< 2 Sarakuna 7 >
1 Sai Elisha ya ce, “Ku ji maganar Ubangiji. Ga abin da Ubangiji ya ce, gobe war haka, za a sayar da mudun gari mai laushi a farashin shekel guda, mudu biyu na sha’ir kuma a shekel ɗaya a ƙofar birnin Samariya.”
2 Sai wani hafsa mataimakin sarki ya ce wa mutumin Allah, “Kai, ko da Ubangiji zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba!” Sai Elisha ya ce, “Za ka gani da idanunka, zai faru, amma ba za ka ci ba!”
3 To, akwai waɗansu kutare huɗu a ƙofar gari. Suka ce wa junansu, “Don me za mu zauna a nan sai mun mutu?
4 In muka ce, ‘Za mu shiga cikin birni’ yunwa tana can, za mu kuwa mutu. Idan kuwa muka zauna a nan, za mu mutu. Saboda haka, bari mu ƙetare zuwa sansanin Arameyawa mu miƙa kai. Idan suka bar mu da rai, to; idan kuwa suka kashe mu, shi ke nan.”
5 Da yamma sai suka tashi suka tafi sansanin Arameyawa. Yayinda suka shiga tsakiyar sansanin Arameyawa kuwa, sai suka tarar ba kowa a can,
6 gama Ubangiji ya sa rundunar Arameyawa suka ji motsin kekunan yaƙi, da motsin dawakai, da na babban rundunar sojoji, saboda haka suka ce wa juna; “Duba, sarkin Isra’ila ya ɗauka hayar sarakuna Hittiyawa da sarakunan Masarawa don su yaƙe mu!”
7 Saboda haka suka tashi, suka gudu da yamma, suka bar tentunansu, da dawakansu, da jakunansu. Suka bar sansanin yadda yake, suka gudu don su ceci rayukansu.
8 Da kutaren nan suka kai bakin sansanin, sai suka shiga wani tenti, suka ci, suka sha, suka kwashi azurfa, da zinariya, da riguna, suka tafi, suka ɓoye su. Sa’an nan suka koma, suka shiga wani tenti, sai suka kwashi kaya daga ciki, suka kuma ɓoye su.
9 Sa’an nan suka ce wa juna, “Ba mu yi abin kirki ba. Wannan rana ce ta albishiri amma muka yi shiru; in kuwa mun bari har gari ya waye, to, fa, wata masifa za tă fāɗo mana. Bari mu tafi nan take mu faɗa a fadan sarki.”
10 Saboda haka suka je suka kira masu tsaron ƙofar birni, suka ce musu, “Mun je sansanin Arameyawa, ga shi kuwa ba mu iske kowa a can ba, babu ko motsin wani, sai dai dawakai da jakuna a daure, tentunan kuwa suna nan yadda suke.”
11 Sai matsaran ƙofar suka sanar da labarin a cikin fada.
12 Sai sarki ya tashi da daren nan ya ce wa hafsoshinsa, “Na san abin da Arameyawan suke shiri! Sun san game da yunwar da muke ciki a nan, domin haka sun bar sansaninsu suka shiga jeji suka ɓuya, suna nufin sa’ad da muka fita daga birni, sai su kama mu da rai, sa’an nan su shiga birnin.”
13 Ɗaya daga cikin fadawan sarki ya ce, “A sa waɗansu mutane su ɗauki dawakai biyar da suka ragu cikin birni, idan ba su tsira ba, za su zama kamar sauran Isra’ilawan da suka riga suka mutu ne. Bari mu aika, mu gani.”
14 Saboda haka suka zaɓi kekunan yaƙi biyu tare da dawakansu, sarki kuwa ya aike su su bi bayan sojojin Arameyawa. Ya umarci masu tuƙinsu ya ce, “Ku je ku bincika abin da ya faru.”
15 Suka bi sawunsu har Urdun, suka ga tufafi da makamai barjat ko’ina a hanya waɗanda Arameyawa suka zubar yayinda suke gudu. Sai’yan aika suka dawo suka ba wa sarki labari.
16 Sa’an nan jama’a suka fita suka kwashi ganima a sansanin Arameyawa. Aka kuwa sayar da gari mai laushi a farashin shekel guda, mudu biyu na sha’ir kuma a shekel guda, yadda Ubangiji ya faɗi.
17 Sai ya kasance cewa Sarki ya sa dogari wanda ya raka shi wajen Elisha ya tsare ƙofar birnin. Sai mutane suka tattake shi a ƙofar har ya mutu, kamar yadda annabi Elisha ya faɗa sa’ad da sarki ya tafi wurinsa.
18 Haka kuwa ya kasance kamar yadda mutumin Allah ya ce wa sarki, “Gobe war haka, za a sayar da mudun gari shekel guda, mudun sha’ir biyu ma a shekel guda, a ƙofar Samariya.”
19 Hafsan ya riga ya ce wa mutumin Allah, “Kai, ko da Ubangiji zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba!” Mutumin Allah kuwa ya faɗa masa, “Za ka gani da idanunka sai dai ba za ka ci ba!”
20 Haka kuwa ya kasance, gama mutane sun tattake shi a hanyar shiga, har ya mutu.