< 2 Sarakuna 24 >

1 A zamani Yehohiyakim, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kawo wa ƙasar farmaki, Yehohiyakim dai ya zama abokin tarayyarsa na tsawon shekara uku. Daga baya kuma sai ya canja ra’ayi ya yi wa Nebukadnezzar tawaye.
בימיו עלה נבכדנאצר מלך בבל ויהי לו יהויקים עבד שלש שנים וישב וימרד בו
2 Ubangiji ya aiki maharan Babiloniyawa, da na Arameyawa, da na Mowabawa, da na Ammonawa. Ya aike su su hallaka Yahuda bisa ga maganar Ubangiji wadda ya furta ta bakin bayinsa annabawa.
וישלח יהוה בו את גדודי כשדים ואת גדודי ארם ואת גדודי מואב ואת גדודי בני עמון וישלחם ביהודה להאבידו כדבר יהוה--אשר דבר ביד עבדיו הנביאים
3 Ba shakka waɗannan abubuwa sun faru da Yahuda bisa ga umarnin Ubangiji domin yă kawar da su daga gabansa saboda zunuban Manasse da dukan abin da ya yi,
אך על פי יהוה היתה ביהודה להסיר מעל פניו--בחטאת מנשה ככל אשר עשה
4 haɗe da zub da jinin marasa laifi. Gama ya ƙazantar da Urushalima da jinin marasa laifi. Ubangiji kuwa bai yi niyyar yafewa ba.
וגם דם הנקי אשר שפך וימלא את ירושלם דם נקי ולא אבה יהוה לסלח
5 Game da sauran ayyukan mulkin Yehohiyakim da abubuwan da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.
ויתר דברי יהויקים וכל אשר עשה הלא הם כתובים על ספר דברי הימים--למלכי יהודה
6 Yehohiyakim ya huta da kakanninsa. Yehohiyacin ɗansa ya gāje shi.
וישכב יהויקים עם אבתיו וימלך יהויכין בנו תחתיו
7 Sarkin Masar bai sāke fita daga ƙasarsa don yaƙi ba domin sarkin Babilon ya mamaye yankin, daga Rafin Masar har zuwa Kogin Yuferites.
ולא הסיף עוד מלך מצרים לצאת מארצו כי לקח מלך בבל מנחל מצרים עד נהר פרת כל אשר היתה למלך מצרים
8 Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas da ya zama sarki, ya kuma yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Nehushta’yar Elnatan, mutuniyar Urushalima.
בן שמנה עשרה שנה יהויכין במלכו ושלשה חדשים מלך בירושלם ושם אמו נחשתא בת אלנתן מירושלם
9 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi.
ויעש הרע בעיני יהוה ככל אשר עשה אביו
10 A wannan lokaci, hafsoshin Nebukadnezzar sarkin Babilon suka kawo wa Urushalima yaƙi, suka kuma kewaye ta.
בעת ההיא--עלה (עלו) עבדי נבכדנאצר מלך בבל ירושלם ותבא העיר במצור
11 Nebukadnezzar na Babilon da kansa kuwa ya zo birnin yayinda hafsoshinsa suka kewaye ta.
ויבא נבכדנאצר מלך בבל על העיר ועבדיו צרים עליה
12 Yehohiyacin sarkin Yahuda, da mahaifiyarsa, da masu yi masa hidima, da hakimansa, da kuma fadawansa duk suka miƙa kansu ga Nebukadnezzar. A shekara ta takwas ta mulkin sarkin Babilon, sarkin Babilon ya mai da Yehohiyacin ɗan kurkuku.
ויצא יהויכין מלך יהודה על מלך בבל הוא ואמו ועבדיו ושריו וסריסיו ויקח אתו מלך בבל בשנת שמנה למלכו
13 Yadda Ubangiji ya faɗa, Nebukadnezzar ya kwashe dukan dukiyar haikalin Ubangiji, da ta fadan sarki, ya kuma kwashe dukan kayan zinariyar da Solomon sarkin Isra’ila ya ƙera domin haikalin Ubangiji.
ויוצא משם את כל אוצרות בית יהוה ואוצרות בית המלך ויקצץ את כל כלי הזהב אשר עשה שלמה מלך ישראל בהיכל יהוה כאשר דבר יהוה
14 Ya kwashi dukan mutanen Urushalima zuwa bauta, ya kwashi dukan fadawa, da mayaƙa, da masu sana’a, da maƙera, yawansu ya kai dubu goma. Ba wanda ya ragu, sai matalautan ƙasar.
והגלה את כל ירושלם ואת כל השרים ואת כל גבורי החיל עשרה (עשרת) אלפים גולה וכל החרש והמסגר לא נשאר זולת דלת עם הארץ
15 Nebukadnezzar ya ɗauki Yehohiyacin ya kai bauta a Babilon. Ya kuma kwashe mahaifiyar sarki, da matansa, da fadawansa, da manyan mutanen ƙasar daga Urushalima ya kai Babilon.
ויגל את יהויכין בבלה ואת אם המלך ואת נשי המלך ואת סריסיו ואת אולי (אילי) הארץ הוליך גולה מירושלם בבלה
16 Sarkin Babilon kuma ya kwashe dukan mayaƙa dubu bakwai, ƙarfafu, shiryayyu don yaƙi, da masu sana’a, da maƙera dubu ɗaya, ya kai Babilon.
ואת כל אנשי החיל שבעת אלפים והחרש והמסגר אלף--הכל גבורים עשי מלחמה ויביאם מלך בבל גולה בבלה
17 Sarkin Babilon ya sa Mattaniya, ɗan’uwan mahaifin Yehohiyacin, ya zama sarki a madadinsa, ya canja masa suna zuwa Zedekiya.
וימלך מלך בבל את מתניה דדו תחתיו ויסב את שמו צדקיהו
18 Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal’yar Irmiya; mutuniyar Libna.
בן עשרים ואחת שנה צדקיהו במלכו ואחת עשרה שנה מלך בירושלם ושם אמו חמיטל (חמוטל) בת ירמיהו מלבנה
19 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Yehohiyakim ya yi.
ויעש הרע בעיני יהוה ככל אשר עשה יהויקים
20 Saboda fushin Ubangiji ne dukan waɗannan abubuwa suka faru da Urushalima, da kuma Yahuda, a ƙarshe kuma ya kawar da su daga fuskarsa. To, sai Zedekiya ya yi wa sarkin Babilon tawaye.
כי על אף יהוה היתה בירושלם וביהודה עד השלכו אתם מעל פניו וימרד צדקיהו במלך בבל

< 2 Sarakuna 24 >