< 2 Sama’ila 24 >
1 Fushin Ubangiji ya sāke ƙuna a kan Isra’ila, sai ya zuga Dawuda, yana cewa, “Je ka ƙidaya Isra’ila da Yahuda.”
耶和华又向以色列人发怒,就激动大卫,使他吩咐人去数点以色列人和犹大人。
2 Saboda haka sarki ya ce wa Yowab da komandodin da suke tare da shi, “Tafi cikin dukan kabilan Isra’ila, daga Dan har zuwa Beyersheba, ku ƙidaya mayaƙa don in san yawansu.”
大卫就吩咐跟随他的元帅约押说:“你去走遍以色列众支派,从但直到别是巴,数点百姓,我好知道他们的数目。”
3 Amma Yowab ya ce wa sarki, “Ubangiji Allahnka ya sa mayaƙan su ƙaru sau ɗari fiye da yadda suke, har ranka yă daɗe, sarki yă gani da idonsa. Me ya sa ranka yă daɗe, sarki yake so yă yi abu haka?”
约押对王说:“无论百姓多少,愿耶和华—你的 神再加增百倍,使我主我王亲眼得见。我主我王何必喜悦行这事呢?”
4 Duk da haka, maganar sarki ya rinjayi Yowab da komandodin soja, sai suka tashi daga gaban sarki, suka tafi su ƙirga mayaƙan Isra’ila.
但王的命令胜过约押和众军长。约押和众军长就从王面前出去,数点以色列的百姓。
5 Bayan suka ƙetare Urdun, sai suka yi sansani kusa da Arower, kudu da garin da yake cikin kwari, sa’an nan suka ratsa ta wajen Gad, suka ci gaba zuwa Yazer.
他们过了约旦河,在迦得谷中、城的右边亚罗珥安营,与雅谢相对,
6 Suka tafi Gileyad ta yankin Tatim Hodshi, sa’an nan suka tafi Dan Ya’an, suka kuma yi wajen kewaye Sidon.
又到了基列和他停·合示地,又到了但·雅安,绕到西顿,
7 Sa’an nan suka yi ta wajen kagarar Taya da dukan garuruwan Hiwiyawa da Kan’aniyawa. A ƙarshe, suka ci gaba zuwa Beyersheba a Negeb na Yahuda.
来到泰尔的保障,并希未人和迦南人的各城,又到犹大南方的别是巴。
8 Bayan suka ratsa dukan ƙasashen, a ƙarshe suka koma Urushalima, bayan wata tara da kwana ashirin.
他们走遍全地,过了九个月零二十天,就回到耶路撒冷。
9 Yowab ya ba wa sarki jimillar yawan mayaƙan. A Isra’ila akwai mutum dubu ɗari takwas da za su iya riƙe takobi. A Yahuda kuwa mutum dubu ɗari biyar.
约押将百姓的总数奏告于王:以色列拿刀的勇士有八十万;犹大有五十万。
10 Bayan Dawuda ya ƙidaya mayaƙan, lamirinsa ya kāshe shi, sai ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji na yi laifi ƙwarai a kan abin da na yi. Ina roƙonka ka gafarta wa bawanka. Na yi wauta ƙwarai.”
大卫数点百姓以后,就心中自责,祷告耶和华说:“我行这事大有罪了。耶和华啊,求你除掉仆人的罪孽,因我所行的甚是愚昧。”
11 Kafin Dawuda yă tashi da safe kashegari, maganar Ubangiji ta riga ta zo wa annabin nan Gad, mai duban nan na Dawuda. Ubangiji ya ce,
大卫早晨起来,耶和华的话临到先知迦得,就是大卫的先见,说:
12 “Je ka faɗa wa Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, ina ba ka zaɓi uku. Ka zaɓi ɗaya daga cikinsu don in aikata maka shi.’”
“你去告诉大卫,说耶和华如此说:‘我有三样灾,随你选择一样,我好降与你。’”
13 Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Kana so a yi yunwa shekara uku a ƙasarka? Ko kana so ka yi ta gudu a gaban abokan gābanka har wata uku? Ko kuwa ka fi so a yi annoba kwana uku a ƙasarka? Yanzu, sai ka yi tunani, ka yanke shawarar game da amsar da zan mayar wa wanda ya aiko ni.”
于是迦得来见大卫,对他说:“你愿意国中有七年的饥荒呢?是在你敌人面前逃跑,被追赶三个月呢?是在你国中有三日的瘟疫呢?现在你要揣摩思想,我好回复那差我来的。”
14 Dawuda ya ce wa Gad, “Na shiga uku. Gara mu fāɗa a hannuwan Ubangiji gama alherinsa da girma yake. Amma fa kada ka bar ni in fāɗa a hannun mutane.”
大卫对迦得说:“我甚为难!我愿落在耶和华的手里,因为他有丰盛的怜悯。我不愿落在人的手里。”
15 Saboda haka Ubangiji ya aika da annoba a kan Isra’ila tun daga safe har zuwa lokacin da aka ƙayyade, mutum dubu saba’in kuwa daga Dan zuwa Beyersheba suka mutu.
于是,耶和华降瘟疫与以色列人,自早晨到所定的时候;从但直到别是巴,民间死了七万人。
16 Da mala’ikan Ubangiji ya miƙa hannunsa wajen Urushalima, don yă hallaka ta, sai Ubangiji ya tsai da masifar, ya ce wa mala’ikan da yake wahal da mutane, “Ya isa, ka janye hannunka.” A lokacin kuwa Mala’ikan Ubangiji yana tsaye a masussukar Arauna, mutumin Yebus.
天使向耶路撒冷伸手要灭城的时候,耶和华后悔,就不降这灾了,吩咐灭民的天使说:“够了!住手吧!”那时耶和华的使者在耶布斯人亚劳拿的禾场那里。
17 Da Dawuda ya ga mala’ikan da ya bubbugi mutane, sai ya ce wa Ubangiji, “Ni ne na yi zunubi, na kuma yi abin da ba daidai ba. Waɗannan tumaki ne kawai. Me suka yi? Bari hukuncinka yă sauko a kaina da iyalina.”
大卫看见灭民的天使,就祷告耶和华说:“我犯了罪,行了恶;但这群羊做了什么呢?愿你的手攻击我和我的父家。”
18 A ranar, Gad ya koma wurin Dawuda ya ce, “Ka tashi, ka tafi ka gina wa Ubangiji bagade a masussukar Arauna, mutumin Yebus.”
当日,迦得来见大卫,对他说:“你上去,在耶布斯人亚劳拿的禾场上为耶和华筑一座坛。”
19 Saboda haka Dawuda ya haura, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Gad.
大卫就照着迦得奉耶和华名所说的话上去了。
20 Da Arauna ya hangi Dawuda da mutanensa suna zuwa wajensa, sai ya fita a guje, ya je ya rusuna a gaban sarki.
亚劳拿观看,见王和他臣仆前来,就迎接出去,脸伏于地,向王下拜,
21 Arauna ya ce, “Me ya sa ranka yă daɗe, sarki ya zo wajen bawansa?” Dawuda ya ce, “Don in saya masussukarka, saboda in gina wa Ubangiji bagade don a tsayar da annoban da suke a bisa mutane.”
说:“我主我王为何来到仆人这里呢?”大卫说:“我要买你这禾场,为耶和华筑一座坛,使民间的瘟疫止住。”
22 Arauna ya ce wa Dawuda, “Bari ranka yă daɗe, sarki yă ɗauki duk abin da ya ga dama yă miƙa shi. Ga shanu, don hadaya ta ƙonawa, ga kuma kayan masussuka da itacen shanu, don itace.”
亚劳拿对大卫说:“我主我王,你喜悦用什么,就拿去献祭。看哪,这里有牛可以作燔祭,有打粮的器具和套牛的轭可以当柴烧。
23 Dukan wannan, ranka yă daɗe, Arauna ya ba wa sarki. Arauna ya kuma ce, “Bari Ubangiji Allahnka yă karɓa.”
王啊,这一切,我亚劳拿都奉给你”;又对王说:“愿耶和华—你的 神悦纳你。”
24 Amma sarki ya ce wa Arauna, “A’a, dole in biya ka saboda waɗannan. Ba yadda zan miƙa wa Ubangiji Allahna hadayun ƙonawa da bai ci mini kome ba.” Sai Dawuda ya saya, ya kuma biya masussukar, da shanun a bakin shekel hamsin na azurfa.
王对亚劳拿说:“不然。我必要按着价值向你买;我不肯用白得之物作燔祭献给耶和华—我的 神。”大卫就用五十舍客勒银子买了那禾场与牛。
25 Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Sa’an nan Ubangiji ya amsa addu’o’in a madadin ƙasar, aka kuma kawar wa Isra’ila annoban.
大卫在那里为耶和华筑了一座坛,献燔祭和平安祭。如此,耶和华垂听国民所求的,瘟疫在以色列人中就止住了。