rod of men, and with the stripes of the children of men;
15 Amma ba za a taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi yadda na ɗauke ta daga wurin Shawulu ba, shi wannan wanda na kawar daga gabanka.
but My mercy shall not depart from him, as I took it from Saul, whom I put away before thee.
16 Gidanka da kuma masarautarka za su dawwama har abada a gabana; gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’”
And thy house and thy kingdom shall be made sure for ever before thee; thy throne shall be established for ever.'
17 Natan ya gaya wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.
According to all these words, and according to all this vision, so did Nathan speak unto David.
18 Sa’an nan Sarki Dawuda ya je ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ko gidana, har da ka ɗaga mu zuwa wannan matsayi?
Then David the king went in, and sat before the LORD; and he said: 'Who am I, O Lord GOD, and what is my house, that Thou hast brought me thus far?
19 Har ya zama kamar wannan bai isa ba a gabanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka kuma yi magana game da nan gaba na gidan bawanka. Haka ka saba yi da mutane, ya Ubangiji Mai Iko Duka?
And this was yet a small thing in Thine eyes, O Lord GOD; but Thou hast spoken also of Thy servant's house for a great while to come; and this too after the manner of great men, O Lord GOD.
20 “Me kuma Dawuda zai ce maka? Gama ka san bawanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka.
And what can David say more unto Thee? for Thou knowest Thy servant, O Lord GOD.
21 Gama saboda maganarka da kuma bisa ga nufinka, ka aikata wannan babban abu, ka kuma sanar da bawanka.
For Thy word's sake, and according to Thine own heart, hast Thou wrought all this greatness, to make Thy servant know it.
22 “Kai mai girma ne, ya Ubangiji Mai Iko Duka! Babu wani kamar ka, babu kuma wani Allah sai kai; kamar yadda muka ji da kunnuwanmu.
Therefore Thou art great, O LORD God; for there is none like Thee, neither is there any God beside Thee, according to all that we have heard with our ears.
23 Wane ne kuma yake kamar da mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allah ya fita don yă kuɓutar wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa da kuma al’amuran banmamaki ta wurin korin al’ummai da allolinsu daga gaban mutanenka, waɗanda ka kuɓutar daga Masar?
And who is like Thy people, like Israel, a nation one in the earth, whom God went to redeem unto Himself for a people, and to make Him a name, and to do for Thy land great things and tremendous, even for you, in driving out from before Thy people, whom Thou didst redeem to Thee out of Egypt, the nations and their gods?
24 Ka kafa mutanenka Isra’ila kamar naka na kanka har abada, kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.
And Thou didst establish to Thyself Thy people Israel to be a people unto Thee for ever; and Thou, LORD, becamest their God.
25 “Yanzu kuwa, ya Ubangiji Allah, ka cika alkawarin da ka yi game da bawanka da gidansa. Ka yi kamar yadda ka alkawarta,
And now, O LORD God, the word that Thou hast spoken concerning Thy servant, and concerning his house, confirm Thou it for ever, and do as Thou hast spoken.
26 domin sunanka yă kasance da girma har abada. Sa’an nan mutane za su ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki, Allah ne a bisa Isra’ila!’ Kuma gidan bawanka Dawuda zai kahu a gabanka.
And let Thy name be magnified for ever, that it may be said: The LORD of hosts is God over Israel; and the house of Thy servant David shall be established before Thee.
27 “Ya Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka bayyana wa bawanka cewa, ‘Zan gina maka gida.’ Saboda haka bawanka ya sami ƙarfin hali yă miƙa maka wannan addu’a.
For Thou, O LORD of hosts, the God of Israel, hast revealed to Thy servant, saying: I will build thee a house; therefore hath Thy servant taken heart to pray this prayer unto Thee.
28 Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai Allah ne! Maganarka da aminci take, ka kuma yi wa bawanka waɗannan abubuwa masu kyau.
And now, O Lord GOD, Thou alone art God, and Thy words are truth, and Thou hast promised this good thing unto Thy servant;
29 In ya gamshe ka, bari ka albarkaci gidan bawanka don yă dawwama a gabanka har abada; gama kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka riga ka yi magana, kuma saboda kai ka sa albarka ga gidan bawanka, lalle zai kasance da albarka har abada.”
now therefore let it please Thee to bless the house of Thy servant, that it may continue for ever before Thee; for Thou, O Lord GOD, hast spoken it; and through Thy blessing let the house of Thy servant be blessed for ever.'