< 2 Sama’ila 6 >
1 Dawuda ya sāke tattara zaɓaɓɓun mutanen Isra’ila, dubu talatin.
2 Shi, da dukan mutanensa suka tashi daga Ba’ala-Yahuda don su hauro da akwatin alkawarin Allah, wanda ake kira da SunanUbangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a tsakanin kerubobin da suke a kan akwatin alkawarin.
3 Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah a sabuwar keken yaƙi, suka kawo shi daga gidan Abinadab, wanda yake bisa tudu. Uzza da Ahiyo,’ya’yan Abinadab maza, suka bi da keken yaƙin da akwatin alkawarin Allah yake ciki suka bi da keken yaƙin
4 da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo kuwa yana tafiya a gaban Abinadab.
5 Dawuda da dukan gidan Isra’ila suka yi biki sosai da dukan ƙarfinsu a gaban Ubangiji, da waƙoƙi, da molaye, da garayu, da ganguna, da kacau-kacau da kuma kuge.
6 Da suka kai masussukar Nakon, sai Uzza ya miƙa hannu don yă riƙe akwatin alkawarin Allah, gama shanun sun yi tuntuɓe.
7 Fushin Ubangiji kuwa ya ƙuna a kan Uzza domin aikin rashin bangirma, saboda haka Allah ya buge shi ya kuma mutu a can kusa da akwatin alkawarin Allah.
8 Ran Dawuda ya ɓace gama fushin Ubangiji ya ɓarke a kan Uzza. Shi ya sa har wa yau ana kira wurin Ferez Uzza.
9 Dawuda ya ji tsoron Ubangiji a ranar, sai ya ce, “Yaya akwatin alkawarin Ubangiji zai iya zuwa wurina?”
10 Bai so yă ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji yă kasance tare da shi a Birnin Dawuda ba. A maimakon haka sai ya kai shi gidan Obed-Edom mutumin Gat.
11 Akwatin Alkawarin Ubangiji ya kasance a gidan Obed-Edom mutumin Gat har tsawon wata uku, Ubangiji kuwa ya albarkace shi da dukan iyalinsa.
12 To, sai aka faɗa wa Sarki Dawuda cewa, “Ubangiji ya sa wa gidan Obed-Edom albarka da dukan abin da yake da shi, saboda akwatin alkawarin Allah.” Saboda haka sai Dawuda ya gangara ya hauro da akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-Edom zuwa Birnin Dawuda da farin ciki.
13 Sa’ad da waɗanda suke ɗaukan akwatin alkawarin Ubangiji suka yi tafiya taki shida, sai yă yi hadayar bijimi da saniya mai ƙiba.
14 Dawuda, sanye da efod lilin, ya yi ta rawa a gaban Ubangiji da dukan ƙarfinsa,
15 yayinda shi da dukan gidan Isra’ila suka hauro da akwatin alkawarin Ubangiji da sowa da kuma busar ƙahoni.
16 Sa’ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal’yar Shawulu ta leƙa ta taga ta ga Dawuda sarki yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta rena shi a zuciyarta.
17 Suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, aka ajiye shi a inda aka shirya masa a cikin tentin da Dawuda ya shirya dominsa. Dawuda kuma ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama a gaban Ubangiji.
18 Bayan ya gama yin hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki.
19 Sa’an nan ya rarraba abinci, da ƙosai, dabino, da waina ga kowane mutum a cikin dukan jama’ar Isra’ila, maza da mata. Dukan mutane kuwa suka watse zuwa gidajensu.
20 Da Dawuda ya koma gida don yă sa wa gidansa albarka, sai Mikal’yar Shawulu ta fito don tă tarye shi, sai ta ce, “Tabbas sarkin Isra’ila ya fiffita kansa yau, ya tuɓe a gaban bayinsa’yan mata, kamar yadda duk marar kunya yakan yi!”
21 Dawuda ya ce wa Mikal, “Na yi rawana domin in girmama Ubangiji ne, wanda ya zaɓe ni a maimakon mahaifinki ko wani daga cikin dukan gidansa, shi ne kuma ya sa ni sarki a kan Isra’ila, mutanen Ubangiji, zan yi biki a gaban Ubangiji.
22 Zan ma mai da kaina abin reni fiye da haka, za a kuma zama abin reni a gare ki. Amma waɗannan bayi’yan matan da kika yi magana a kai, za su gan ni da martaba.”
23 Mikal’yar Shawulu kuwa ba tă haifi ɗa ba har mutuwarta.