< 2 Sama’ila 19 >
1 Aka faɗa wa Yowab cewa, “Sarki yana kuka, yana kuma makoki saboda Absalom.”
有人告诉约押说:“王为押沙龙哭泣悲哀。”
2 Saboda haka sai nasarar da aka yi a ranar ta zama makoki ga dukan sojoji, gama a ranar, rundunoni sun ji an ce, “Sarki yana baƙin ciki domin ɗansa.”
众民听说王为他儿子忧愁,他们得胜的欢乐却变成悲哀。
3 Mutane fa suka shiga birni shiru, sai ka ce waɗanda sukan sace jiki don kunya sa’ad da suka gudo daga yaƙi.
那日众民暗暗地进城,就如败阵逃跑、惭愧的民一般。
4 Sarki ya rufe fuskarsa ya yi kuka da ƙarfi yana cewa, “Ya ɗana Absalom! Ya Absalom ɗana, ɗana!”
王蒙着脸,大声哭号说:“我儿押沙龙啊!押沙龙,我儿,我儿啊!”
5 Sai Yowab ya shiga gidan sarki ya ce, “Yau ka kunyatar da dukan mutanenka, waɗanda ba da daɗewa ba sun ceci ranka, da rayukan’ya’yanka maza, da na’ya’yanka mata, da na matanka da kuma na ƙwarƙwaranka.
约押进去见王,说:“你今日使你一切仆人脸面惭愧了!他们今日救了你的性命和你儿女妻妾的性命,
6 Kana ƙaunar maƙiyinka, kana ƙin waɗanda suke ƙaunarka. Ka bayyana a fili cewa komandodi da sojojinsu ba kome ba ne a gare ka. Na ga cewa da za ka yi farin ciki, da a ce Absalom yana da rai a yau, dukanmu kuma mun mutu.
你却爱那恨你的人,恨那爱你的人。你今日明明地不以将帅、仆人为念。我今日看明,若押沙龙活着,我们都死亡,你就喜悦了。
7 Yanzu ka fita ka ƙarfafa mutanenka. Na rantse da Ubangiji, in ba ka fita ba, babu mutum guda da za a bari tare da kai a daren nan. Wannan zai fi maka muni fiye da kowace irin masifar da ta auko maka tun ƙuruciyarka har zuwa yanzu.”
现在你当出去,安慰你仆人的心。我指着耶和华起誓:你若不出去,今夜必无一人与你同在一处;这祸患就比你从幼年到如今所遭的更甚!”
8 Saboda haka sarki ya tashi, ya zauna a bakin hanyar shiga. Da aka faɗa wa mutane cewa, “Sarki yana zaune a bakin hanyar shiga,” sai duk suka zo gabansa. Ana cikin haka, Isra’ilawa dai sun riga sun tsere zuwa gidajensu.
于是王起来,坐在城门口。众民听说王坐在城门口,就都到王面前。 以色列人已经逃跑,各回各家去了。
9 Mutane ko’ina a kabilan Isra’ila, suka yi ta gardama da juna, suna cewa, “Sarki ne ya cece mu daga hannun abokan gābanmu, shi ne kuma ya kuɓutar da mu daga hannun Filistiyawa. Amma ga shi ya tsere daga ƙasar saboda Absalom;
以色列众支派的人纷纷议论说:“王曾救我们脱离仇敌的手,又救我们脱离非利士人的手,现在他躲避押沙龙逃走了。
10 kuma shi Absalom, da muka naɗa yă yi mulkinmu, ya mutu a yaƙi. Saboda haka don me ba kwa ce wani abu game da dawo da sarki?”
我们膏押沙龙治理我们,他已经阵亡。现在为什么不出一言请王回来呢?”
11 Sai Sarki Dawuda ya aika da saƙo zuwa wurin Zadok da Abiyatar, firistoci, ya ce, “Ku tambayi dattawan Yahuda, ‘Me ya sa ku ne za ku zama na ƙarshe a yin tunanin komar da sarki zuwa fada, da yake abin da ake faɗi ko’ina a Isra’ila ya kai kunnen sarki a mazauninsa?
大卫王差人去见祭司撒督和亚比亚他,说:“你们当向犹大长老说:‘以色列众人已经有话请王回宫,你们为什么落在他们后头呢?
12 Ku’yan’uwana ne, jikina, jinina kuma. To, don me za ku zama na ƙarshe na yarda a dawo da sarki zuwa fada?’
你们是我的弟兄,是我的骨肉,为什么在人后头请王回来呢?’
13 Ku kuma ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba jikina ba ne da jinina? Allah yă hukunta ni, da hukunci mai tsanani, idan daga yanzu ba ka zama komandan sojojina a maimakon Yowab ba.’”
也要对亚玛撒说:‘你不是我的骨肉吗?我若不立你替约押常作元帅,愿 神重重地降罚与我!’”
14 Ta haka ya rinjayi zukatan dukan mutane Yahuda, kamar mutum ɗaya. Suka aika da saƙo wurin sarki suka ce, “Ka dawo, kai da dukan mutanenka.”
如此就挽回犹大众人的心,如同一人的心。他们便打发人去见王,说:“请王和王的一切臣仆回来。”
15 Sa’an nan sarki ya dawo, ya kuma tafi har zuwa Urdun. To, mutanen Yahuda suka zo Gilgal don su fita su taryi sarki, su kuma kawo shi ƙetaren Urdun.
王就回来,到了约旦河。犹大人来到吉甲,要去迎接王,请他过约旦河。
16 Shimeyi ɗan Gera, mutumin Benyamin daga Bahurim ya gaggauta, ya gangara tare da mutanen Yahuda don su taryi Sarki Dawuda.
巴户琳的便雅悯人、基拉的儿子示每急忙与犹大人一同下去迎接大卫王。
17 Tare da shi akwai kabilar Benyamin mutum dubu, tare da Ziba, mai hidimar gidan Shawulu, da’ya’yansa maza goma sha biyar, da bayi ashirin. Suka ruga zuwa Urdun, inda sarki yake.
跟从示每的有一千便雅悯人,还有扫罗家的仆人洗巴和他十五个儿子,二十个仆人;他们都趟过约旦河迎接王。
18 Suka haye a mashigin don su ƙetaro da iyalin sarki, su kuma yi duk abin da yake so. Sa’ad da Shimeyi ɗan Gera ya haye Urdun, sai ya fāɗi rubda ciki a gaban sarki
有摆渡船过去,渡王的家眷,任王使用。 王要过约旦河的时候,基拉的儿子示每就俯伏在王面前,
19 ya ce masa, “Ranka yă daɗe, ina roƙonka kada ka riƙe laifina a zuciya. Kada ka tuna da laifin da na yi maka ranka yă daɗe, ranan nan da kake gudu daga Urushalima. Kada ka tuna da shi ko kaɗan.
对王说:“我主我王出耶路撒冷的时候,仆人行悖逆的事,现在求我主不要因此加罪与仆人,不要记念,也不要放在心上。
20 Na sani ni bawanka na yi maka laifi. Shi ya sa na zama na farko daga dukan Gidan Yusuf, da mutanen Isra’ila wanda ya fito don yă tarye ka yau, ranka yă daɗe, sarki.”
仆人明知自己有罪,所以约瑟全家之中,今日我首先下来迎接我主我王。”
21 Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce, “Bai kamata a kashe Shimeyi saboda wannan ba? Ya la’anci shafaffe na Ubangiji.”
洗鲁雅的儿子亚比筛说:“示每既咒骂耶和华的受膏者,不应当治死他吗?”
22 Dawuda ya ce, “Me ya haɗa ni da ku, ku’ya’yan Zeruhiya? Yau ɗin nan kun zama maƙiyana! Ya kamata a kashe wani a Isra’ila a yau? Ban san cewa yau ni sarki ne a bisa Isra’ila ba?”
大卫说:“洗鲁雅的儿子,我与你们有何关涉,使你们今日与我反对呢?今日在以色列中岂可治死人呢?我岂不知今日我作以色列的王吗?”
23 Saboda haka sarki ya ce wa Shimeyi, “Ba za ka mutu ba.” Sarki kuwa ya yi alkawari har da rantsuwa.
于是王对示每说:“你必不死。”王就向他起誓。
24 Mefiboshet, jikan Shawulu, shi ma ya gangara don yă taryi sarki. Tun daga ranar da sarki ya gudu har ran da ya komo lafiya, Mefiboshet bai lura da ƙafafunsa, ko yă aske gemunsa, ko yă wanke tufafinsa ba.
扫罗的孙子米非波设也下去迎接王。他自从王去的日子,直到王平平安安地回来,没有修脚,没有剃胡须,也没有洗衣服。
25 Sa’ad da ya zo daga Urushalima don yă taryi sarki, sai sarki ya ce masa, “Me ya sa ba ka tafi tare da ni ba Mefiboshet?”
他来到耶路撒冷迎接王的时候,王问他说:“米非波设,你为什么没有与我同去呢?”
26 Sai ya ce, “Ranka yă daɗe sarki, da yake bawanka gurgu ne, na ce, ‘A sa mini sirdi a kan jakina don in hau in tafi tare da sarki.’ Amma Ziba bawana ya bashe ni.
他回答说:“我主我王,仆人是瘸腿的。那日我想要备驴骑上,与王同去,无奈我的仆人欺哄了我,
27 Ya kuwa ɓata suna bawanka a gaban ranka yă daɗe, sarki. Ranka yă daɗe, sarki yana kama da mala’ikan Allah, ka yi abin da ka ga ya fi maka kyau.
又在我主我王面前谗毁我。然而我主我王如同 神的使者一般,你看怎样好,就怎样行吧!
28 Duk zuriyar kakana ba su cancanci kome ba sai mutuwa daga ranka yă daɗe, amma ka ba wa bawanka wuri cikin mutanen da suke ci a teburinka. Saboda haka, wanda’yanci nake da shi da zan yi wani ƙarin roƙo a wurin sarki?”
因为我祖全家的人,在我主我王面前都算为死人,王却使仆人在王的席上同人吃饭,我现在向王还能辨理诉冤吗?”
29 Sarki ya ce masa, “Me ya sa kake zancen nan? Ai, na riga na umarta, da kai, da Ziba ku raba filayen.”
王对他说:“你何必再提你的事呢?我说,你与洗巴均分地土。”
30 Mefiboshet ya ce wa sarki, “Bari yă ɗauki kome, yanzu da ranka yă daɗe, sarki ya dawo gida lafiya.”
米非波设对王说:“我主我王既平平安安地回宫,就任凭洗巴都取了也可以。”
31 Barzillai mutumin Gileyad shi ma ya zo daga Rogelim don yă ƙetare Urdun tare da sarki, yă kuma sallame shi daga can.
基列人巴西莱从罗基琳下来,要送王过约旦河,就与王一同过了约旦河。
32 To, Barzillai fa tsoho ne, mai shekara tamanin. Ya tanada wa sarki a lokaci da yake Mahanayim, gama shi attajiri ne.
巴西莱年纪老迈,已经八十岁了。王住在玛哈念的时候,他就拿食物来供给王;他原是大富户。
33 Sarki ya ce wa Barzillai, “Ka ƙetaro tare da ni ka zauna tare da ni a Urushalima, zan kuwa tanada maka.”
王对巴西莱说:“你与我同去,我要在耶路撒冷那里养你的老。”
34 Amma Barzillai ya ce wa sarki, “Shekara nawa ya rage mini har da zan tafi Urushalima da sarki?
巴西莱对王说:“我在世的年日还能有多少,使我与王同上耶路撒冷呢?
35 Yanzu ina da shekara tamanin. Zan iya bambanta abu mai daɗi da marar daɗi kuma ne? Bawanka zai iya jin ɗanɗano abin da yake ci, ko yake sha ne? Har yanzu zan iya jin muryoyin mawaƙan maza da mata? Don me bawanka zai zama ƙari kaya ga ranka yă daɗe?
仆人现在八十岁了,还能尝出饮食的滋味、辨别美恶吗?还能听男女歌唱的声音吗?仆人何必累赘我主我王呢?
36 Bawanka zai ƙetare Urdun tare da sarki, yă ɗan yi maka rakiya kaɗan. Me ya sa ranka yă daɗe zai ba ni irin wannan lada.
仆人只要送王过约旦河,王何必赐我这样的恩典呢?
37 Ka bar bawanka yă koma, don in mutu a garina, kusa da kabarin mahaifina da mahaifiyata. Amma ga bawanka Kimham. Bari yă ƙetare tare da ranka yă daɗe, sarki. Ka yi abin da ka ga dama da shi.”
求你准我回去,好死在我本城,葬在我父母的墓旁。这里有王的仆人金罕,让他同我主我王过去,可以随意待他。”
38 Sarki ya ce, “Kimham zai ƙetare tare da ni, zan kuwa yi masa abin da ya gamshe ka. Kuma duk abin da kake bukata a wurina, zan yi maka.”
王说:“金罕可以与我同去,我必照你的心愿待他。你向我求什么,我都必为你成就。”
39 Saboda haka dukan mutane suka ƙetare Urdun, sa’an nan kuma sarki ma ya ƙetare. Sarki ya yi wa Barzillai sumba ya albarkace shi, sa’an nan Barzillai ya koma gidansa.
于是众民过约旦河,王也过去。王与巴西莱亲嘴,为他祝福,巴西莱就回本地去了。
40 Sa’ad da sarki ya ƙetare zuwa Gilgal, Kimham ma ya ƙetare tare da shi. Dukan sojojin Yahuda da rabin sojojin Isra’ila suka ƙetare da sarki.
王过去,到了吉甲,金罕也跟他过去。犹大众民和以色列民的一半也都送王过去。
41 Nan take sai ga mutane Isra’ila suna zuwa wurin sarki, suna cewa, “Don me’yan’uwanmu, mutanen Yahuda, suka saci sarki, suka kawo shi da iyalinsa a ƙetaren Urdun, tare da dukan mutanensa?”
以色列众人来见王,对他说:“我们弟兄犹大人为什么暗暗送王和王的家眷,并跟随王的人过约旦河?”
42 Dukan mutanen Yahuda suka ce wa mutanen Isra’ila, “Mun yi haka domin sarki danginmu na kurkusa ne. Don me kuke fushi game da wannan? Mun ci wani abu daga cikin kayan sarki ne? Mun ɗauki wani abu wa kanmu ne?”
犹大众人回答以色列人说:“因为王与我们是亲属,你们为何因这事发怒呢?我们吃了王的什么呢?王赏赐了我们什么呢?”
43 Sa’an nan mutanen Isra’ila suka ce wa mutanen Yahuda, “Muna da rabo goma a wurin sarki; ban da haka ma, muna da hakki mafi yawa a wurin Dawuda fiye da ku. Don me kuke mana reni? Ba mu ne ma muka fara magana dawowa da sarki ba?” Amma mutanen Yahuda suka ɗauka maganar da zafi fiye da mutanen Isra’ila.
以色列人回答犹大人说:“按支派,我们与王有十分的情分;在大卫身上,我们也比你们更有情分。你们为何藐视我们,请王回来不先与我们商量呢?” 但犹大人的话比以色列人的话更硬。