< 2 Bitrus 1 >

1 Siman Bitrus, bawa da kuma manzon Yesu Kiristi, Zuwa ga waɗanda ta wurin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi sun sami bangaskiya mai daraja irin tamu.
Siman Bitrus, bawa da manzon Almasihu Yesu, zuwa ga wadanda suka karbi bangaskiya mai daraja kamar yadda muka karba, bangaskiya cikin adalcin Allahnmu da Yesu Almasihu.
2 Alheri da salama su zama naku a yalwace ta wurin sanin Allah da Yesu Ubangijinmu.
Bari alheri ya kasance tare da ku; bari salama ta karu ta wurin sanin Allah da na Yesu Ubangijinmu.
3 Ikonsa na Allahntaka ya ba mu kome da muke bukata don rayuwa da kuma tsoron Allah ta wurin sanin wanda ya kira mu ta wurin ɗaukakarsa da nagartarsa.
Dukkan abubuwan ikon Allah na rayuwa da Allahntaka an bamu su ta wurin sanin Allah, wanda ya kira mu ta wurin daukakarsa da nagarta.
4 Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen sha’awace-sha’awace suke jawowa.
Ta wurin wanan, ya bamu babban alkawari mai daraja. Yayi wanan ne saboda ku zama masu rabo cikin Allahntaka, yayin da ku ka kubuta daga lalacewa da ke cikin duniya saboda mugayen sha'awace sha, awace.
5 Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani;
Saboda wanan dalilin kuyi iyakacin kokarinku ku kara nagarta ta wurin bangaskiyarku, kuma ta wurin adalci, sani.
6 ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah;
Ta wurin sani ku kara da kamun kai, kuma ta wurin kamun kanku, ku kara da jimrewa, ta wurin jimrewarku, ku kara da bin Allah.
7 ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga’yan’uwa; ga nuna alheri ga’yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna.
Ta wurin bin Allah, ku kara da kauna irin ta 'yan'uwa, ta wurin kauna irin ta 'yan'uwa, ku kara kauna.
8 Domin in kuna ƙaruwa a waɗannan halaye, za su kāre ku daga rashin tasiri da rayuwa na rashin amfani cikin saninku na Ubangijinmu Yesu Kiristi.
Idan wadannan abubuwan suna cikinku, kuma suka yi girma a cikinku, baza a sami bakarare ko rashin 'ya'ya cikin sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu ba.
9 Amma in wani ba shi da su, ba shi da hangen nesa ke nan kuma makaho ne, ya kuma manta cewa an tsarkake shi daga zunubansa na dā.
Amma duk wanda ya rasa wadannan abubuwan yana kallon abin da ke kusa ne kawai; ya makance. Ya manta da cewa an wake shi daga tsofaffin zunubansa.
10 Saboda haka’yan’uwana, ku ƙara aniya wajen tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Gama in kuka yi waɗannan abubuwa, ba za ku taɓa fāɗuwa ba,
Saboda haka, 'yan'uwa, kuyi iyakacin kokari ku tabbatar da kiranku da zabenku. Idan kun yi wadannan abubuwan, baza ku yi tuntube ba.
11 za ku sami kyakkyawar marabta cikin madawwamin mulkin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi. (aiōnios g166)
Ta haka zaku sami shiga cikin mulki na har'abada na Ubangijinmu da Maicetonmu Yesu Almasihu. (aiōnios g166)
12 Saboda haka kullum zan tuna muku da waɗannan, ko da yake kun sansu kun kuma kahu ƙwarai cikin gaskiyar da kuke da ita yanzu.
Saboda haka a shirye nake kulayomi in tunashe ku game da wadannan abubuwan, ko da yake kun san su, kuma kun yi karfi cikin gaskiya yanzu.
13 A ganina ya dace in tunashe ku muddin ina raye cikin tentin wannan jiki,
Ina tunani daidai ne in zuga ku da tuni game da wadannan abubuwan, tun ina cikin wannan jiki.
14 domin na sani na kusa in ajiye shi a gefe, yadda Ubangijinmu Yesu Kiristi ya nuna mini a sarari.
Domin na sani jim kadan zan bar wannan jiki, kamar yadda Yesu Almasihu ya nuna mani.
15 Zan kuwa yi iyakacin ƙoƙari in ga cewa bayan rabuwata kullum za ku iya tuna da waɗannan abubuwa.
Zan yi iyakancin kokarina kulayomi domin ku rika tunawa da abubuwan, bayan kaurata.
16 Ba mu bi tatsuniyoyin da aka ƙaga da wayo sa’ad da muka gaya muku game da ikon Ubangijinmu Yesu Kiristi da zuwansa ba, sai dai mu shaidu ne na ɗaukakarsa mai girma da muka gani da ido.
Domin bamu bi labaru da aka kago na nuna wayo cikinsu ba, da muka fada maku game da iko da bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu, amma mu shaidu ne na ikonsa.
17 Gama ya sami girma da ɗaukaka daga Allah Uba sa’ad da murya ta zo masa daga Mafificiyar Ɗaukaka cewa, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; da shi nake jin daɗi ƙwarai.”
Gama ya karbi daukaka da daraja daga wurin Allah Uba lokacin da murya ta zo daga ikon mai daukaka cewa, “Wannan shine dana, kaunataccena, wanda nake jin dadinsa kwarai.”
18 Mu kanmu mun ji wannan muryar da ta zo daga sama sa’ad da muke tare da shi a kan dutse mai tsarki.
Mun ji muryar nan da ta zo daga sama, lokacin da mu ke tare da shi a dutse mai tsarki.
19 Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har yă zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku.
Muna da wannan kalmar annabci wanda akwai tabbaci sosai, kun yi daidai idan kun mayar da hankali a kansu. Yana nan kamar fitillar da take walkiya a wuri mai duhu kafin asubahi ya zo, kuma tauraron asubahi ya tashi cikin zukatanku.
20 Gaba da kome dai, dole ku gane cewa babu annabcin Nassin da ya fito daga fassarar annabi da kansa.
Ku san da wannan tun da farko, cewa babu annabci da ke bisa ga fasarar mutum.
21 Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.
Domin babu annabcin da ya taba zuwa ta wurin nufin mutum. Maimakon haka, Ruhu Mai Tsarki ne ke iza su, su fadi maganar Allah.

< 2 Bitrus 1 >