< 2 Bitrus 3 >
1 Abokaina ƙaunatattu, wannan ita ce wasiƙata ta biyu gare ku. Na rubuta su biyun su zama abin tuni don su faɗakar da ku ga tunani mai kyau.
Hanc ecce vobis, carissimi, secundam scribo epistolam, in quibus vestram excito in commonitione sinceram mentem:
2 Ina so ku tuna da kalmomin da annabawa masu tsarki na dā suka faɗa da kuma umarnin da Ubangijinmu da Mai Cetonmu ya bayar ta wurin manzanninku.
ut memores sitis eorum, quæ prædixi, verborum, a sanctis prophetis et apostolorum vestrorum, præceptorum Domini et Salvatoris.
3 Da farko dai, dole ku fahimci wannan cewa a kwanakin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna bin mugayen sha’awace-sha’awacensu.
Hoc primum scientes, quod venient in novissimis diebus in deceptione illusores, juxta proprias concupiscentias ambulantes,
4 Za su ce, “Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta.”
dicentes: Ubi est promissio, aut adventus ejus? ex quo enim patres dormierunt, omnia sic perseverant ab initio creaturæ.
5 Amma da gangan suke manta cewa tun dā can ta wurin maganar Allah sammai suka kasance aka kuma yi ƙasa daga ruwa ta wurin ruwa kuma.
Latet enim eos hoc volentes, quod cæli erant prius, et terra de aqua, et per aquam consistens Dei verbo:
6 Ta wurin waɗannan ruwan ne aka nutsar, aka kuma hallakar da duniya ta wancan lokaci.
per quæ, ille tunc mundus aqua inundatus, periit.
7 Ta wurin wannan magana ce aka ajiye sammai da ƙasa na yanzu domin wuta, an ajiye su kuma don ranar hukunci da hallaka ta mutane marasa tsoron Allah.
Cæli autem, qui nunc sunt, et terra eodem verbo repositi sunt, igni reservati in diem judicii, et perditionis impiorum hominum.
8 Amma kada ku manta da wannan abu guda ɗaya, abokaina ƙaunatattu. Ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekaru dubu ne, shekaru dubu kuma kamar kwana ɗaya ne.
Unum vero hoc non lateat vos, carissimi, quia unus dies apud Dominum sicut mille anni, et mille anni sicut dies unus.
9 Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.
Non tardat Dominus promissionem suam, sicut quidam existimant: sed patienter agit propter vos, nolens aliquos perire, sed omnes ad pœnitentiam reverti.
10 Amma ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo. Sammai za su ɓace da ruri, abubuwan da suke cikinsu za su ƙone, ƙasa kuma da dukan abin da yake cikinta za su tonu.
Adveniet autem dies Domini ut fur: in quo cæli magno impetu transient, elementa vero calore solventur, terra autem et quæ in ipsa sunt opera, exurentur.
11 Da yake za a hallaka dukan abubuwa ta haka, waɗanne irin mutane ne ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi rayuwar tsarki da ta tsoron Allah,
Cum igitur hæc omnia dissolvenda sunt, quales oportet vos esse in sanctis conversationibus, et pietatibus,
12 yayinda kuke zuba ido ga zuwan ranar Allah kuna gaggauta zuwanta. Wannan rana za tă kawo wa sammai hallaka ta ƙunan wuta, abubuwa kuma za su narke don zafi.
exspectantes, et properantes in adventum diei Domini, per quem cæli ardentes solventur, et elementa ignis ardore tabescent?
13 Amma bisa ga alkawarinsa muna zuba ido ga sabuwar sama da kuma sabuwar ƙasa, inda adalci zai yi zama.
Novos vero cælos, et novam terram secundum promissa ipsius exspectamus, in quibus justitia habitat.
14 Saboda haka, abokaina ƙaunatattu, da yake kuna zuba ido ga wannan, sai ku yi matuƙar ƙoƙari don a same ku ba tabo, sai dai zaman salama da shi.
Propter quod, carissimi, hæc exspectantes, satagite immaculati, et inviolati ei inveniri in pace:
15 Ku yi zaman sanin cewa haƙurin Ubangijinmu yana nufin ceto ne, kamar yadda ƙaunataccen ɗan’uwanmu Bulus ma ya rubuta muku da hikimar da Allah ya ba shi.
et Domini nostri longanimitatem, salutem arbitremini: sicut et carissimus frater noster Paulus secundum datam sibi sapientiam scripsit vobis,
16 Haka yake rubutu cikin dukan wasiƙunsa, yana magana a cikinsu a kan waɗannan al’amura. Wasiƙunsa sun ƙunshi waɗansu abubuwa masu wuyar fahimta, waɗanda jahilai da kuma waɗanda ba tsayayyu ba ne suke murɗe ma’anarsu, kamar yadda suke yi da sauran Nassosi, ta haka suke jawo wa kansu hallaka.
sicut et omnibus epistolis, loquens in eis de his in quibus sunt quædam difficilia intellectu, quæ indocti et instabiles depravant, sicut et ceteras Scripturas, ad suam ipsorum perditionem.
17 Saboda haka, abokaina ƙaunatattu, da yake kun riga kun san wannan, sai ku zauna a faɗake don kada a ɗauke hankalinku ta wurin kuskuren marasa bin dokan nan har ku fāɗi daga matsayinku.
Vos igitur fratres, præscientes custodite, ne insipientium errore traducti excidatis a propria firmitate:
18 Sai dai ku yi girma cikin alheri da sanin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka ta tabbata yanzu da har abada! Amin. (aiōn )
crescite vero in gratia, et in cognitione Domini nostri, et Salvatoris Jesu Christi. Ipsi gloria et nunc, et in diem æternitatis. Amen. (aiōn )