< 2 Sarakuna 2 >
1 Da lokaci ya yi da Ubangiji zai ɗauki Iliya zuwa sama cikin guguwa, Iliya da Elisha kuwa suna kan hanyarsu daga Gilgal.
2 Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ka dakata a nan; Ubangiji ya aike ni Betel.” Amma Elisha ya amsa ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai kuma kana a raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka gangara zuwa Betel.
3 Sai ƙungiyar annabawa a Betel suka fito zuwa wajen Elisha suka ce masa, “Ka san cewa Ubangiji zai ɗauki maigidanka daga wurinka yau?” Sai ya ce, “I, na sani, amma kada ku yi magana game da wannan.”
4 Sai Iliya ya ce masa, “Ka dakata a nan Elisha; Ubangiji ya aike ni Yeriko.” Sai ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai ma kana a raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka sai suka tafi Yeriko.
5 Ƙungiyar annabawa a Yeriko suka haura zuwa wajen Elisha suka ce, “Ko ka san Ubangiji zai ɗauki maigidanka daga gare ka yau?” Sai ya ce, “I, na sani, amma ku bar zancen nan tukuna.”
6 Sai Iliya ya ce masa, “Ka dakata a nan, Ubangiji ya aike ni Urdun.” Sai Elisha ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai kuma kana raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka ci gaba da tafiya tare.
7 Mutum hamsin na ƙungiyar annabawa suka je suka tsaya da nisa, suna fuskantar inda Iliya da Elisha suka tsaya a Urdun.
8 Sai Iliya ya tuɓe rigarsa, ya nannaɗe ya bugi ruwan Urdun da shi. Sai ruwan ya dāre gida biyu, suka haye a busasshiyar ƙasa.
9 Da suka haye, sai Iliya ya ce wa Elisha, “Faɗi mini, abin da kake so in yi maka kafin a ɗauke ni daga gare ka!” Elisha ya amsa ya ce, “Bari in gāji ninki biyu na ruhunka.”
10 Iliya ya ce, “Ka nemi abu mai wuya, amma in ka ga lokacin da aka ɗauke ni daga gare ka, zai zama naka, in ba haka ba, ba za ka samu ba ke nan.”
11 Yayinda suke tafiya suna magana, sai kwatsam, keken yaƙin wuta da dawakan wuta suka ratse tsakaninsu, sai Iliya ya tafi sama a cikin guguwa.
12 Da Elisha ya ga haka sai ya yi ihu yana cewa, “Babana! Babana! Kekunan yaƙin da mahayan dawakan Isra’ila!” Elisha kuwa bai sāke ganinsa ba. Sai ya kama tufafinsa ya yayyage.
13 Sai ya ɗauki rigar da ta fāɗo daga Iliya ya koma ya tsaya a gaɓar Kogin Urdun.
14 Sa’an nan Elisha ya ɗauki rigar da ta fāɗo daga Iliya ya bugi ruwan da shi. Ya ce, “Yanzu ina Ubangiji Allah na Iliya?” Da ya bugi ruwan sai ruwan ya dāre gida biyu, sai ya haye.
15 Ƙungiyar annabawa daga Yeriko, waɗanda suke kallo, suka ce, “Ruhun Iliya yana a kan Elisha.” Sai suka je su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa.
16 Suka ce, “Duba, mu bayinka muna da masu ji da ƙarfi hamsin. Bari su je su nemi maigidanka. Wataƙila, Ruhun Ubangiji ya ɗauke shi ya ajiye bisa wani dutse, ko wani kwari.” Elisha ya ce, “A’a, kada ku aike su.”
17 Amma suka matsa masa har ya ji ba ya iya hana su. Saboda haka ya ce, “Ku aike su.” Sai suka aiki mutane hamsin, suka yi ta nema har kwana uku amma ba su same Iliya ba.
18 Da suka dawo wurin Elisha, wanda yake a Yeriko, sai ya ce musu, “Ban ce muku kada ku tafi ba?”
19 Mutane garin suka ce wa Elisha, “Ranka yă daɗe, duba, garin yana da kyan gani, amma ruwan ba shi da kyau, ƙasar kuma ba ta ba da amfani.”
20 Sai ya ce, “Ku kawo mini sabuwar ƙwarya, ku kuma sa gishiri a ciki.” Sai suka kawo masa.
21 Sai ya tafi maɓulɓular ruwan yana watsa gishirin a ciki, yana cewa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Na warkar da ruwan nan. Ba zai ƙara jawo mutuwa, ko yă hana ƙasar ba da amfani ba.’”
22 Ruwan ya tsabtacce har yă zuwa yau, bisa ga faɗin Elisha.
23 Daga nan sai Elisha ya tafi Betel. Yayinda yake tafiya a hanya, sai waɗansu matasa suka fito daga cikin gari, suka yi masa dariya suna cewa, “Ka haura, ya kai mai kai marar gashi! Ka haura, kai mai kai marar gashi!”
24 Sai ya juya ya dube su, ya la’anta su da sunan Ubangiji. Sai beyar guda biyu suka fito daga jeji suka hallaka matasa arba’in da biyu daga cikinsu.
25 Sai ya ci gaba zuwa Dutsen Karmel, daga can kuma ya koma Samariya.