< 2 Sarakuna 23 >

1 Sai sarki ya kira dukan dattawan Yahuda da Urushalima.
君王於是派人召集猶大和耶路撒冷所有的長老來到他跟前。
2 Sai ya haura zuwa cikin haikalin Ubangiji tare da mutanen Yahuda, da na Urushalima, da firistoci, da annabawa, dukan mutane, manya da ƙanana. Ya karanta musu duk kalmomin Littafin Alkawari, wanda aka samu a haikalin Ubangiji.
君王同所有的猶大人、耶路撒冷的居民、眾司祭、眾先知、全體人民,不分貴賤大小,上了上主聖殿,將在上主殿內尋獲的約書上的一切話,讀給他們聽。
3 Sarki ya tsaya dab da ginshiƙi ya kuma sabunta alkawarin a gaban Ubangiji, ya ce zai bi Ubangiji, yă kiyaye dokokinsa, da ƙa’idodinsa, da farillansa, da dukan zuciyarsa da dukan ransa, ta haka ya tabbatar da kalmomin alkawarin da yake a rubuce a cikin littafin nan. Sa’an nan dukan mutane ma suka yi alkawari yin haka.
君王站在高台上,在上主面前立約,要全心全意跟隨上主,遵守祂的誡命、典章和法律,履行這卷書上所記載的盟約的話;全體人民也一致接受了這盟約。
4 Sai Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist, tare da firistocin da suke taimakonsa, da masu tsaron ƙofa su kawar da dukan abubuwan da aka yi domin Ba’al, da domin Ashera, da kuma domin dukan rundunar taurari, daga haikalin Ubangiji. Ya ƙone su a bayan Urushalima a filayen Kwarin Kidron, ya kwashe tokan zuwa Betel.
君王於是吩咐大司祭希耳克雅和副大司祭以及守門的,將那些為巴耳,為阿舍辣和為天上萬象所製造的祭器,都從上主殿內搬出,在耶路撒冷外克德龍谷的田野中焚燒了,把灰燼帶到貝特耳去。
5 Ya kawar da firistocin gumakan da sarakunan Yahuda suka naɗa don su ƙona turare a masujadan kan tuddai na garuruwan Yahuda, da kuma waɗanda suke kewaye da Urushalima, masu ƙona turare wa Ba’al, rana da wata, ga rukunin taurari, da kuma ga dukan rundunan taurari.
君王廢除了以前猶大王派定在猶大各城,和耶路撒冷周圍高丘上的焚香的僧侶,以及向巴耳、太陽、月亮和黃道帶,並天上萬象焚香的人;
6 Ya ɗauke ginshiƙin Ashera daga haikalin Ubangiji zuwa Kwarin Kidron can bayan Urushalima, ya ƙone shi a can. Ya niƙa shi sai da ya zama toka, sai ya watsar da ƙurar a filin kabarin talakawa.
又將木偶從上主的殿內搬到耶路撒冷城外克德龍谷,在克德龍谷焚燒了,磨碎成灰,將灰撒在平民的墳墓上;
7 Ya kuma rurrushe mazaunan karuwai mazan haikali waɗanda suke a haikalin Ubangiji, da kuma inda mata suke yi wa Ashera saƙa.
拆毀了上主殿內廟倡的房舍,婦女們為木偶編織衣服的地方。
8 Yosiya ya kawo dukan firistoci daga garuruwan Yahuda, ya kuma lalatar da masujadan kan tuddai daga Geba har zuwa Beyersheba, inda firistoci suke ƙona turare. Ya rurrushe matsafai a ƙofofi shigan gari na mashigi zuwa Ƙofar Yoshuwa, gwamnan birnin, wanda yake a hagu da ƙofar birnin.
又從猶大各城將所有的司祭召來,破壞了司祭們焚香的高丘,從革巴直到貝爾舍巴;拆毀了城門左邊,市長約叔亞門前的羊神祭壇。
9 Ko da yake firistocin masujadan kan tuddai ba su yi hidima a bagaden Ubangiji a Urushalima ba, sun ci burodi marar yisti tare da sauran firistoci.
無論如何,高丘的司祭,不能上耶路撒冷上主的祭壇,只能在自己的兄弟中間分食無酵餅。
10 Ya lalatar da Tofet, wanda yake a Kwarin Ben Hinnom, don kada kowa yă iya yin amfani da wurin don yă miƙa hadayar ɗansa, ko’yarsa a wuta ga Molek.
約史雅又破壞了本希農山谷中的托斐特,免得再有人火祭子女,獻給摩肋客。
11 Ya kawar da dawakan nan da sarakunan Yahuda suka keɓe wa gumakan nan na rana daga mashigin haikalin Ubangiji. Waɗannan dawakan suna kusa da ɗakin Natan Melek, ɗaya daga cikin dattawan sarki. Yosiya ya kuma ƙone kekunan yaƙi a yin sujada ga gumakan nan rana.
又將以前猶大王在上主聖殿門前,靠近太監乃堂默肋客住宅的廊房裏,獻於太陽的駿馬除去;也用火燒掉了奉獻給太陽的車輛。
12 Ya rushe bagadan da sarakunan Yahuda suka kafa a kan ɗakin sama kusa da ɗakin sama na Ahaz, da kuma bagadai biyu da Manasse ya gina a filaye biyu na haikalin Ubangiji. Ya kawar da su daga can, ya farfashe su, ya zubar da tarkacen a Kwarin Kidron.
猶大王在阿哈次的樓房頂上所建築的祭壇,和默納舍在上主聖殿兩庭院內建築的祭壇,君王也都拆掉搗毀,把碎塊倒在克德龍谷裏。
13 Sarkin kuma ya lalatar da masujadan kan tuddan da suke gabas da Urushalima, kudu da Tudun Hallaka, waɗanda Solomon sarkin Isra’ila ya gina don Ashtarot, ƙazantacciyar alliyar Sidoniyawa, da Kemosh ƙazantaccen allah na Mowab, da kuma Molek allahn banƙyama na mutanen Ammon.
從前以色列王撒羅滿在耶路撒冷東,橄欖山南,為漆東人的可惡之物阿市托勒特,為摩阿布的可惡之物革摩士,為阿孟子民的可惡之物米耳公所建立的高丘,君王一概破壞了;
14 Yosiya ya farfashe keɓaɓɓun duwatsu, ya rurrushe ginshiƙan Asheransu, ya baza ƙasusuwan mutane a can.
又打碎了石柱,砍斷了木偶,用人骨填滿了那些地方。
15 Har ma da bagaden Betel, masujadan kan tudun da Yerobowam ɗan Nebat ya yi, wanda ya sa Isra’ila suka yi zunubi. Wannan bagade da masujadan kan tudun ma ya kawar, ya ƙone masujadan kan tudun, ya niƙa su, ya kuma ƙone ginshiƙin Ashera.
此外,那使以色列陷於罪惡的乃巴特的兒子雅洛貝罕,在貝特耳所立的祭壇和高丘,約史雅也將這祭壇拆毀,將丘壇的石塊打碎成灰,燒了木偶。
16 Da Yosiya ya dubi kewaye da shi, ya ga kaburburan da suke can a gefen tudu, sai ya sa aka kwaso ƙasusuwan da suke cikinsu aka ƙone a kan bagade don yă lalatar da shi bisa ga maganar Ubangiji ta bakin mutumin Allah, wanda ya yi annabcin waɗannan abubuwa.
約史雅轉身,看見山上墳墓,就派人掘出墳裏的骨骸,放在祭壇上焚燒,污辱了這祭壇,應驗了天主的人,當雅洛貝罕在慶節日站在這祭壇上時,所說的的話。約史雅再戔身遙望,看見曾預言這些事的天主的人的墳墓,
17 Sarkin ya yi tambaya, ya ce, “Wane kabari ke nan nake gani?” Mutanen birnin suka ce, “Ai, kabarin annabin Allah ne wanda ya fito daga Yahuda, shi ne ya yi annabcin waɗannan abubuwan da ka aikata gāba da bagaden Betel.”
就問說:「看見的是誰的墓碑﹖」城中的人回答說:「是天主的人的墳墓,他從猶大來,預言了你剛才對貝特耳祭壇所行的事」。
18 Sai ya ce, “Ku rabu da shi, kada wani yă dami ƙasusuwansa.” Saboda haka suka bar kasusuwansa, da na annabin da ya fito Samariya.
君王遂說:「讓他安息吧! 誰也不要移動他的骨骸! 」因此人沒有移動他的骨骸,也沒有移動那撒瑪黎雅先知的骨骸。
19 Kamar yadda ya yi a Betel, Yosiya ya kawar da dukan ɗakunan gumaka a kan tuddan da sarakunan Isra’ila suka gina a garuruwan Samariya, waɗanda suka tozarta Ubangiji.
從前以色列王在e口城內所建築,而激怒上主的高丘廟宇,約史雅也一律除去,對這些廟宇所行的,完全像在貝特耳所行一樣。
20 Yosiya ya yayyanka dukan firistoci na waɗannan masujadan kan tuddai, ya kuma ƙone ƙasusuwan mutane a kansu. Sa’an nan ya koma Urushalima.
凡在那裏所有的高丘司祭,他都在祭壇上殺了,並且在祭壇焚燒了人骨,然後回了耶路撒冷。
21 Sarkin ya ba da umarnin nan ga dukan mutane, cewa, “Ku yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, yadda aka rubuta a Littafin Alkawari.”
君王吩咐全體人民說:「你們要按照這約書所記載的,向上主你們的天主舉行逾越節」。
22 Ba a taɓa yin irin Bikin Ƙetarewa haka ba, tun zamanin da masu shari’a suke aiki a matsayin sarakuna, ko a kwanakin sarakunan Isra’ila, ko na Yahuda.
實在,自從民長統治以色列時日以來,和在以色列各君王及猶大王當政期間,從來沒有舉行過像這樣的一個逾越節,
23 Amma a shekara ta goma sha takwas ta mulkin sarki Yosiya, aka yi Bikin Ƙetarewan nan ga Ubangiji a Urushalima.
只有在約史雅王十八年,在耶路撒冷向上主舉行了這樣的逾越節。
24 Ban da haka, Yosiya ya kawar da masu duba, da masu maita, da allolin gidaje, da gumaka, da duk wani abin banƙyaman da ya gani a Yahuda da Urushalima. Ya yi wannan domin yă cika wa’adodin shari’a yadda suke a littafin da Hilkiya firist ya samu a haikalin Ubangiji.
此外,凡在猶大地和耶路撒冷所見到的那些招魂的,行邪術的,忒辣芬和偶像,以及可憎之物,約史雅一概掃除,履行了司祭希耳克雅在上主殿內,所發見的書上所記載的法律。
25 Babu wani sarki kafin Yosiya, ko kuma a bayansa, wanda ya juya ga Ubangiji da dukan zuciyarsa, da dukan ransa, da dukan ƙarfinsa bisa ga shari’ar Musa, kamar yadda ya yi.
在他以前沒有人一個君王像他這樣按照梅瑟的法律,全心全意全力歸向上主;在他以後也沒有一個像他一樣的。
26 Duk da haka, Ubangiji bai huce daga zafin fushinsa wanda ya ƙuna game da Yahuda saboda abin da Manasse ya aikata don yă tozarta shi ba.
雖然如此,上主仍未息向猶大所發的盛怒烈火,因為默納舍種種行事,太激怒了上主,
27 Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan shafe Yahuda ma kamar yadda na shafe Isra’ila, daga gabana, zan ƙi Urushalima birnin da na zaɓa, da wannan haikali wanda na ce, ‘A can Sunana zai kasance.’”
因此上主說:「我仍要由我面前除去猶大,如同我除去了以色列一樣;我要拋棄我所選擇的這座耶路撒冷城,和我所說我名必留其間的殿」。
28 Game da sauran ayyukan mulkin Yosiya, da duk abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.
約史雅其餘的事蹟,他的一切作為,都記載在猶大王實錄上。
29 Yayinda Yosiya yake sarki, Fir’auna Neko, sarkin Masar ya haura zuwa Kogin Yuferites don yă taimaki sarkin Assuriya da yaƙi. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa’ad da Fir’auna Neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Megiddo.
約史雅年間,埃及王法郎乃苛上到幼發拉的河,亞述王那裏,約史雅出兵與他對抗,初次會戰,就在默基多陣亡。
30 Bayin Yosiya suka ɗauko gawarsa daga Megiddo suka kai Urushalima, suka binne shi a kabarinsa. Sai mutanen ƙasar suka ɗauki Yehoyahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki a madadin mahaifinsa.
他的臣僕將他的屍體,用車從默基多運到耶路撒冷,葬在他自己的墳墓裏;當地的人民推舉約史雅的兒子約哈次,給他傅油,繼承父位為王。
31 Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki. Ya yi mulki na wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal’yar Irmiya; mutuniyar Libna.
約哈次登極時年二十三歲,在耶路撒冷為王三個月,他的母親名叫哈慕塔耳,是里貝納人耶勒米雅的女兒。
32 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda kakanninsa suka yi.
他行上主視為惡的事,完全像他祖先所行的一樣。
33 Fir’auna Neko ya sa shi a sarƙa a Ribla a ƙasar Hamat don kada yă yi mulki a Urushalima, sa’an nan ya sa wa Yahuda harajin talenti ɗari na azurfa, da talenti ɗaya na zinariya.
法郎乃苛將他幽禁在哈瑪特的黎貝拉,不要他在耶路撒冷作王,並要那地方繳約一百「塔冷通」銀子和十「塔冷通」金子作賠款。
34 Fir’auna Neko ya naɗa Eliyakim ɗan Yosiya sarki a maimakon mahaifinsa, ya kuma canja masa suna zuwa Yehohiyakim. Ya ɗauki Yehoyahaz ya kai Masar, a can ya mutu.
以後,法郎乃苛立了約史雅的兒子厄里雅金繼他父親約史雅為王,給他改名叫約雅金;後將約哈次帶到埃及去了,約哈次就死在那裏。
35 Yehohiyakim ya riƙa biyan Fir’auna Neko azurfa da zinariyar da ya umarta. Don yă yi haka sai ya riƙa karɓar azurfa da zinariya daga mutanen ƙasar, kowa bisa ga ƙarfinsa.
約雅金將金銀付給法郎,但為交付的求要賠款,只得國家徵稅,要本國人民每人依照自己的家業,繳納金銀,送給法欴乃苛。
36 Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Zebuda’yar Fedahiya, mutuniyar Ruma.
約雅金登極時年二十五歲,在耶路撒冷為王十一年;他的母親名叫則步達,是魯瑪人培達雅的女兒。
37 Ya kuma aika mugunta a gaban Ubangiji yadda kakanninsa suka yi.
他行了上主視為惡的事,全像他祖先所行的一樣。

< 2 Sarakuna 23 >