< 2 Bitrus 2 >
1 Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya.
But there were also false prophets among the people, even as there shall be among you lying teachers, who shall bring in sects of perdition, and deny the Lord who bought them: bringing upon themselves swift destruction.
2 Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya.
And many shall follow their riotousnesses, through whom the way of truth shall be evil spoken of.
3 Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.
And through covetousness shall they with feigned words make merchandise of you. Whose judgment now of a long time lingereth not, and their perdition slumbereth not.
4 Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci; (Tartaroō )
For if God spared not the angels that sinned, but delivered them, drawn down by infernal ropes to the lower hell, unto torments, to be reserved unto judgment: (Tartaroō )
5 in har bai ƙyale duniya ta dā ba sa’ad da ya kawo ambaliya a kan mutanenta marasa tsoron Allah, amma ya kiyaye Nuhu, mai wa’azin adalci, da kuma waɗansu bakwai;
And spared not the original world, but preserved Noe, the eighth person, the preacher of justice, bringing in the flood upon the world of the ungodly.
6 in har ya hukunta biranen Sodom da Gomorra ta wurin ƙone su suka zama toka, ya kuma maishe su misali na abin da zai faru da marasa tsoron Allah;
And reducing the cities of the Sodomites, and of the Gomorrhites, into ashes, condemned them to be overthrown, making them an example to those that should after act wickedly.
7 in kuwa har ya ceci Lot, mai adalci, wanda ya damu ainun da ƙazamar rayuwar mutane marasa bin doka;
And delivered just Lot, oppressed by the injustice and lewd conversation of the wicked.
8 (adon kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa’ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci)
For in sight and hearing he was just: dwelling among them, who from day to day vexed the just soul with unjust works.
9 in haka ne, to, Ubangiji ya san yadda zai ceci mutane masu tsoron Allah daga gwaje-gwaje, yă kuma tsare marasa adalci don ranar hukunci, har yă zuwa ranar shari’a.
The Lord knoweth how to deliver the godly from temptation, but to reserve the unjust unto the day of judgment to be tormented.
10 Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki. Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama;
And especially them who walk after the flesh in the lust of uncleanness, and despise government, audacious, self willed, they fear not to bring in sects, blaspheming.
11 duk da haka ko mala’iku ma da suka fi su ƙarfi suka kuma fi su iko, ba sa kawo irin wannan zargi na ɓata suna game da waɗannan talikai a gaban Ubangiji.
Whereas angels who are greater in strength and power, bring not against themselves a railing judgment.
12 Amma waɗannan mutane suna yin saɓo a kan abubuwan da ba su fahimta ba. Suna kama da dabbobi marasa hankali, halittun da suke bin abin da jikinsu ya faɗa musu kawai, waɗanda aka haifa don a kama a hallaka, kuma kamar dabbobi su ma za su hallaka.
But these men, as irrational beasts, naturally tending to the snare and to destruction, blaspheming those things which they know not, shall perish in their corruption,
13 Za a yi musu sakamako da muguntar da suka yi. A ra’ayinsu jin daɗi shi ne a yi annashuwa da rana tsaka. Su ƙazamai ne marasa kunya, suna cike da jin daɗin sha’awace-sha’awacensu yayinda suke cin biki tare da ku.
Receiving the reward of their injustice, counting for a pleasure the delights of a day: stains and spots, sporting themselves to excess, rioting in their feasts with you:
14 Idanunsu sun cike da zina, ba sa ƙoshi da yin zunubi; suna jarrabtar waɗanda ba tsayayyu ba; gwanaye ne a kan kwaɗayi, la’anannun iri!
Having eyes full of adultery and of sin that ceaseth not: alluring unstable souls, having their heart exercised with covetousness, children of malediction:
15 Sun bar miƙaƙƙiyar hanya suka bauɗe suna bin hanyar Bala’am ɗan Beyor, wanda ya yi ƙaunar hakkin mugunta.
Leaving the right way they have gone astray, having followed the way of Balaam of Bosor, who loved the wages of iniquity,
16 Amma an tsawata masa saboda laifinsa ta wurin jaki, dabbar da ba ta magana, wadda ta yi magana da muryar mutum ta kuma kwaɓi haukan annabin.
But had a check of his madness, the dumb beast used to the yoke, which speaking with man’s voice, forbade the folly of the prophet.
17 Waɗannan mutane maɓulɓulai ne babu ruwa da kuma hazon da guguwar iska take kora. An shirya matsanancin duhu dominsu.
These are fountains without water, and clouds tossed with whirlwinds, to whom the mist of darkness is reserved.
18 Gama suna surutai banza na girman kai, ta wurin son bin fasikanci na mutuntaka, sukan jan hankulan mutanen da suke kuɓucewa daga waɗancan masu zama cikin kuskure.
For, speaking proud words of vanity, they allure by the desires of fleshly riotousness, those who for a little while escape, such as converse in error:
19 Suna yin musu alkawarin’yanci, yayinda su kansu bayi ne ga aikin lalata gama mutum bawa ne ga duk abin da ya mallake shi.
Promising them liberty, whereas they themselves are the slaves of corruption. For by whom a man is overcome, of the same also he is the slave.
20 In har sun kuɓuta daga lalacin duniya ta wurin sanin Ubangijinmu da kuma Mai Cetonmu Yesu Kiristi sai suka sāke koma a cikin lalacin, har ya rinjaye su, za su fi muni a ƙarshe fiye da farko.
For if, flying from the pollutions of the world, through the knowledge of our Lord and Saviour Jesus Christ, they be again entangled in them and overcome: their latter state is become unto them worse than the former.
21 Zai fi musu kyau da ba su taɓa sanin hanyar adalci ba, fiye da a ce sun sani sa’an nan su juya bayansu ga umarni mai tsarkin nan da aka ba su.
For it had been better for them not to have known the way of justice, than after they have known it, to turn back from that holy commandment which was delivered to them.
22 A kansu karin maganan nan gaskiya ce, “Kare ya koma kan amansa,” da kuma, “Alade da aka yi wa wanka, ya koma birgimarsa cikin laka.”
For, that of the true proverb has happened to them: The dog is returned to his vomit: and, The sow that was washed, to her wallowing in the mire.