< 2 Sarakuna 15 >

1 A shekara ta ashirin da bakwai ta mulkin Yerobowam sarkin Isra’ila, Azariya ɗan Amaziya, sarkin Yahuda ya fara mulki.
בשנת עשרים ושבע שנה לירבעם מלך ישראל מלך עזריה בן אמציה מלך יהודה
2 Yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya daga Urushalima.
בן שש עשרה שנה היה במלכו וחמשים ושתים שנה מלך בירושלם ושם אמו יכליהו מירושלם
3 Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, yadda mahaifinsa Amaziya ya yi.
ויעש הישר בעיני יהוה ככל אשר עשה אמציהו אביו
4 Amma bai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane kuwa suka yi ta yin hadaya da ƙona turare a can.
רק הבמות לא סרו עוד העם מזבחים ומקטרים בבמות
5 Ubangiji ya sa wa sarki ciwon kuturta har mutuwarsa, ya kuma zauna a keɓe. Yotam ɗan sarki, shi ne ya gudanar da sha’anin fada, ya kuma shugabanci mutanen ƙasar.
וינגע יהוה את המלך ויהי מצרע עד יום מתו וישב בבית החפשית ויותם בן המלך על הבית שפט את עם הארץ
6 Game da sauran ayyukan mulkin Azariya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.
ויתר דברי עזריהו וכל אשר עשה הלא הם כתובים על ספר דברי הימים--למלכי יהודה
7 Azariya ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi kusa da su a Birnin Dawuda. Yotam ɗansa, kuma ya gāje shi.
וישכב עזריה עם אבתיו ויקברו אתו עם אבתיו בעיר דוד וימלך יותם בנו תחתיו
8 A shekara ta talatin da takwas ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Zakariya ɗan Yerobowam ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki wata shida.
בשנת שלשים ושמנה שנה לעזריהו מלך יהודה מלך זכריהו בן ירבעם על ישראל בשמרון--ששה חדשים
9 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi. Bai bar aikata zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila suka yi ba.
ויעש הרע בעיני יהוה כאשר עשו אבתיו לא סר מחטאות ירבעם בן נבט אשר החטיא את ישראל
10 Sai Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla wa Zakariya maƙarƙashiya. Ya tasam masa a gaban jama’a, ya kashe shi, ya kuma gāje shi.
ויקשר עליו שלם בן יבש ויכהו קבל עם וימיתהו וימלך תחתיו
11 Game da sauran ayyukan mulkin Zakariya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
ויתר דברי זכריה הנם כתובים על ספר דברי הימים--למלכי ישראל
12 Ta haka maganar Ubangiji da ya yi wa Yehu ta cika, wadda ya ce, “Zuriyarka za tă zauna a kursiyin Isra’ila har tsara ta huɗu.”
הוא דבר יהוה אשר דבר אל יהוא לאמר בני רביעים ישבו לך על כסא ישראל ויהי כן
13 Shallum ɗan Yabesh ya zama sarki a shekara ta talatin da tara ta mulkin Uzziya sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki na wata ɗaya a Samariya.
שלום בן יביש מלך בשנת שלשים ותשע שנה לעזיה מלך יהודה וימלך ירח ימים בשמרון
14 Sa’an nan Menahem ɗan Gadi ya gangara daga Tirza ya haura zuwa Samariya. Ya tasam wa Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya kuma gāje shi.
ויעל מנחם בן גדי מתרצה ויבא שמרון ויך את שלום בן יביש בשמרון וימיתהו וימלך תחתיו
15 Game da sauran ayyukan mulkin Shallum, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
ויתר דברי שלום וקשרו אשר קשר הנם כתובים על ספר דברי הימים--למלכי ישראל
16 A lokacin nan sai Menahem ya taso daga Tirza, ya kai wa Tifsa hari da kowa wanda yake a birnin da kewayenta, don sun ƙi su buɗe ƙofofinsu. Ya kori Tifsa daga aiki, ya kuma tsattsaga cikin dukan mata masu juna biyu.
אז יכה מנחם את תפסח ואת כל אשר בה ואת גבוליה מתרצה--כי לא פתח ויך את כל ההרותיה בקע
17 A shekara ta talatin da takwas ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Menahem ɗan Gadi ya zama sarkin Isra’ila, ya yi mulki a Samariya shekara goma.
בשנת שלשים ותשע שנה לעזריה מלך יהודה מלך מנחם בן גדי על ישראל עשר שנים--בשמרון
18 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. A duk tsawon mulkinsa, bai rabu da zunuban da Yerobowam ɗan Nebat ya sa Isra’ila suka aikata ba.
ויעש הרע בעיני יהוה לא סר מעל חטאות ירבעם בן נבט אשר החטיא את ישראל--כל ימיו
19 Sai Ful sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar hari, Menahem kuwa ya ba shi talenti dubu na azurfa don yă sami goyon bayansa, yă kuma ƙarfafa kahuwa mulkin.
בא פול מלך אשור על הארץ ויתן מנחם לפול אלף ככר כסף--להיות ידיו אתו להחזיק הממלכה בידו
20 Menahem ya tara kuɗin ne ta hanyar haraji a Isra’ila inda ya sa kowane attajiri ya ba da shekel hamsin don a ba sarkin Assuriya. Sa’an nan sarkin Assuriya ya janye, bai ƙara kasance a ƙasar ba.
ויצא מנחם את הכסף על ישראל על כל גבורי החיל לתת למלך אשור חמשים שקלים כסף לאיש אחד וישב מלך אשור ולא עמד שם בארץ
21 Game da sauran ayyukan mulkin Menahem, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
ויתר דברי מנחם וכל אשר עשה הלוא הם כתובים על ספר דברי הימים--למלכי ישראל
22 Menahem ya huta tare da kakanninsa. Fekahiya ɗansa kuma ya gāje shi.
וישכב מנחם עם אבתיו וימלך פקחיה בנו תחתיו
23 A shekara ta hamsin ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Fekahiya ɗan Menahem ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki shekara biyu.
בשנת חמשים שנה לעזריה מלך יהודה מלך פקחיה בן מנחם על ישראל בשמרון--שנתים
24 Fekahiya ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat wanda ya sa Isra’ila ya aikata ba.
ויעש הרע בעיני יהוה לא סר מחטאות ירבעם בן נבט אשר החטיא את ישראל
25 Ɗaya daga cikin manyan fadawansa, Feka ɗan Remaliya, ya ƙulla masa maƙarƙashiya. Ɗauke da mutanen Gileyad hamsin, ya kashe Fekahiya tare da Argob da kuma Ariye a fadan sarki a Samariya. Ta haka Feka ya kashe Fekahiya ya kuma gāje shi.
ויקשר עליו פקח בן רמליהו שלישו ויכהו בשמרון בארמון בית מלך (המלך) את ארגב ואת האריה ועמו חמשים איש מבני גלעדים וימתהו וימלך תחתיו
26 Game da sauran ayyukan mulkin Fekahiya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
ויתר דברי פקחיה וכל אשר עשה הנם כתובים על ספר דברי הימים--למלכי ישראל
27 A shekara ta hamsin da biyu ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Feka ɗan Remaliya ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya yi mulki shekara ashirin.
בשנת חמשים ושתים שנה לעזריה מלך יהודה מלך פקח בן רמליהו על ישראל בשמרון--עשרים שנה
28 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai kauce wa zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta yi ba.
ויעש הרע בעיני יהוה לא סר מן חטאות ירבעם בן נבט אשר החטיא את ישראל
29 A zamanin Feka sarkin Isra’ila, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya zo ya kama Iyon, Abel-Bet-Ma’aka, Yanowa da Kedesh da kuma Hazor. Ya kame Gileyad da Galili, haɗe da dukan ƙasar Naftali, ya kuma kwashi mutanen zuwa Assuriya.
בימי פקח מלך ישראל בא תגלת פלאסר מלך אשור ויקח את עיון ואת אבל בית מעכה ואת ינוח ואת קדש ואת חצור ואת הגלעד ואת הגלילה כל ארץ נפתלי ויגלם אשורה
30 Sa’an nan Hosheya ɗan Ela ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya. Ya fāɗa masa ya kuma kashe shi, sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki a shekara ta shirin ta mulkin Yotam ɗan Uzziya.
ויקשר קשר הושע בן אלה על פקח בן רמליהו ויכהו וימיתהו וימלך תחתיו--בשנת עשרים ליותם בן עזיה
31 Game da sauran ayyukan mulkin Feka da duk abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
ויתר דברי פקח וכל אשר עשה הנם כתובים על ספר דברי הימים--למלכי ישראל
32 A shekara ta biyu ta mulkin Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila, Yotam ɗan Uzziya sarkin Yahuda ya fara mulki.
בשנת שתים לפקח בן רמליהו מלך ישראל מלך יותם בן עזיהו מלך יהודה
33 Ya zama sarki yana da shekara ashirin da biyar, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha,’yar Zadok.
בן עשרים וחמש שנה היה במלכו ושש עשרה שנה מלך בירושלם ושם אמו ירושא בת צדוק
34 Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa Uzziya ya yi.
ויעש הישר בעיני יהוה ככל אשר עשה עזיהו אביו עשה
35 Duk da haka, bai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane suka ci gaba da yin hadaya da ƙona turare a can. Yotam ya sāke gina Ƙofar Bisa ta haikalin Ubangiji.
רק הבמות לא סרו--עוד העם מזבחים ומקטרים בבמות הוא בנה את שער בית יהוה--העליון
36 Game da sauran ayyukan mulkin Yotam da aikin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.
ויתר דברי יותם אשר עשה הלא הם כתובים על ספר דברי הימים--למלכי יהודה
37 (A kwanakin nan Ubangiji ya fara aikan Rezin sarkin Aram da Feka ɗan Remaliya, su yi gāba da Yahuda.)
בימים ההם--החל יהוה להשליח ביהודה רצין מלך ארם ואת פקח בן רמליהו
38 Yotam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda, birnin mahaifinsa. Ahaz ɗansa kuma ya gāje shi.
וישכב יותם עם אבתיו ויקבר עם אבתיו בעיר דוד אביו וימלך אחז בנו תחתיו

< 2 Sarakuna 15 >