< 2 Sarakuna 4 >
1 Matar wani daga ƙungiyar annabawa ta yi wa Elisha kuka ta ce, “Mijina, bawanka, ya mutu, ka kuma san yadda ya girmama Ubangiji. Amma ga shi yanzu mai binsa bashi ya zo yă kwashe’ya’yana maza biyu su zama bayinsa.”
2 Elisha ya amsa mata ya ce, “Me kike so in yi miki? Ki faɗa mini, me kike da shi a gidanki?” Sai ta ce, “Baiwarka ba ta da kome a can, sai ɗan tulun man zaitun.”
3 Elisha ya ce, “Ki je wurin dukan maƙwabtanki, ki nemi tulunan da babu kome a ciki. Kada ki nemo kaɗan kawai.
4 Sa’an nan ki shiga ciki, ki kulle ƙofar da ke da’ya’yanki kuke ciki. Ku ɗuɗɗura man a dukan tulunan, sa’ad da kowanne ya cika, sai ki ajiye a gefe.”
5 Ta tashi ta shiga tare da’ya’yanta maza, suka kulle ƙofa.’Ya’yanta suka kawo mata tuluna, ita kuma tana ɗurawa.
6 Da dukan tulunan suka cika, sai ta ce wa ɗanta, “Kawo mini wani tulu.” Amma ya amsa ya ce, “Ai, ba saura.” Sa’an nan man ya daina zuba.
7 Sai ta tafi ta faɗa wa mutumin Allah. Shi kuwa ya ce mata, “Tafi, ki sayar da man, ki biya bashinki. Ki biya bukatanki da na’ya’yanki da sauran da ya rage.”
8 Wata rana Elisha ya tafi Shunem. Akwai wata mai arziki a can wadda ta gayyace shi cin abinci. Sai ya zama duk lokacin da yake wucewa, yakan tsaya a can don cin abinci.
9 Ta ce wa mijinta, “Na san cewa wannan mutum da kullum yake zuwa nan mai tsarki ne na Allah.
10 Bari mu yi ɗan ɗaki a rufin gida mu kuma sa masa gado da tebur da kujera da kuma fitila. Saboda a duk lokacin da ya zo wurinmu, sai yă sauka a can.”
11 Wata rana da Elisha ya zo, sai ya haura ɗakinsa ya kwanta.
12 Ya ce wa bawansa Gehazi, “Kira mutuniyar Shunam nan.” Sai ya kira ta, ta zo ta tsaya a gabansa.
13 Elisha ya ce masa, “Ka ce mata, ‘Kin yi duk wannan ɗawainiya saboda mu. Yanzu, me kike so a yi miki? Kina so mu yi magana a madadinki wa sarki ko babban hafsan mayaƙa?’” Sai ta ce, “A’a, ina da dukan abin da nake bukata a cikin jama’ata.”
14 Sai Elisha ya tambayi Gehazi ya ce, “Me za mu yi mata?” Sai ya amsa ya ce, “Ba ta da ɗa, ga shi kuma mijinta ya tsufa.”
15 Sai Elisha ya ce, “Ka kira ta.” Sai ya kira ta, ta zo ta tsaya a bakin ƙofa.
16 Elisha ya ce mata, “War haka baɗi, za ki riƙe ɗa na kanki.” Sai ta ce masa, “A’a, ranka yă daɗe, mutumin Allah, kada ka ruɗi baiwarka!”
17 Amma matan ta yi ciki, a shekara ta biye kuwa a daidai lokacin, sai ta haifi ɗa kamar yadda Elisha ya faɗa mata.
18 Yaron ya yi girma, wata rana sai ya tafi wurin mahaifinsa, wanda yake tare da masu girbi.
19 Ba zato sai ya ce wa mahaifinsa, “Wayyo! Kaina yana mini ciwo! Kaina yana mini ciwo!” Sai mahaifinsa ya ce wa bawansa, “Kai shi wurin mahaifiyarsa.”
20 Bayan bawan ya ɗaga shi ya kai wurin mahaifiyarsa, sai yaron ya zauna a cinyarta har tsakar rana, sa’an nan ya mutu.
21 Sai ta haura ta shimfiɗa shi a gadon mutumin Allah, ta rufe ƙofar, ta fita.
22 Ta kira mijinta ta ce, “Ina roƙonka ka aika mini da ɗaya daga cikin bayi da kuma jaka, don in yi sauri in je wurin mutumin Allah in dawo.”
23 Sai ya ce, “Me zai kai ki wurinsa, ai, yau ba Sabon Wata ba ne ko ranar Asabbaci?” Sai ta ce, “Ba kome.”
24 Sai ta sa wa jakar sirdi ta ce wa bawanta, “Yi ta kora mini jakar, kada ka sassauta, sai na faɗa maka.”
25 Ta haka ta kama hanya ta tafi wurin mutumin Allah a Dutsen Karmel. Da ya hange ta daga nesa, sai mutumin Allah ya ce wa bawansa Gehazi, “Duba! Ga mutuniyar Shunam nan can!
26 Ka yi gudu ka tarye ta ka tambaye ta, ‘Lafiyarki? Mijinki yana nan lafiya? Yaronki yana nan lafiya?’” Ta amsa ta ce, “Kome lafiya yake.”
27 Da ta isa wurin mutumin Allah a dutsen, sai ta kama ƙafafunsa. Sai Gehazi ya zo don yă ture ta, amma mutumin Allah ya ce, “Ka bar ta! Tana cikin baƙin ciki ƙwarai, amma Ubangiji ya ɓoye mini, bai kuma faɗa mini me ya sa ba.”
28 Sai ta tambaya shi ta ce, “Na roƙe ka ɗa ne, ranka yă daɗe? Ba na ce maka, ‘Kada ka sa in fara bege ba’?”
29 Elisha ya ce wa Gehazi, “Ka yi ɗamara, ka ɗauki sandana ka ruga a guje. Idan ka sadu da wani, kada ka gaishe shi, idan kuma wani ya gaishe ka, kada ka amsa. Ka shimfiɗa sandana a fuskar yaron.”
30 Amma mahaifiyar yaron ta ce, “Muddin Ubangiji yana raye, kai kuma kana a raye, ba zan bar ka ba.” Saboda haka ya tashi ya bi ta.
31 Gehazi ya yi gaba, ya shimfiɗa sandan a fuskar yaron, amma babu motsi, babu alamar rai. Saboda haka Gehazi ya koma ya taryi Elisha, ya faɗa masa, “Yaron bai tashi ba.”
32 Da Elisha ya isa gidan, sai ga gawar yaron kwance a kan gadonsa.
33 Sai ya shiga, ya rufe ƙofa, daga shi sai yaron, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji.
34 Sa’an nan ya hau gadon yă kwanta a bisa yaron, ya miƙe a kansa, baki da baki, ido da ido, hannu da hannu. Yayinda ya miƙe kansa a kan yaron, sai jikin yaron ya ɗau ɗumi.
35 Elisha ya tashi, ya yi ta kai komo a cikin ɗakin. Sa’an nan ya sāke koma kan gadon yă miƙe a kan yaron, sai yaron ya yi atishawa sau bakwai, ya kuma buɗe idanunsa.
36 Elisha ya kira Gehazi ya ce, “Kirawo mutuniyar Shunam.” Ya kuwa kira ta. Sa’ad da ta zo, sai Elisha ya ce mata, “Ɗauki ɗanki.”
37 Sai ta shiga, ta fāɗi a ƙafafunsa ta rusuna har ƙasa. Sa’an nan ta ɗauki ɗanta ta fita.
38 Sai Elisha ya koma Gilgal, a can kuwa ana yunwa a yankin. Yayinda ƙungiyar annabawa suke tattaunawa da shi, sai ya ce wa Gehazi bawansa, “Ka sa babban tukunya a wuta, ka yi wa mutanen nan fate.”
39 Ɗaya daga cikin mutanen ya shiga gona don neman ganyaye, ya kuwa sami kabewar jeji. Ya tsinko’ya’yanta cike da shafin rigarsa. Da ya dawo, sai ya yayyanka su ya zuba a cikin tukunyar faten, ko da yake ba wanda ya san ko mene ne.
40 Sai aka zuba wa mutanen faten, amma da suka fara ci, sai suka yi ihu suna cewa, “Ya mutumin Allah, akwai dafi a cikin tukunyan nan!” Suka kuwa kāsa ci.
41 Elisha ya ce, “Samo mini ɗan gari.” Aka kawo masa ya kuma sa a cikin tukunyan ya ce, “Raba wa mutanen su ci.” Ya kasance kuwa babu wani abin damuwa a tukunyar.
42 Sai ga wani mutum ya zo daga Ba’al-Shalisha, ya kawo wa Elisha dunƙulen burodi guda ashirin na sha’ir da aka gasa daga nunan fari na hatsi, tare da kawunan sababbin hatsi. Sai Elisha ya ce, “Ka ba mutanen su ci.”
43 Sai bawansa ya ce, “Yaya zan raba wa mutane ɗari wannan?” Amma Elisha ya amsa ya ce, “Ka raba wa mutane su ci, gama haka Ubangiji ya ce, ‘Za su ci har su bar saura.’”
44 Sa’an nan ya ajiye a gabansu, suka kuwa ci har suka bar saura, bisa ga maganar Ubangiji.