< 2 Sama’ila 2 >
1 Bayan’yan kwanaki, sai Dawuda ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In haura zuwa ɗaya daga cikin biranen Yahuda?” Ubangiji ya ce, “Haura.” Dawuda ya ce, “Wanne zan tafi?” Ubangiji ya ce, “Je Hebron.”
2 Saboda haka sai Dawuda ya tafi can tare da matansa biyu, Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel.
3 Dawuda kuma ya tafi tare da dukan mutanen da suke tare da shi, kowa da iyalinsa, suka zauna a Hebron da garuruwansa.
4 Sa’an nan mutanen Yahuda suka zo Hebron, a can kuwa suka naɗa Dawuda sarkin Yahuda. Sa’ad da aka gaya wa Dawuda cewa mutanen Yabesh Gileyad ne suka binne Shawulu,
5 sai ya aiki manzanni zuwa Yabesh Gileyad a ce musu, “Ubangiji yă albarkace ku saboda alherin da kuka nuna wa Shawulu ta wurin binne shi.
6 Bari Ubangiji yă nuna muku ƙaunarsa da amincinsa, ni kuma zan nuna muku irin wannan alherin saboda kun yi haka.
7 Yanzu fa, sai ku ƙarfafa, ku yi jaruntaka, gama Shawulu sarkinku ya mutu, gidan Yahuda kuwa sun naɗa ni sarki a kansu.”
8 Ana cikin haka, Abner ɗan Ner, komandan sojojin Shawulu, ya ɗauki Ish-Boshet ɗan Shawulu ya kawo shi Mahanayim.
9 Ya naɗa shi sarkin Gileyad, da na Ashuri, da na Yezireyel, da a kan Efraim, da Benyamin, da kuma na dukan Isra’ila.
10 Ish-Boshet ɗan Shawulu yana da shekaru arba’in sa’ad da ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi sarauta shekara biyu. Amma fa, gidan Yahuda, suka bi Dawuda.
11 Tsawon lokacin da Dawuda ya yi mulki a Hebron a kan gidan Yahuda, shekara bakwai ne da wata shida.
12 Abner ɗan Ner, tare da mutanen Ish-Boshet ɗan Shawulu, suka bar Mahanayim suka tafi Gibeyon.
13 Yowab wanda ake ce mamarsa Zeruhiya tare da waɗansu mutanen Dawuda suka fito suka haɗu da su tafkin Gibeyon, Suka zauna, waɗannan a wannan gefe, waɗancan a wancan gefe.
14 Sa’an nan Abner ya ce wa Yowab, “Bari mu bar waɗansu samari su tashi su yi faɗa hannu da hannu a gabanmu.” Yowab ya ce, “To, su tashi.”
15 Saboda haka samarin suka tashi aka ƙidaya su, mutum sha biyu wajen Benyamin da Ish-Boshet ɗan Shawulu, sha biyu kuma wajen Dawuda.
16 Sa’an nan kowannensu ya kama abokin gābansa a kā ya soki da wuƙa a jiki, sai duka suka fāɗi a ƙasa. Saboda haka ne ake kiran wannan wuri Helkat Hazzurim a Gibeyon.
17 Faɗan ya yi zafi a ranar ƙwarai, mutanen Dawuda suka ci mutanen Abner da na Isra’ila.
18 ’Ya’yan Zeruhiya, maza uku sun kasance a can. Su ne, Yowab, Abishai da Asahel. To, Asahel mai gudu ne kamar barewa.
19 Ya fafari Abner, bai juya dama ko hagu ba, yayinda yake fafararsa.
20 Abner ya waiga, sai ya ce, “Kai ne, Asahel?” Ya ce, “Ni ne.”
21 Sai Abner ya ce masa, “Yi dama ko hagu ka runtumi ɗaya daga cikin samarin, ka ƙwace makamansa.” Amma Asahel bai bar fafararsa ba.
22 Abner ya sāke gargaɗe shi ya ce, “Ka bar fafarata! Yaya zan kashe ka? Yaya zan yin ido biyu da ɗan’uwanka Yowab?”
23 Amma Asahel ya ƙi yă bar fafararsa; saboda haka Abner ya soki Asahel da māshinsa a ciki; har māshin ya fita ta bayansa. Nan take ya fāɗi, ya mutu. Kowa da ya zo wurin da Asahel ya fāɗi, ya mutu, sai yă tsaya.
24 Amma Yowab da Abishai suka fafari Abner, kuma da rana tana fāɗuwa sai suka iso tudun Amma, kusa da Giya, a hanyar zuwa jejin Gibeyon.
25 Sa’an nan mutanen Benyamin suka haɗa kansu suka koyi bayan Abner. Suka zama ƙungiya guda, suka tsaya daram a kan tudu.
26 Sai Abner ya kira Yowab ya ce, har abada ne māshi zai yi ta hallakarwa? Ba ka sani cewa ƙarshen zai zama da ɗaci ba. Sai yaushe za ka umarci mutanenka su daina fafaran’yan’uwansu?
27 Yowab ya ce, “Muddin Allah yana a raye, da ba a ce ka yi magana ba, da mutanen za su ci gaba da fafaran’yan’uwansu har gari yă waye.”
28 Sai Yowab ya busa ƙaho, dukan mutane kuwa suka tsaya; suka daina fafaran Isra’ila. Nan take faɗan ya tsaya.
29 Abner da mutanensa suka ratsa kwarin Urdun dukan dare. Sa’an nan suka haye kogin, suka kuwa ci gaba dukan safe har suka zo Mahanayim.
30 Da Yowab ya dawo daga fafaran Abner, sai ya tattara dukan mutanensa. Ban da Asahel, sai ya gane an rasa mutum goma sha tara na Dawuda.
31 Amma mutanen Dawuda sun kashe mutum ɗari uku da sittin daga kabilar Benyamin da suke tare da Abner.
32 Suka ɗauki gawar Asahel suka binne a kabarin mahaifinsa a Betlehem. Sa’an nan Yowab da mutanensa suka bi dare har suka iso Hebron da safe.