< 2 Sarakuna 20 >
1 A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da rashin lafiya har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya ɗan Amoz ya zo wurinsa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka domin za ka mutu, ba za ka warke ba.”
那时,希西家病得要死。亚摩斯的儿子先知以赛亚去见他,对他说:“耶和华如此说:‘你当留遗命与你的家,因为你必死,不能活了。’”
2 Hezekiya ya juya fuskarsa wajen bango ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce,
希西家就转脸朝墙,祷告耶和华说:
3 “Ya Ubangiji, ka tuna yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da zuciya ɗaya, na kuma aikata abin da yake daidai a gabanka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi.
“耶和华啊,求你记念我在你面前怎样存完全的心,按诚实行事,又做你眼中所看为善的。”希西家就痛哭了。
4 Kafin Ishaya yă bar tsakiyar filin gida, sai maganar Ubangiji ta zo masa cewa,
以赛亚出来,还没有到中院,耶和华的话就临到他,说:
5 “Ka koma ka ce wa Hezekiya, shugaban mutanena, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na mahaifinka Dawuda ya ce, na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan warkar da kai. A rana ta uku daga yau za ka haura zuwa haikalin Ubangiji.
“你回去告诉我民的君希西家说:耶和华—你祖大卫的 神如此说:‘我听见了你的祷告,看见了你的眼泪,我必医治你;到第三日,你必上到耶和华的殿。
6 Zan ƙara maka shekara goma sha biyar. Zan kuma cece ka daga hannun sarkin Assuriya. Zan kāre birnin nan saboda kaina da kuma bawana Dawuda.’”
我必加增你十五年的寿数,并且我要救你和这城脱离亚述王的手。我为自己和我仆人大卫的缘故,必保护这城。’”
7 Sai Ishaya ya ce, “A kwaɓa ɓaure.” Sai aka yi haka, aka shafa wa marurun, ya kuma warke.
以赛亚说:“当取一块无花果饼来。”人就取了来,贴在疮上,王便痊愈了。
8 Hezekiya ya tambayi Ishaya, “Wace alama ce za tă nuna cewa Ubangiji zai warkar da ni, kuma cewa in tafi haikalin Ubangiji kwana uku daga yanzu?”
希西家问以赛亚说:“耶和华必医治我,到第三日,我能上耶和华的殿,有什么兆头呢?”
9 Sai Ishaya ya ce, “Ga alamar Ubangiji zuwa gare ka da za tă nuna cewa Ubangiji zai cika alkawarinsa. Kana so inuwa tă yi gaba da taki goma, ko tă koma baya da taki goma?”
以赛亚说:“耶和华必成就他所说的。这是他给你的兆头:你要日影向前进十度呢?是要往后退十度呢?”
10 “Ai, abu mai sauƙi ne inuwa tă yi gaba da taki goma.” In ji Hezekiya, “Gwamma dai tă koma baya da taki goma.”
希西家回答说:“日影向前进十度容易,我要日影往后退十度。”
11 Sai annabi Ishaya ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa inuwa ta koma baya da taki goma bisa ga magwajin rana wanda Sarki Ahaz ya gina.
先知以赛亚求告耶和华,耶和华就使亚哈斯的日晷向前进的日影,往后退了十度。
12 A wannan lokaci, Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu tare da kyauta, domin ya sami labarin rashin lafiyar Hezekiya.
那时,巴比伦王巴拉但的儿子米罗达·巴拉但听见希西家病而痊愈,就送书信和礼物给他。
13 Hezekiya ya karɓi jakadun, ya nuna musu dukan abin da yake a ɗakunan ajiyarsa, azurfa, zinariya, kayan ƙanshi da mai, wurin ajiye makamansa da kuma dukan abin da aka samu a ɗakin ajiyarsa. Babu wani abu a fadansa ko a dukan mulkinsa da Hezekiya bai nuna musu ba.
希西家听从使者的话,就把他宝库的金子、银子、香料、贵重的膏油,和他武库的一切军器,并他所有的财宝,都给他们看。他家中和他全国之内,希西家没有一样不给他们看的。
14 Sai annabi Ishaya ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya tambaye shi ya ce, “Me mutanen nan suka ce, kuma daga ina suka fito?” Sai Hezekiya ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Daga Babilon.”
于是先知以赛亚来见希西家王,问他说:“这些人说什么?他们从哪里来见你?”希西家说:“他们从远方的巴比伦来。”
15 Annabin ya yi tambaya, “Me suka gani a fadanka?” Hezekiya ya ce, “Ba abin da yake a ma’ajina da ban nuna musu ba.”
以赛亚说:“他们在你家里看见了什么?”希西家说:“凡我家中所有的,他们都看见了;我财宝中没有一样不给他们看的。”
16 Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji kalmar Ubangiji.
以赛亚对希西家说:“你要听耶和华的话,
17 Lokaci yana zuwa da za a kwashe kome a fadanka da kuma dukan abubuwan da kakanninka suka tara har yă zuwa yau, a kai su Babilon. Ba abin da za a rage, in ji Ubangiji.
日子必到,凡你家里所有的,并你列祖积蓄到如今的,都要被掳到巴比伦去,不留下一样。这是耶和华说的。
18 Za a kuma kwashe waɗansu daga cikin zuriyarka, na jiki da jininka waɗanda za a haifa maka, su zama bābānni a fadan sarkin Babilon.”
并且从你本身所生的众子,其中必有被掳去在巴比伦王宫里当太监的。”
19 Hezekiya ya ce, “Maganar Ubangiji da ka faɗa ta yi kyau.” Gama ya yi tunani cewa, “Ai, ba ni da damuwa, tun da yake za a yi zaman lafiya da salama a kwanakina.”
希西家对以赛亚说:“你所说耶和华的话甚好!若在我的年日中有太平和稳固的景况,岂不是好吗?”
20 Game da sauran ayyukan mulkin Hezekiya, dukan nasarorinsa da yadda ya yi tafki da kuma bututun ruwa inda ya kawo ruwa cikin birni, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.
希西家其余的事和他的勇力,他怎样挖池、挖沟、引水入城,都写在犹大列王记上。
21 Hezekiya ya huta tare da kakanninsa. Manasse ɗansa kuma ya gāje shi.
希西家与他列祖同睡。他儿子玛拿西接续他作王。